PAGE 1
Kai da ganin unguwar kasan akwai masu kudi saboda jerin gidajen da aka gina naji da gani. A bakin titi ne wata yarinya sai tafiya takeyi ta dauko bokiti a kanta. Shigar datayi kansa ka bayyana daga gidan data fito. Bako shakka su madaidaita ne: Ba rashi ba kudi. Haka ta cigaba da tafiya cikin sauri ba tare da shakkar komi ba. Da rana ne tsaka saboda haka ba kowa a saman hanyar domin mafi yawan mutane kan samu wurin hutu a wannan lokaci. Tana cikn tafiya ne sai wata mota bugagga ta wuceta. Motar tafiya take a hankali sai duma ke tashi sama sama. Har motar tayi nisa sai tayo baya har saida ta tsaya gab da wannan yarinyar mai dauke da bokiti. A hankali aka fara sauke gilashin. Caraf sai wannan yarinyar tayi ido hudu da wanda ke cikin motar. Ai kuwa tana ganinsa gabanta ya fadi duuumm. Da sauri ta juya da nufin komawa inda ta fito. Shi kuwa da sauri ya fito yana kiranta.
" Yasmin, yasmin, ke magana fa nake. "
Tanaji amma haka ta kyaleshi kamar bataji ba. Shi kuwa sai ya dada kara matsawa wurinta. " Yasmin Wai meke faruwane?"
" To ba ita bace." haka yarinyar ta fada tana sauri. Shi kuwa da sauri yaci gabanta. To anan ya mata kallon tsaf.
" Hahahhh! Au dama haka kike? Shine kike boye boye don kada na gane. To naga kome kuma nasan kome. Ta ALLAH ba taki ba,nan gani nan bari yarinya. Hahhhhhh." Haka ya cigaba da dubanta yana dariya ba kakkautawa. Kai da gani kasan shekarun su daya.
" Wa ma kikace ne abbanki, hhhhhhh. Yau dai na kama diyar commssioner na dibar ruwa." Haka wannan yaron ya ci gaba da tsangwamarta. Ita kuwa ta riga tasan asirinta ya tonu. Saboda haka ta kyaleshi sai tafiyarta take. Shi kuwa sai ya bita sai magana yake yana dariya tare da shammatarta saboda karyar data masa na cewa ita diyar commissioner ce tare da nuna masa cewa gidansu akwai hali domin abbanta nada mukami sosai a gwamnati. Shi kuwa kai tsaye ya aminta saboda irin yadda take shigar kece raini tare da hawan manyan motoci. Amma sai gashi yau ya kamata ta dauko bokitin nika saman kai.
PAGE 2
Haduwarsu ta farko itace a wani wurin shakatawa na kiyon dabbobi wato ( Amusement park)
Yarinya ce santaleliya ke zaune saman wata kujera ta alfarma sai murmushi take. Kai da ganin shigarta kasan nan gani nan bari. Wato mai kudi ya wuce raini. Wani table ne kusa da ita sai kayan marmari a samansa irin su dangin inabi. Tanaci tana kallon jama a dai dai. Tana cikin wannan hali ne sai ta hango wata jeep baka. Wani hadadden gayene ya fito ba wasa. Ya buga wanka over sai bouncing yakeyi. Yan matan dake wurin sai kallonsa suke wai a tsammaninsu ya zabi daya a ciki. Anan yayi banza dasu ya nufi wata hanya. Har ta debe tsammanin bazata kara ganinsa ba kawai saita hango shi ya nufota. Wani dadi ne ya lullube ta domin yau tasan batayi fitowar banza ba. Cikin murmushi da sakin fuska ya karaso wurinta yana taku dai dai. Kallon shigarta ya farayi daga sama har kasa. Daga nan sai ya fara magana
" Amincin ALLAH ya tabbata a gareki yake wannan gimbiya mai farin idanu da hasken fuska."
Anan ta dago kai ta kalleshi cikin dariya har saida hakoranta suka fito.
" Ko zan iya zama kusa dake?" ya tambaya.
" A a!" Ta fada cikin murmushi.
" To me yasa?"
" Saboda ba kai nakeso ka zauna ba."
" Hhhh. Yan mata kenan! To fadamin wa kikeso ya zauna a gurin?"
" Dadadan kalamanka sune suka cancanci zama a wannan kujerar ba kaiba."
Anan ya tuntsire da dariya har saida ya gincira da bangon dake kusa dashi. Cikin sauri ya zauna yana duban fuskarta. " Indai dadadan kalamai ne to kin samu. Ki dauka cewa daga yanxu zakijisu har sai kin gundura. To amma kafin nan ya kamata nima kiban wani abu kinga daganan sai mu amfani juna."
YOU ARE READING
REZA
HumorSirrin namiji da yadda ake cutarsa, sai da ba kowane namiji sirrin nasa yake a bayyane ba. Sunanta reza, kuma tayi fice wurin cutar da maza tare da samun abunda takeso a duk lokacin dataga dama, a cikin hakane reza zatayi mugun gamo wato haduwar ta...