PAGE 50" Ai kedai bari kande. Ai ni naji dadin wannan haduwa dake domin zamuci duniyarmu a saukake." Inji zainab.
" Hajiya da gaske?" Yasmin ta tambaya.
" Au kin aza ina wasane?" Inji zainab. Anan suka taba hannu suna kyalkyatar dariya.
Washe gari bayan alhaji ya tafi saiga yasmin ta shigo da wani saurayi a cikin gidan. Hajiya zainab na cikin falo sai taji shigowarsu. Ai kuwa tana ganinsu ta mike tsage. Kura masa ido tayi ko kyaftawa batayi. Yaron ya kasance dogo fari kyakkyawa dan shala irin wanda takeso. Wata bakar suit ce yasa ta masa kyau sosai. Anan zainab ta sheko a guje ta rungume yasmin cikin murna. " Ba sai an fada ba nasan yayi." Haka zainab ta fada bayan ta matso kusa dashi. " Dan saurayi cire glass din na gani." Injita.
Anan ya cire glass din a hankali cikin murmushi. Ai kuwa tana ganin irin kyawonsa sai ta rude. Fadawa jikinsa tayi ta wani kankaneshi sai fara a take. Anan yasmin ta tsayu tana kallonsu duk da taji kishi sosai domin itama fa..... Amma haka ta daure domin tasan zasuyi samu. Zainab din ta kasance katanya mai kiba amma ba sosai ba. Anan ta jashi daki a guje suna shiga tasa sakata kome zasuyi dai oho. To bayan shigarsu dakin kafin a fara abun sai yar hira ta barke tsakaninsu. " Dan saurayina...umyun." Haka ta fada cikin shagwaba tana karkada idanu wai ita kyakkyawa. " Au bazaka matso kusa dani ba? To bari nazo." Anan ta xauna kusa dashi ta wani jawoshi a jikinta. " To fadamin meye sunan?"
" Zaki iya kirana da audu." Haka ya fada mata amma a zahiri ba haka bane: huzaifa ne abokin yasmin reza.
" Amma fa ka hadu." Anan ta fara taba fuskarsa. Shi kuwa sai ya fara jayewa.
" Haba ya kana kaucewa kaxo mu fara mana" Inji zainab.
" Nifa kin san bana aiki kyauta. Yanxu sai ki fadamin ina kika ajiye kudin?" Inji huzaifa.
Anan zainab tayi shiru domin batasan kudin da zata nuna masa ba. Can saita tuno da wadanda alhaji ya bata. Kawai sai ta jawosu ta nuna masa." Ga wadannan muna gamawa shi kenan sai ka dauka." Ai kuwa huzaifa najin haka sai ya rungumeta kamar da gaske. Ita kuwa kyalkyatar dariya ta farayi dama abunda takeso kenan. Haka huzaifa yayita nunnugarta sai da ya bari ta kamu sannan ya saketa ya mike tsaye.PAGE 51
" Ya naga ka tashi. Zo mana dan saurayina." Inji zainab.
" Hajiya kiyi hakuri wani abune na tuno dashi,, yanxu haka jirane ake nakai wani sako amma na manta nazo nan. Ki bari kawai gobe xan zo nan sai mu cigaba.
" Haba kai kuwa ya zaka yimin haka. Sai da ka bari na farajin dadi sannan zaka tashi.' Inji zainab.
" Hajiya kada ki samu damuwa gobe warahaka zan dawo." Anan ya juya da nufin fita ita kuwa sai ta fara gyra kayanta.
" Bazaka tsaya na raka kaba."
To bayan ya fita ne sai ya tarar da yasmin tana jiran fitowarsa." Ina fatan dai ka gano inda kudin suke?" Haka ta fada cikin karamar murya don kada hajiyar taji.
" E mana tun yaushe." Ya bata amsa.
" To yanxu ya kenan?" Ta tambaya.
" Kada ki damu sai gobe zamu kammala."
Suna cikin maganar saiga hajiya zainab din ta fito. " Muje na takama kofar gida." Injita. Har sun fara tafiya sai ya tuno akwai maganar da yakeso ya fadawa
yasmin. Anan ya juyo gunta.
" Yasmin ji mana!" Injishi. Ita kuwa yasmin saita juyo tana saurarensa. Ita kuwa zainab sai tayi mamaki domin tasan cewa sunanta kande amma gashi yana cewa yasmin kuma sai gashi ta juyo.
" Au dama sunanki yasmin?" Zainab ta tambaya.
" A a ba haka bane sunanta, nine nayi subutar baki." Inji huzaifa don kada ta gane.
" Kai audu nifa a ganina kamar baka santa ba." Inji zainab.
" Injiwa ya fada miki? Ni ko na santa sosai "
" To idan ka santa meye sunanta wanda muke kiranta dashi a wannan gida?" Anan huzaifa yayi shiru domin bai san irin amsar da zai bata ba. Can sai dabara ta fado masa. Anan ya dauki wayarsa yayi kamar an bugo masa.
" Hello. Reza ya kike ya makarantar. Ina fatan dai kin shiga sabon gidan tare dani. Domin yanzu haka ina tare dake da hajiya kuma tana bukatar sanin password dinki. Saboda haka sai ki gaggauta fadamin da sauri." Yana fadar haka sai ya juya ya kalli yasmin, ita kuwa tana ganin haka saita gano cewa da ita yake. Daganan itama saita daga waya tayi kamar an kirata.
PAGE 52
YOU ARE READING
REZA
HumorSirrin namiji da yadda ake cutarsa, sai da ba kowane namiji sirrin nasa yake a bayyane ba. Sunanta reza, kuma tayi fice wurin cutar da maza tare da samun abunda takeso a duk lokacin dataga dama, a cikin hakane reza zatayi mugun gamo wato haduwar ta...