PAGE 31Bayan sati uku da haduwar yasmin da maryam. Wata rana maryam na cikin dakinta ita kadai tana kallon labarai na NTA ga talabijin kwatsam sai taga wani labari mai firgitarwa kamar haka. " Innalilahi wainna ilaihir rajiun. Ayau ne muka samu labarin cewa mashahurin dan kasuwar nan mai suna alhaji sadi mai katifa ya samu karayar arziki har takai da cewa abinci ma roko yake a basa. Babu wanda yasan dalilin wannan jaraba iyaka dai malamai sunce yine na ALLAH. Saboda wannan dalili ne yasa sarkin malamai na wannan jaha yayi umarni da asa wannan labari ga media yadda duk wanda ya gani sai ya taimaka masa da addua." Daga nan sai aka nuno vedio dinsa duk ya canza yayi wani baki. Kayan jikinsa sun rine saboda datti. Wasu mutane kuma sai bashi sadaka suke naira biyar naira goma shi kuma ya dage sai amsa yake yana godiya. Wannan labari ya mutukar tayarwa da maryam hankali domin ko da dai rana bata taba tsammanin cewa irin hakan kan iya faruwa ga mai kudi irin alhaji sadi ba domin ko kyauta zaiyi to daga dubu darine zuwa sama yake bayarwa.
Batasan lokacin data saki remote din ta fada duniyar tunani akan abunda ya kawowa wannan mai kudi bala i haka ba. Tana cikin wannan tunani sai taji an yi sallama a dakin. Tana dubawa sai taga yasmin ta shigo. Anan maryam ta sheko a guje suka rungume juna cikin farin ciki. " Har na debe rai daga ganinki. A tsammanina bazan kara saki a ido ba." Haka maryam ta fada bayan ta jawota sun zauna.
" Kiyi hakuri kawata na dade inaso inaso naxo wurinki amma lokacine ban samu ba. Kin san harkar tamu ta kananan mata." Inji yasmin.
" Wai kanana. Ai ku manya ne mudai ne yara. To ya kike ya hutawarki?"
" Duk lafiya kalau."
" Kawata yanzu fa naga abun mamaki. Wai kinji cewa alhaji sadin dana fada miki cewa yana auri saki ya samu karayar arziki. Yanzu ma abinci roko yake a basa. Ni abunda ya dauremin kai shine ya akayi ya talauce a cikin sati uku." Inji maryam.
Anan yasmin da kyalkyace da dariya. "Maryam kenan. Ai wannan kadan ne daga cikin ayyukan mu. Shi kadan ma ya gani."
" Wai ko kina nufin kin san abunda ke faruwa ne. Dama alkawarin da kika dauka na cewa sai kin maida shi walakantacce kuma bawan mata ashe da gaske kike. To fadamin ya akayi kika samu damar yi masa haka?" Maryam ta tambaya.
To anan ne yasmin ta fara bata labari.
Wata rana a a cikin wata unguwa............PAGE 32
Dan saurayine ke tafiya a saman titi yayi wanka kai kace wani dan minister. Sai ga yarinyarsa a gefe suna tafiya sai tadi suke cikin annushuwa. Suna cikin hakane saiga wata mota baka ta wuce a kusa dasu. Motar na wucewa sai ta yo baya har saida ta tsaya kusa dasu. Daga nan sai wata yarinya ta fito daga cikin motar. Ai kuwa tana fitowa sai suka hada ido da wannan saurayin da yayi wanka. Shi kuwa yana ganinta saiya juya baya.
"Haba sweetheart ya naga ka wani juyawa baya?" Inji yarinyar.
"E wallahi ina dan tunani ne. Amma yanxu na tuno wani abu. Kin gane ko bari mu koma gidanku inaga kamar na manta wani abu."Cewar yaron.
"Okay ba matsala muje mana." Inji yarinyar.
To kafin su yi nisa ne sai wannan yarinyar data fito cikin mota ta fara kiransa. "Huzaifa, Huzaifa,Huzaifa."
"Laaaaa sweetheart naji kamar ana kiranka!" Inji yarinyar.
" Manta kawai bani bane wani ne can ke magana." Inji huzaifa.
" Nifa kamar muryar mace nakeji tana kiranka." Cewar yarinyar.
"Haba dear ki yarda dani mana. Kin fasan banida kowa in ba keba."Cewar huxaifa.
Anan yarinyar ta danyi murmushi. " To yayi na yarda mu tafi kawai."
Suna cikin tafiyar ne sai yarinyar nan data fito cikin mota taci gabansu. " Haba huzaifa ya kana guduna. Ka saurara kaji mana." Injita.
"Ke mahaukaciya ki rabu dani. Kin san fa na miki kashedi akaina ko." Inji huzaifa.
"Haba huzaifa ya kana fadin haka. Niface yasmin dinka ko ka manta."
"Nifa ban gane ba shin wai wannan wacece data tsayu a gabanmu?" Yarinyar ta tambaya.
" Manta da ita kawai mahaukaciya ce zo muyi tafiyarmu." Inji huzaifa bayan ya jawo hannuta. Ita kuwa yarinyar buge hannunsa tayi cikin fushi tana cewa:
" Ni ba zanje ko ina ba sai ka fadamin ko wacece ita."
Cikin fushi huzaifa ya nuni yasmin da yatsa. " Ke idan baki shiga taitayinki ba zan cimiki mutunci fa. Na fiki tashanci fa. Yanxu zaki bacemin da gani ko saina debeki ne."
" Haba huzaifa ya kana fadar haka nifa yau ba da fada naxo ba. Alheri ne na kawoma kuma inda ka saurareni duk zamu karu." Inji yasmin.
" Ke nifa ba wani alheri tsakanina dake. Ke ni har zaki dubi idona...." Anan ya kalli yarinyarsa. " Sweetheart zo mu tafi kawai"
YOU ARE READING
REZA
HumorSirrin namiji da yadda ake cutarsa, sai da ba kowane namiji sirrin nasa yake a bayyane ba. Sunanta reza, kuma tayi fice wurin cutar da maza tare da samun abunda takeso a duk lokacin dataga dama, a cikin hakane reza zatayi mugun gamo wato haduwar ta...