PAGE 21
" Aishat," Haka ya fada ita kuwa sai tayi da dai duniya batasan dashi ba. Juyawa tayi tana ayyukanta. Shi kuwa manir sai mamaki ya kamashi. Anan ya matso kusa da ita yana dubanta cike da mamaki. " Wai kada fa ince gimbiyar ce da kanta na gani ko kuwa?"
" Haba malam wai meye hakane sai wani matseni kake. To na fada ba ita bace sai ka matsa ka bani wuri ko!" Inji yasmin cikin fushi. Anan ta tashi tsaye tana ciccika.
" Amma ban taba tsammanin haka a gareki ba. Dama ashe ke mayaudariya ce. Shine harda cemin ke diyar..." To kafin ya karasa maganarsa ne sai umma ta tari numfashinsa.
" Haba dan danga. Ai ko maye akace yayi hakuri ya dangana. To balantana kai da ba mayen ba tunda tace ba ita bace sai kayi hakuri ka tafi mana."
" Au, wato dama duk abunda take da saninki kenan. Dama kece ke daure mata tana yadda taso ko. To bari kuji. Koda sama zata hadu baxan yarda ba. Alkur an sai kun ban kudina."
" To kudin naka nawane da har kake ikirarin su. Dan neman marassa kunya ka fadi muji." Inji umma.
" To idan zaki biya sai ki biya domin 3.6 million ne." Inji manir
Ai kuwa umma naji haka sai cikinta ya bada wani kulululu. Anan tayi shiru domin tasan da cewa yau fa karyarsu ta kare assiri ya tonu. Can sai ta nisa ta fara magana." Ni a ganina kayi kuskure domin ita wannan da kake gani daga gida sai gida. Ko fita batayi balantana har ta gamu da wani can."
" Ai wannan magana dagaji nasa babu kamshin gaskiya a ciki. To idan abunda kika fadi gaskiya ne ta jiyo ta kalleni mana." Inji manir.
Anan yasmin tayi shiru kuma taki juyowa. " Wato kyaleni zakiyi kenan. To wallahi kinyi kadan. Ba moriya kuma ba kudi. Wato tunda kin samu damar amsar kudin shine kika gudu daga ranar ban kara ganinki ba sai yau ko. To yau karyarki ta kare kome zai faru sai dai ya faru amma sai kin ban kudina."
" Au, wato dama kaima mutumin banza ne ko. Kune kwadayi manema mata. Idan an biya bukata sai a gudu. To gashi baka samu nasara ba ita ta samu. Kuma data biya bukatarta saita gudu. Har shine kake ganin laifinta don ta amshi kudinka. To wayace ka bata ai kai ka bata. Da ace ka samu nasarar yi mata juna biyu ai da shikenan ko duriyarka bazamu kara jiba. Shawaraki kawai." Inji umma ladiyo cikin fushi.
PAGE 22" Nifa ba ruwana da duk a abunda zaku fada ku fada kawai. Amma kudi dole sai sun fito yanxun nan a wurina nan. Barima ku gani." Anan ya tankwahe rigar hannunsa. To a wannan lokaci masu sayen waina sun fara ragewa saboda wasu duk an sallamesu. Wato a cikin rumfar dai su uku ne ke tada jijiyoyin wuya. Anan ya jawo yasmin da karfin tsiya da nufin lahanta ta. Ita kuwa tana ganin haka saita rankwada masa mari. To kafin kaceme sai suka kaceme da kokuwa. Ita kuwa umma ladiyo maburkaki ta dauko tana dukansu don su bari amma ko saurararta basayi. Manir ne ya takarkare shi a ganinsa tunda yasmin mace ce zai iya kaita kasa cikin sauki amma sai gashi abu ya gagara. Daya turata sai yaji kamar ya tura kato domin ko motsi batayi. Suna cikin hakane yasim ta samu nasarar tallabosa kamar yadda masu tallar dawo ke rike roba. Sai da tayi hajijya dashi sannan ta jefa shege cikin kwandon wanke wanke ji kake kimissss.
" Wayyo cikina." Anan ya tashi yana gurmanta. " Ke don ubanki ni zaki yiwa..." Anan yayo cikin yasmin ita kuwa tana ganin haka saita juya ta dauko bokiti mai cike da kullu. Juyewa manir kullun tayi sannan tayi jifa da bokiti tana jiran isowarsa.
" Kam bala in nan da rayuwa!, ke ni zaki zubawa kullu?"
" An zuba kome zakayi ka dade baka yiba."
Anan manir yayo cikinta da nufin lankwasheta ita kuwa umma ladiyo sai tasha gabansa. " Kul kada ka taba min diya!"
" To hala bakiga abunda tamin bane. Ai kome xai faru sai dai ya faru saina hallakata." Anan ya miko hannu da nufin ya jawo yasmin ita kuwa saita jawoshi sai ga manir a kasa ji kake timmm hakoransa na cizon kasa. To kafin ya tashine saita tallabosa kamar ta dauki dan yaro. Sai da ta nunashi a sama sannan ta makashi saman tanda. Kuma a wannan lokaci tandar ta dauki zafi sai tiriri take. To da aka jefa manir saman tanda duwayyunsa ne suka fara sauka saman tandar kafin jikinsa. Anan yayi wani ihu sannan yayi tsalle sama. " Ayihuhu." Da karfi ya fadi hakan bayan ya fado yana soshe soshe. Da sauri ya cire wandonsa bai damu da mutanen dake kallonsa ba. A guje ya nufi wani bokiti shi a tsammaminsa ruwa ne amma kash ba haka ba. Sai da yayi tsalle sannan ya dunguma a ciki. Anan yayi ihu wanda yafi na farko sannan ya fita cikin rumfar a guje ba wando. Wai ashe ruwan xafine tafasashshi wani mai shayi ya kawo a ajiye masa. To a cikinsu ne ya fada. Haka manir ya fita a guje ba wando bai tsaya ta motarsa ba balantana daukar wandonsa.
YOU ARE READING
REZA
HumorSirrin namiji da yadda ake cutarsa, sai da ba kowane namiji sirrin nasa yake a bayyane ba. Sunanta reza, kuma tayi fice wurin cutar da maza tare da samun abunda takeso a duk lokacin dataga dama, a cikin hakane reza zatayi mugun gamo wato haduwar ta...