PAGE 41
" Haba alhaji kaima fa kasan cewa yarinyar tauraruwa ce kuma iri irensu taurari suna wuyar gani fa. Ni kaina kafin wannan biki nasha mutukar wahala kafin na sameta." Inji huzaifa.
" Ka. To ai wannan ba komi bane indai kudine bakada matsalarsu domin zan baka ko nawane. Ni abunda nakeso kawai shine ka kawomin ita." Inji alhaji.
" To alhaji ba matsala zan duba. Amma fa kasan tauraruwa ce kafin ka samu abunda kakeso dole sai ka bita sau da kafa. Duk abunda tace kayi sai kayi." Inji huzaifa.
" Ai wannan ba matsala bane. Kadai ka kawota ka gani. Anan alhaji ya wani gyara tsayi wai shi saurayi. " Ya kaga wannan tsayin. Nayi kuwa?"
" Haba alhaji ai ka hadu. Ko baturiya ta ganka ai dole ta yarda balle bahuasa." Inji huzaifa. A cikin xuciyarsa kuwa in banda shammatar alhaji ba abunda yake:
( Kaine dadi mata ko? Zakaci ubanka nan bada jimawa ba. Ka aza wani katon ciki sai kace kwarya) haka huzaifa yake fadi cikin zuciyarsa amma a xahiri ba abunda yakeyi in banda yi masa kirari.
" Wato alhaji zamuyi sabuwar bakuwa a gidan nan kenan!" Inji huzaifa.
" E mana bani mu tabe." Cewar alhaji. Anan suka taba hannu suna wata rawa mai ban dariya. Daga nan kuma sai alhaji ya jashi wani daki inda ya bashi kudi masu yawa.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan abu. Sai huzaifa yayi niyar kaiwa abokiyarsa xiyara wato yasmin domin su sun tayi. A cikin darene ya shigo wani restaurant sai dube dube yake. Ai kuwa bai wani bata lokaci ba ya hango wadda yake nema zaune tana jiransa. Cikin fara a ya nufi wurinta. Anan ta tarbe shi cikin murmushi da karamci. Tun kafin ya xauna ne ya fara mata kirari:
" Reza muguwar uwa, ke ka haihuwar diya ki kashe abarki. Reza muguwar uwa, ko uwarki baki ragama ba balle uwar wasu. Reza muguwar uwa, idan ba a soki don ALLAH ba sai an sonki don kaifinki. Reza muguwar uwa, ba dai mutum ba ko aljan yana shakkunki. Reza muguwar uwa, nan gani na bari yayan magori.Reza muguwar uwa, ke kadai ka gashi ki soye ki dafe kuma ki zauna lafiya. Reza muguwar uwa, ta kano tumbin giwa kodame kazo an fika "
Anan yasmin ta kyalkyace da dariyar farin ciki." To yanzu meye labarin?" Ta tambaya.
" Ai mun gama da alhaji sadi. Inaga sai dai wani ba shiba." Cewar huzaifa.
" Da kyau. Dama abunda nakeso naji. Yanxu taso muje kaga abunda na tsara." Anan ta jawo hannunsa har suka fito daga cikin restaurant din.
PAGE 42
" Yasmina reza, yasmeeeeena. Yasmeeena rezaaaaa." Haka alhaji ke tafiya yana wakarsa cikin jin dadi har ya shigo wani daki inda ya iske yasmin zaune tana jiransa. " Tab, ALLAHU AKBAR. Lalle huzaifa yayi aiki mai kyau ai yanxu ya fadamin cewa wai kina jirana. To lale marhaba ya sahibata." Anan alhaji ya zauna kusa da ita sai faman kallonta yake. " Amma fa naji mutukar dadi bisa ga wannan ziyara da kika kawomin. Kuma ina fatan ya bayyana miki komai."
" E mana ya fadamin. Amma kuma kaima ina fatan ya fadama game dani domin inada tsada sosai idan zaka iya siya to." Inji yasmin.
Anan alhaji ya kyalkyace da dariya. " Haba yan mata ai ni ko nawane zan biya indai kudine to bamatsalarki bane. Yanzu sai ki fadamin miliyan nawa zan bayar?"
" Alhaji miliyan fa kace?" Yasmina ta tambaya cikin mamaki.
" E mana ko sunyi kadan ne?" Inji alhaji.
" A a basu yiba. Ai ni alhaji wannan gida naka ya burgeni. Ace ma nice dashi dana huta." Inji yasmin.
Anan alhaji ya kyalkyace da dariya. " Ai kada ki damu yan mata indai gidane zan iya gina miki irin wanda kikeso. "
"Laaaa alhaji da gaske? "
" E mana ai gida ba kome bane. Ke har kamfani idan kinaso kin san fa inada kamfanona da yawa. Zan iya baki duk wanda kikeso." Inji alhaji.
" Alhaji kai babban mutum ne kace kanada dukiya sosai."
" Ke, ai ina fada miki bazan iya kirga dukiyata ba ni kaina." Alhaji ya bata amsa. Daga nan sai yasmin ta matse shi domin ta jawo hankalinsa.
" Shi yasa nake sonka alhaji."
A haka yasmin ta yita bugun cikin alhaji don taji tarin dukiyarsa shi kuwa yayita fada mata. Sai da ta tabbatar tasan dukkan dukiyarsa tare da inda yake ajiye takaddun mallakar kamfanoninsa da gidajensa. Haka tayi kokari wurin matsarsa da dadadan kalamai har saida ya fada mata inda yake ajiye kudinsa a cikin gidansa. Kai harda pin dinsa na ATM sai da ta sani da kuma inda yake ajiyesa. Daga nan sai tayi kara jawo hankalinsa wurin nuna masa jikinta domin ya rude. Sai da ta bari ya kosa dasu fara harka sai taki bashi. Takaddun gidajensa dana kamfanonansa ta dauko. Daga nan sai tayi rubutu kamar haka:
" Ni alhaji sadi mai katifa na sadaukar da kamfanona da gidajena da kuma waa harin dukiyata ga yasmin akan tiriliyan arba in. Kuma ta bayar da kudin har na karba." Anan ta mika masa tace idan yayi signing zata bashi abunda yakeso. Shi kuma cikin gaggawa yayi signing ya mika mata ba tare da sanin abunda ta rubuta ba saboda rudewar da yayi wurin kallon jikinta.
YOU ARE READING
REZA
HumorSirrin namiji da yadda ake cutarsa, sai da ba kowane namiji sirrin nasa yake a bayyane ba. Sunanta reza, kuma tayi fice wurin cutar da maza tare da samun abunda takeso a duk lokacin dataga dama, a cikin hakane reza zatayi mugun gamo wato haduwar ta...