page 1-2

603 25 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_.
☘☘ ☘☘ ☘☘

*AMATULLAH*
_baiwar allah..._

☘☘ ☘☘ ☘☘

©
ZEENAT DEEN SHAXEE
_________________

FACEBOOK
zeenat deen shaxee

WATTPAD
@zeenatdeenshaxee

EMAIL
zeenatdeens@gmail.com


PAGE 1-2

----------------------------------------

Office ne babba wanda yake,dauke da tebura guda biyu da dukkan alamu na mutun biyune ko wane bango dauke yake da hotunan samari guda biyu wadan bazasu huce 35yr ba sanye suke,da kayan lauyoyi.

Samarinne azaune akan kujera dayan ya rabbaka ta gumi wato baristah Sadiq kenan sai dayan yana kallonsa wato baristah Abdullahi.

Abdullahi ne ya kalli Sadiq yace. '' Sadiq wai mai,yake damun kane tun,daga,zuwa gidan yarin can duk kabi kawani,canza kullun cikin tunani kaki,ka tsayar da hankalinka akan,wannan 'kara kuma kai kanka kasan,cewa bamu da isheshshen lokaci saura kwana uku fa ashiga kotu.'' " Himmm kai dai bari abokina akwai wata yarinya daga gani agidan yarin wacce,bazata huce 17yr ba tayi mugun bani,tausayi wanda yazama dole yau inkoma."

" Sadiq kenan inka koma,maizakayi mata kasan irin laifin datayine kaffa kaman yanzu yara 'kanana ne kiyi mugayen laifuka kisan kai shaye - shaye raba zumunci kai hadda daba ma kai kan ai kasani tunda tare ake kawo mana karar ko kawai ka manta da zancan dan Allah muyi abunda yake gaban mu."

Cikin wani yanayi Sadiq ya kalli Abdullayi ya kamo,hannun sa ya rike sannan ya kalleshi yace." Abokina tunda kaga na damu da abun yakama ta ka tambayeni dalilina kai kanka kasani niban cika saka abubuwa araina ba ko. " " Tabbas hakane abokina gayamun dalilin in fahimta ko zan samu ta inda zan tai maka " Yauwa abokina in baka mantaba kwanaki nasha gaya miki cewa ina yawan yin,mafar kin wata dattijiwar mata tana kuka tana cemun katai maka mata dan Allah tana cikin mahuyacin hali to kullun haka rannan sai matar take cemun 'yata ce ta shiga wani haline saboda dalilina ka taimaka mun zaka ga bakar azirfa,ahannun ta mai dutse ruwan dorawa a da baki katafi kaje inda take in kaje baza tayi maka maganaba inaso kace mata zaman amana da fahimtar juna har abada. Daga nan tabace mun." tashi tsaye yayi ya juya bayan sa yayi wani dogon nimfashi sannan yacigaba da cewa." Ranar damu kaje,gidan yarin mata wannan yarinyar dana gani tayi mugun kama da wannan matar,danake mafar kinta sosai,da sosai sannan naga zoben da ta kwatan tamun kuma yanayin yarinyar dana gani yayi mugun daga mun hankali ina ganin akwai wani boyayyan lamari,atare da ita"

Jikin Abdullayi ne yayi mugun sanyi shima tashi yayi yakama abokinsa ya juyo dashi sannan ya rike masa hannu." Tabbas kana da dalilin da zaisaka damuwa sosai kuma nima nadau maka alkawarin tayaka wannan abunda ya kutso maka kuma insha Allah saimun yi nasara dari bisa dai yanzu tashi mukoma gidan yarin domum muga ta ina zamu fara."

Tashi sukayi suka futo daga office din zuwa harabar dasuke ajiye moto cinsu mota daya suka hau Abdullayi ne yake jan motar suka dau hanyar suna tafiya ahankali.

WACECE WANNAN YARINYAR KUMA MAI YAKAITA GIDAN YARI WACECE WACCE SADIQ YAKE MAFAR KI WAYE SADIQ DA ABDULLAYI MAZAI FARU

KUD ZAKU SAMI WANNAN AMSAR ACIKIN WANNAN LABARIN.

AMATULLAHIWhere stories live. Discover now