Akwai wani abu page 4.

593 25 1
                                    

💖AKWAI WANI ABU💖






By Sawwama A.




Page 4.





Farin ciki a wajen mata da mijin nan ba a cewa komi sosai hajiya farida tayi mamakin yanda d'an yaron nan ya gano tana da ciki ita bata sani ba.
Taci alwashin da ta sami lafiya zata je wajen da ta ga yaron ta bincike shi there is something special about the boy.

Laulayi me zafi hajiya farida ke yi hakan ya sa bata samu daman zuwa duba yaron ba har sai da cikinta ya kai wata hud'u sannan ta samu kanta a wannan lokacin ne ta fitini alhaji abdullahi suka je inda suka fara ganinshi.

Sun kai minti talatin bata ga billawanshi ba sai almajirai masu sayar da abubuwa har su cire tsammani da ganinshi sai suka hangoshi sanye da kayan makaranta kanshi d'auke da roban ruwan sayarwa bakin nan duk a bushe da ka ganshi ka ga yunwa da gajiya a tattare dashi.

Sam bai lura dasu ba harkan gabanshi kawai yake. Hawaye ne ya cika idanun hajiya farida na tausayinshi,su ko iyayen yaron nan wasu irin iyaye ne ace yaro karami kaman wannan is exposed to neman kudi saboda rashin sauke hakkin da ke kansu.

Alhaji ta nunawa yaron tace "ka ganshi can,ka kirawo mana shi ni kam ina tausayinshi kuma ina da burin taimaka mishi."

Gyad'a kai alhaji yayi cike da gamsuwa kafin ya bude murfin motan ya fita can inda yake tsugune yaje yace ya dauko roban ruwan shi ya zo bakin mota za a siya.

Jiki na rawa ya dau roban ya nufi bakin motan yana isa ya ga hajiya farida bai mantata ba fuskarsa cike da farin ciki yace "lah hajiyar nan ce da ta siya min takalmi." Murmushi tayi kwalla na zubo mata.

Kallonta yayi yace kullum in nayi sallah sai na rokan miki Allah ya sa baby a cikin ai yanzu kinga akwai ko?" Gyada kai tayi kuka na kokarin cin karfinta.

Tunawa yayi bai gaisheta ba da sauri ya dan rusuna yace "ina wuni?" Cikin danne kukanta tace "lafiya lau,yaya ma sunanka?"

"Dan baiwa!" Ya bata amsa a tak'aice dariya tayi tace "ai dan baiwa ba suna bane ya sunanka na gaskiya?" Watsa hannu yayi yace "ban sani ba amma ni ina ji kaman deenie ne sunana."

"Toh ka tambayi mamanka mana" ta ce mishi tana kallon cute face dinshi
"Bani da mama" ya bata amsa a tak'aice cikin tausayawa tace "ayyah! Babanka fa?"

"Shima banda shi." Ya kuma bata amsa

"Ya subahana! Toh a wajen wa kake zaune?"

"Ba kowa"

"Ban gane ba kowa ba,da iyayenka suka rasu babu wanda ya rikeka a danginku."

"Nifa banda kowa ban san ko iyayena suna nan ba ko sun rasu.."

"Innalillahi wa inna ilaihi raju'un" ta fad'a a kid'ime tana kallon fuskar mijinta dake tsaye a bayanshi.

"Deenie bana son karya fa ya ina maka kallon yaro me hankali yanzu zaka fara yi min karya,ka gaya min ina ne gidanku su waye iyayenka."

Idonshi ne ya ciko da hawaye yace "nifa na gaya miki bani da iyaye bani da gida."

"Toh a ina kake kwana?"

Alhaji ya tambayeshi,d'aga kai yayi  kalleshi d'an jim yayi kafin yace "a masallaci ko a cikin rumfa a kasuwa."

A tare suka furta kalman innalillahi wa inna ilaihir raju'un"

"Me yasa? Ina iyayenka suka je? Ya akayi ka tsinci kanka a halin da kake ciki yanzu,wake baka abinci wa ya saka ka a makaranta?" Hajiya farida ta tambayeshi cikij tsananin kuka.

AKWAI WANI ABUWhere stories live. Discover now