💖AKWAI WANI ABU💖
By Sawwama A.
Page 3.
Haka aka ci abinci cikin shiru babu wanda ya kara magana although Al amin da Ahmad suna ta cakulan juna amma babu wanda ya kulasu hakan ya k'ara girman mamakin Sharafudden na yadda bata tsawatar musu kan table manners da take magana akai ba.
A hankalce yake da kowa a wajen musamman Hajiya da alhaji da suka kasance masoyan da yake bala'in sha'awa sai dai yau bai ga wannan soyayyar ko kulawan a tsakaninsu ba.
A shekaru goma komi ya canza ciki har da iyayensa biyu wanda canjin bai mishi dad'i ba.
Cike da tsoro Ruqayya ta kalli hajiya tace "mommy excuse me zan je d'auko fresh juice d'in zuwa yanzu yayi sanyi" sai da ta shek'a ta fesar sannan ta gyad'a mata kai.
Innalillahi ko dai Ruqayya tayiwa hajiya laifi ne sharafudden ya tambayi kanshi for all he knows ruqayyah itace apple of hajiya's eyes meke faruwa?
Cikin nutsuwa Ruqayya ta tashi ta shiga kitchen cikin y'an mintina kad'an ta dawo hannunta d'auke da jug babba cup d'in kowa tabi tana zuba pineapple juice d'in da ta had'a da hannunta tana zuwa kan hajiya d'aga hannu alamun ba zata sha ba a gaban alhaji ta dire sauran murmushi yayi mata tare da godia.
Suna k'okarin tashi uncle mas'ud ya shigo kani a wajen alhaji sai da gaban sharafudden ya fad'i sanin tsananin tsanan da mutumin yayi mishi kallon hajiya yayi wanda ita ke kareshi kullum a wajen uncle mas'ud fuskarta fad'add'a yayi da fara'a ganin uncle mas'ud d'in yanzu sharafudden ya daina mamakin changes d'in da yake gani a yinin ranan da ya dawo kasarsa hajiya da uncle mas'ud da suke kaman wuta da audiga yau sune suke yiwa juna murmushin jin dadin ganin juna duk kuwa da kasancewar tsanar ta uncle mas'ud shi kad'ai ke yin abunsa amma hajiya bata kulashi.
"Kai ka girma ba ka iya gaisuwa ba ko? Yaushe ma ka iso k'asar" maganan uncle mas'ud ya katse mishi tunani d'an duk'awa yayi yana kallon fuskar uncle mas'ud d'in da ya koma a tamke saboda ganinshi.
Kafin yayi magana alhaji yace "kai ni ban son sakarci daga dawowan yaro zaka fara halin naka haba."
Cikin b'acin rai yace "yaya dama ai ku kuke d'aurewa yaron nan gindi yake iskancin da ya ga dama,gashi nan tunda ka tura shi waje sai da ya kwashi shekaru ya dawo ai ni ban tsammanin zaka waiwayi wanda suka tallafa maka tsintaccen mage." Ya juyar da maganansa ga sharafudden.
"Mas'ud in ka zo gidana dan ka tayarwa da iyalina hankaline the dooe is this way!" Alhaji ya daka mishi tsawa da sauri Sharafudden yace "alhaji plsss..." Ruqayya na ganin haka ta ja y'an k'annenta suka shiga ciki. Hajiya ma tasowa tayi ta matso gareshi tace "alhaji ba za a yi haka ba,ka kwantar da hankalinka ka san yanayin jikinka,maganan mas'ud fa na hanya sharafudden bai kyauta ba shekaru goma fa bai waiwayemu ba sai dai waya haba maganar sa ai abin dubawa ne."
Wani kallo alhaji ya watsa mata cikin jin zafin abinda tace yace "i hate the changes in you,first Ruqayya yanzu kuma sharafudden kaman ba ke kika insisting kar ya dawo ba amma yanzu kin zo kina biyewa shashasha ne,farida kina bani kunya these days." Daga haka ya juya ya haura sama.
Kallon sharafudden uncle mas'ud yayi yace "kai kuma...." Da sauri hajiya tace "ah ah mas'ud kai wuce d'akinka ka samu ka huta."
Ajiyan zuciya ya sauke ya koma part d'insa wanka yayi zuciyarsa fal da tunane tunane he really wants answers ya sani akwai wani abu something is defnitely wrong but what?
Hoton first birthday d'in da Hajiya farida ta celebrating mishi yake kallo a hankali komi da ya faru a shekarun baya suka fara dawo mishi.
💖💖💖💖💖💖
Shi dai bai san shi ko almajiri bane ko b'ata yayi ba ko me? Shi dai kawai ya ganshi a street he is a street boy ya kan titi yake rayuwa bai san ta ya akayi ya fara rayuwa akan titi ba shi dai haka ya tsinci kanshi.
Ba irin aikin da ba yayi tsintar robobi ya siyar kwashewa y'an kasuwa shara dako da dai duk wani abu da d'an shekarunsa zai iya.
Bacci kuwa duk inda dare yayi masa nan yake bacci ko a masallaci ko a cikin rumfar yan kasuwa duk inda ya samu nan yake kwanciya.
Baya bara amma yana bin almajirai suyi aiki wani sa'in har makarantarsu yana zuwa yayi karatu a wadu lokutab har ya rab'e ya dinga kwana dasu daga malamin ya ganoshi ake fatatakarsa sai ya koma wani wajen a haka d'an yaron da bai fi shekaru 9 zuwa goma ba yake rayuwa.
Kwatsam wata rana yaga alamajirai suna zuwa wajen wata hajiya inda zata basu ruwan gora da abubuwan sha suje su siyar ta basu ladansu.
Baiyi k'asa a guiwa ba gaje ya nema ta bashi yasha wahala sosai kafin ta fara bashi govt sec sch yake kaiwa inda yan makaranta ke siya da an tashi zai koma ta bashi ladanshi toh sai kuma washegari.
Yau da gobe y'an makaranta suka fara bashi sha'awa yaji shima yana son yin karatu zage damtsa yayi tare da cin alwashin zai sa kanshi a makaranta,sai ya zamana da an tashi yan makaranta zai je ya dad'o rowa da lemuka ya fara bin titi a haka ne wata rana Allah ya had'ashi da hajiya farida.
Zaune take a cikin mota tana jiran dawowar mijinta da ya fita siyo abu a cikin shago idonta ne ya hango mata wani yaro da yake ta hada zufs yana kokarin neman na kai
Allah wadai tayi da iyaye masu sakin y'ay'ansu haka Allah yayi musu sutura ya basu yaya amma sun yi ko oho dasu gata nan shekaru 15 da aure ba amo ba labari ko b'atan wata bata tab'a yi ba.
D'auke hawayen da ya taru mata a ido tayi har gobe tana tausayawa yara irinta tana tir da iyayen da suke zama suna haihuwa ba tare da sun zauna sun sauje hakokin diyoyinsu dake wuyansu ba.
Ya fito yaro me sayar da ruwa tayi da sauri ya tashi lokaci d'aya ya dakata saboda zafin da ya ziyarci kafanshi sakamakon fama ciwon da yaji a safiyar ranan da yayi kallon kafan nashi tayi ganin yana d'ingisawa har ya iso wajenta "kana neman kudi amma baka iya siyan takalmi ba?" Shiru yayi bai bata amsa ba.
Nawa goran ruwa?" Ta tambayeshi sai lokacin ya dago yace "naira arba'in" kallom fuskanshi tayi tace "so cute,me yasa kana sayar da ruwa amma kai ba zaka sha ba."
Murya k'asa2 yace "na riga na sha na rana sai kuma da dare" dariya tayi tace "shan ruwan ne kaman cin abinci,lokaci lokaci ake sha ai abinci ne ake mishi ci uku a ci da safe,rana da yamma amma shan ruwa ai sai dai in mutum bai ji kishi ba.
Kallonta yayi ya girgiza kai yace " abinci da safe da dare ne kawai ruwa ne so uku..." Har zata kuma magana sai ta tuna ba kowa ke samu yaci so uku ba."
Kallonta yayi yace "yaro ne a cikinki?" Idonta cike da hawaye yayin da fuskarta ke dauke da murmushi tace "ah ah amma da hakan ne da nafi kowa farin ciki." Alhaji ne ya dawo motan sai ya ganta tana magana da yaro kafin yayi magana tace. "Dan ban dari biyu in sallameshi" zarowa yayi ya mik'a mata ita kuma ta mik'awa yaron tace "gashi ka ban ruwa d'aya kaima kasha d'aya sauran canjin ka sai takalmi" godiya ya hau yi mata suka ja motansu suka tafi.
Tunda suka koma gida hajiya farida ke sheka amai nan da nan zazzabi ya rufeta dole ta sa alhaji daukanta ya kai ta asibiti abin farin ciki gwajin farko aka tabbatar musu tana dauke da juna biyu.
Lokacin da aka fad'a musu wannan daddadan labarin furucin yaron da ta siya ruwa a hannunsa ne ya fad'o mata "yaro ne a cikinki?"
*zaku iya biya kudin cigaban wannan littafin a wannan acct 4913066719 Hafsat Abbas Ecobank ko ku tuntubeni a wannan layin 09032871327*
Sawwama Qawwama😘