💖AKWAI WANI ABU..💖
By Sawwama A.
Page 5.
Zaman gidan is so boring to him Allah Allah yake ya fara aiki.
Gidan is too dull is not more the happy home he knew, yanzu hajiya barely have time na gidan ma'aikatan gidan yanzu su kansi isu isu babu wannan barkwancin kannenshi ma bai samun sa su a ido.
3 quarter yake sanye dashi tare da karamin riga Phones dinshi ya kwashe ya sa a aljuhu tunani yake bari ya lek'a garden d'in hajiya ya san yanzu its blooming coz it gives her happiness kula da wajen.
Tana bala'in son flowers ta tab'a bashi labari fitanta waje na farko da alhaji taga gardens a gidajen turawa ya bata sha'awa shine taci alwashin she will make one in her home.
Duk yawan ma'aikatan gidan ita ke kula da kayanta ita take watering ta cutting grass ta share wajen working in that garden gives her joy ko da ya dawo gidan sai ya zamana shi yake taimaka mata tare dashi ake gyaran garden din.
"Innalillahi!" Abinda ya furta kenan ba tare da ya san lokacin da ya furta hakan ba ganin once a colourful garden da ya sani ya koma kaman kufai gaba daya flowers din a death babu abinda ke da rai a wajen sai bishiyoyin wajen bayan haka babu ko flower daya a wajen hasalima in ba wanda ya san an tab'a shuka flowers a wajen ba,ba zaka ce wajen was once a garden gaba daya death grasses ne a wajen.
Motsi yaji ta cikin bishiyoyin,bishiyoyin da he planted them with his own hand shi da hajiya are now all grown up.
D'an zagayawa yayi Ruqayya ya hango tana kokarin tsalla ta ciro mangoro gefenta karamin bokiti ne da ta zuba mangoes din a ciki sai tsalle take bata san da mutum a bayanta ba in tayi tsalle gaba daya sai jikinta ya girgiza.
Sanye take da rigar atampa dinkin A shape hakan ya fitar da kyaun suffarta.
Girgiza kanshi yayi not wanting to think too much.
A hankali ya taka zuwa bayanta,hannu ya sa ba tare da wani wahala ba ya tsinko mangoron da take ta hakilon cirowa.D'an ihu ta sa tare da matsawa hannunta dafe da k'irji tace "yah shar u scared me to death" gira d'aya ya d'aga jin sunan da ta kirashi dashi wai shar sunan da take tsokananahi da shi tana yarinya.
Basarwa yayi ya zira hannunshi a aljuhu yace "me zakiyi da wannan uban mangoron haka? Ba dai sha zaki yi ba ki sa mu ziryan hospital."
Sunkuyar da kai tayi tana wasa da hannunta ya lura da ta girma ta dawo me kunya sosai.
"Ba sha zanyi ba mango juice zan yiwa daddy" ta katse mishi tunani ta hanyar bashi amsa.
"Wow k'anwar tawa fa ba laifi na lura yanzu baki da aikin yi sai fruits juice wa ya koya miki ne?"
Murmushi tayi tace "youtube nan nake koyan komi,nace mommy ta sani a catering school taki i love kitchen it gives me joy in ga ina sarrafa abubuwa but taki." Ta karasa maganan cikin sanyin murya.
Cike da tausayawa yace "me yasa i thought hajiya zata fi kowa farin ciki in kina son girki dan hakan na nufin kin gaje ta." Ya tambayeta dan ya lura ita da hajiya akwai matsala a tarayyarsu.
D'an gyara zaman hulan kanta tayi kaman tana kokonton abinda zata fada "well mommy is not the same mommy that u know,wallahi mommy ta canza gaba d'aya ni ina tunanin akwai wani abu da ya taba kanta time din da muka yi accident din nan."
Zaro ido yayi yace "ko? Amma me yasa kika ce haka wani abu na faruwane ko tana yin wasu abubuwan marasa hankali ne." Ya tambayeta dan dama shi kanshi abubuwa da yawa suna daure mishi kai.
Girgiza kai tayi cikin kasa kasa da murya tace "ko d'aya but she is totally a changed person,ta daina sona kaman da komi nayi zata hantareni haka masu aiki ma da farko bata yi a gaban daddy sai in ta manta ko me yasa oho,ta zo ta daina shi ga kitchen bata girki kullum sai dai ta ci gayu ta sa gold tana ta sa daddy na siya mata tun yana siya da murna yanzu tana son adom jewelries yanzu shima abin ya ishe shi wallahi yanzu between mommy and daddy ba wannan love and affection din in gaya maka yanzu daddy ma gani yake kaman tana zama dashi dan kudinshi ne
"Subhanallahi me yasa zai yi wannan tunanin?" Dan tab'e baki tayi had'e da daga kafada tace "wallahi yah ko da take uwata i sometime feel that way too."
Kallonta yayi da mamaki yace "kai ruky? Me yasa zaki ce haka?"
"Mmm yaya kenan ba dai yanzu baka fi sati da dawowa ba zaka gani zaka ce na gaya maka in less than 2 weeks zaka ji tace zata yi tafiya. Mommy bata wata bata fita a Nigeria ba is either tana dubai ko india ko paris she does'nt shop a Nigeria kuma kullum she is in need of new things ko da yaushe zaka ji tana so a canza abu a palor ko dining,mommy doesnt participate a abubuwan cikin gida ko gyaran dakin daddy bata yi look at this garden is not more a garden wallahi i am fed up i want my old mommy back,bani samun kulawar uwa a matsayina na mace,ta hana min kawa ta hana zuwa makaranta i got addmission twice sai tace makarantan bai yi mata i have no suitor ballw in yi aure in bar dungeon din nan ni da gidan ubana but i cant find peace in it."
Kuka ta fashe dashi tare da sa dukka hannayenta biyu ta rufe fuskanta finally yau ta sauke abinda take ji a ranta she have no one to talk to rayuwarta bak'ik'irin ne mutane daga nesa na envying dinta not knowing the kind hell she is going through.
Hannu yasa ya rungumota jikinshi yana lallashinta zuciyarshi fal tausayinta.
Kanta yake shafawa zuwa bayanta yana rocking dinta a hankali tare da gaya mata kalaman kwantar da hankali.
Sai da tayi kuka me isanta ta raba jikinta da nashi tana goge hawayen fuskanta.
Hanky ya ciro a aljuhunsa ya mika mata sai da ta gama goge idonta ta mika mishi
Dan leka fuskanta yayi yace "you're ok?" Ta gyad'a mishi kai cikin sanyin murya tace "yah thank you for talking to me sosai na ke buqatan hakan i have been carrying this loads in my chest for quite a long time."
Girgiza kai yayi yace "karki damu anytime u feel like talking to someone i am here,i am a good listener."
Kai kawai ta gyad'a mishi daga haka ta dauki roban mangoes dinta ta kama hanyan cikin gidan ajiyan zuciya ya sauke yana mamakin abubuwan sa suka faru ko suke kan faruwa a cikim gidar hajiyarsa da he is so proud of has change she is not the loving mother he knew.
Tafiya suke cikin sabon motan mommynta suna dawowa daga clinic fushi take da momyn saboda taki biyawa ta siya mata ice cream wai dan saboda ana sanyi.
Lokaci lokaci mommyn ke juyowa ta lallashe ta mommy ta juyo tare da sa hannunta daya tana shafa kanta tare da bata hakuri promising her zata bata youghort in sun isa gida ita ta fara hango kuran ruwan da bata san daga inda ya fito ba kafin ta ankarar da mommy,itama mommyn ta gani duk yanda tayi kokarin taka burki motan taki tsayawa sai ma lulawa dasu da ta fara yi.
Ruqayya bata kara sanin me ya faru ba sai dan qani lokaci da ta bude ido da kyar take kallon fuskar mommyn dake yi mata murmushi ta gefen idonta tana iya hango mutum a kwance a gefe daga haka bata kara sanun kanta ba.
A firgice ta farka jikinta duk gumi sai nishi take kaman wacce tayi tsere wannan shine karo na uku da tayi irin wannan mafarkin sak......
*domin samun cigaban wannan littafin a tuntubeni ta wannan layin 09032871327*
Sawwama Qawwama😘