Akwai wani abu page 6

1K 46 18
                                    

💖AKWAI WANI ABU💖





By Sawwama A.





Page 6.




Daren ranan Ruqayya bata samu baccin arziki ba,da ta kwanta mafarkin zai dawo mata a fresh dole yasa ta hakura da baccin ta hau sallah.

Washegari monday yayi daidai da sati biyu da dawowan sharafudden.

Sanye yake cikin uniform dinsa na wajen aiki kayan sun yi mishi kyau sosai sun karbeshi.

Gaban dogon mirror dake manne da drawer dinshi yake kallo shi kanshi ya san he is cute.

Kara kallon kanshi yayi yana kallon how handsome and lucky he is.

Bai san su wayr iyayenshi da danginsa ba but he is grateful to Allah he is handsome,intelligent and rich,not that rich but alhamdulillah tunda yana earning guminshi halaliyarsa duk ta silan wadannan bayin Allahn gabas ya kalla ya sa goshinsa a kasa yana yiwa Allah godiya.

Mikewa yayi yana duba agogon hannunsa "shit!" Yace da

Sauri ya karasa shiryawa ya fito daga d'akinsh main palor ya shiga dan yin sallama da 'yan gidan suyi mishi fatan alkhairi yau ce rananshi ta farko a wajen aiki.

Turus yayi ganin yanda Al-amin ke tsulawa Ruqayya rashin kunya ita kam jugum tayi tana kallonshi.

Da sauri deenie ya karasa ya dafa kanshi yace "haba my lil bro baka san raini bashi da kyau ba kar ka kara yiwa yaya Ruqayya rashin kunya in ba haka ba Allah zai k'onaka."

Ture hannun deenie dake bisa kanshi yayi a fusace yace "ba ruwanka da ni kar ka kara min wani magana tunda naga kai ba yayana bane."

"Alameen!" Alhaji dake gangarowa ya daka mishi tsawa  Ruqayya da deenie da namaki ya kashesu a tsaye suka mai da dubansu kan alhajin"a gidan uban wa kaji cewan shi ba yayanka bane?" Ya kara daka mishi wani tsawan.

"Ah ah Alhaji da gaskiyan yaro fa ni na gaya mishi cewa sharafudden ba yayanshi na jini bane saboda ya sani nan gaba kar ayi musu magud'i"
Hajiya da ta biyo bayan alhaji

A fussace ya juyo kanta yace "a bisa wani dalili zaki yanke wannan danyen aikin."

"To protect my children heritage!" Ta bashi amsa a takaice runtse idanu sharafudden yayi yana jin zafin maganganunta kaman an zuba mishi tafasashen ruwan zafi yana kara tabbatar da maganganun Ruqayya a kwanakin baya.

"Heritage! Heritage!" Abinda alhaji yake iya maimaitawa kawai kenan da k'yar ya iya cewa "farida i am disaplointed in you yaron da kika dauko kika kawo gidan nan da hannunki yau shi kike nunawa rashin yadda."

Kallonshi tayi ta rausayar da kai tace "ah ah alhaji baka fahimceni ba ni ina gudun abinda zai je ya dawo ne kuma ba wai ban yarda ko ina kin sharafudden bane gaskiyace kawai nake fad'a."

"Haka ns" shine kawai abinda alhaji yace kafin ya ja hannun sharafudden suka fita.

Da harara ta bisu sannan ta juyo kan Ruqayyah kallin da ta watsa mata shi ya rikitar da ita "sannu algunguma ba dai juninki munafurci ba Ruqayya toh ki cigaba kannanki zaki dinga yiwa zagon kasa ko? Ni ban san yaushe kika sauya hali ba wallahi haba."

Ita dai bata ce komi ba sai ma mamaki take yi wai itace ta canza hali lallai ma mommyn nan.

Bayan fitan su alhaji daga palon hakuri ya bawa sharafudden kafin ya mika mishi makulli.

Kallon key din yayi yace " alhaji wannan na meye?" Wata farar mota ya nuna mishi yace " tawa gudunmawar kenan na zuwa office Allah ya tsarr yayi taimako amen"

Dan jim deenie yayi dan first agenda dinshi kenan dan shi wallahi yanzu tsoron karban wani abu yake a hannunshi sun mishi babban gata tunda sun bashi ilimi.

Kaman alhaji ya san tunanin da yake yi yace" deenie kar ka damu da farida gaba daya ta sauya ko da ba ka karbi motan nan ba baza ka burgeta ba komi aka yi ba a burgeta yanzu Allah dai ya shirya ameen.

Da haka suka yi sallama kowa ya kama hanyan zuwa wajen nemanshi.

Zaman gidan deenie ya rage sosai kasancewan wasu ranakun yana off amma har karban extra aiki yake dan kar ya zauna dan free lokacin da yake dashi kuma abokin aikinshi ke taya shi neman gidan da zai zauna dan ya yanke shawaran dole ya bar gidn.

Da kyar ya samu gida kusa da airport road 2 bedroom flat mai kyau sosai haka ya cire makudan kudi ya siya.

Wani ranan sunday yana shirin tumkaran alhaji da batun gida Ruqayya ta fado dakinshi a firgice.

Kallon ta yayi mamaki fal fuskanshi kafin yayi magana tacd "yah ina so muyi maganane iys about mommy something is fishy i just saw rungume da uncle ......




Kuyi hkr DA yanayin typing din yau a sch na wuni.

Sawwama Qawwama😘

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 11, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AKWAI WANI ABUWhere stories live. Discover now