page 23-24

133 6 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

_We are here to Educate motivate and Enterain Our Readers..._

☘☘ ☘☘ ☘☘

*AMATULLAH*
_baiwar Allah..._

☘☘ ☘☘ ☘☘☘

©®
*REAL SHAXEE🍒*

*EMAIL*
zeenatdeens90@gmail.com

shaxeezeenatdeen@gmail.com

*wattpad*
*@Real_shaxee*

*Instargram*
*Real_shaxee*

*PAGE 23-24*
___________
" Zan fara baka wasu labarin amma wasu kuma anty ce zata bayar dan haka ke yakamata kifara tunda kece babbar mu kinfimu sanin mafarin komai." murmushi tayi sannan tace." To ai shikenan dafarko dai nima natashi nagannine a GIDAN MARAYU gidane babba akwai bangaran rainon jira jirai akwai bangaran maza samari da matasa da kuma bangaran ofice din da ake zuwa domun amsar yaro dakuma kar barsa akwai bangaran gidan ma aikata sai kuma can ciki makarantar boko ce da islamiyyah sai bangaran wasan yara da manya shugabar gidan sunanta Hajiya Rashida sai mate makiyar ta muna ce mata Umma Hannatu na tsinci kainane aciki ina yar shekara goma sha daya rayuwar gidan gatanan dai ana aikata barna kala kala wata rana ina zaune sai aka aikeni office dan inkai wata takadda da sallama na shiga inda naga wasu maza guda biyu magidan ta dayan da jinjiri a hanunsa tsayawa nayi ina kallon jinjiri saboda kyakykyawane jinayi dayan yace." " Hajiya wannan jinjirin akofar Gidana aka ajiyeshi da kuma wannan agogon wanda da dukkan alamu na gwalne mai tsada saikuma wannan zoben azirfar anyi rubutu ajikin takadda ansaka sunansa Sadiq Abubakar MS to shine mukaga yakamata mukawoshi nan." Hajiya Rashida tace." To yanzu bara muti rubutu atakadda kusaka hannu sannan mu amsheshi." rubutu tayi na ranar da aka kawoshi dakuma takaddar da aka rubuta sunansa akasaka acikin fayal din aka dau photon wadan da suka kawoshi da hoton jijirin suka saka hannu aka saka agogon da zoben a laida akasaka a fayaldin aka ajiye sukuma suka futo Hajiya ta kalleni tace." Maza daukeshi kikaowa Nani din datake kula da jarirai kibata shi kice sabone sunansa,Sadiq." " To Hajiya." nadaukeshi nafuto anan naji wata magana da wadanda suka kawo Sadiq suka ce wadda nariketa har yanzu nahuce natafi bangaran da ake kula da jarirai nashiga inda na tarar da duka Nani din guda biyu sunata sharar,barci dayace mai suna Lami taketa faman kula dajira jiran wasu suna kuka wasu sunyi kashi sai ta gadama take cirewa wanda yayi kashin naje nayimata bayani tace." Ajiye dan banza awancan gadon kullun sai ankawo irinsu amma ba a kara mana albashi taya zamu iya kula dasu." na kalli,gadon data nunamu yayi kura sosai ko zanin gado babu na kalleta nace." Nanii nidai zan dinga kula da Sadiq dan Allah kibar mun shi." tabee baki,tayi tace." Wannan kuma matsalar kice kekikaga zaki iya wahala kije kitayi dama sunyi mana yawa jeki sashi uwar kini bibi." ku lallonta ban kara yiba natafi dakinmu dashi kan kati fata nakaishi inda har yanzu barcinsa yake gwanin sha awa yana cikin kaya yan kanti masu kyau da tahul far mai laushi sai kallonsa nake yanzu kuma nafara tunanin mai zan bashi inya tashi dasauri nakoma office din Hajiya. " Hajiya na gayawa nani komai akan yaron amma na amsheshi nizan dinga kula dashi adakina yanzu abani madarar sa inya tashi in bashi."" Ke har nawa kike dazaki iya kula da yaero kodai kini bibine kawai dason gwaninta ai sai kitayi ga wani gwan gwanican namadara ki dauka da fida daya kuma in madarar ta kare kifara bashi abinci dan bazan iya wannan kashe kudinba maza jeki." jikina ba kwari naje na dauka nafuto wai bazata iya kashe kudiba abunda gwamnatice take yi haka dai nadawo nasamu ruwan zafi a kicin nadama masa kasan cewar akwai arubuce ajikin gwangwanin kuma na dan iya karatuna yana tashi nabashi yasha sai kuma yaci gaba da bacinsa wasu daga cikin yan dakinmu sai hantarata suke wai zan damesu da kukan yaro wau kuma sunata yaba kyansa dadaddare inata tsoron kar yaita kuka amma kuma baiyiba dasafe dazan tafi makarantar boko nakaiwa Nani shi akan tayi masa wanda kuma tarikeshi har nadawo.

Haka natafi inata tunaninsa ana tashinmu nahuce dan insaukeshi abun mamaki ko wankan batayimasa ba yanata kukan yunwa ita kuma tana ta kallonta a tv bance mata komai ba na daukeshi na nufi kicin dinmu gun mai dafa mana abunci wato Umma haka muke ce mata." Umma kinga nani taki yiwa Sadiq wanka sai kuka yake." murmushi tayi tace. " Kinsan halin gidannan Mariya bazata yimasaba nagunsu ma bayi musu sukeba sai sun kwan uku ko hudu kawoshi inyi masa kuma daga yau insai zakije makaranta kidinga kawomunshi inrike miki shi kinji 'yata." murmushin jin dadi nayi namika mata shi natafi.

Haka kuwa akayi kulkun inzani makaranta sai in kaimatashi dana duskanci madarar sa takusa karewa gashi kayansa biyu tal aduniya sai na dage akan sa na ar da akeyi agidan sabulu basilin shirya dan kunbe dinkin hula da soso kullun cikin aiki nake,har natara kudina dayawa agun Mama da kanta taje tasiyo masa madara dara harda kaya da nafkin naji dasi sosai haka naci gaba da rainon sa har yafara koyan tafiya yayi wayo sosai dukda kullun cikin furgicin kar masu daukar yara suzo su dauke mun shi saboda kyansa kuma bulbul dashi ahaka har yayi shekara hudu yafara zuwa makaranta nikuma nakusa gama sokondiri na inshiryashi inna kaishi tasu sai inhuce tamu.

Sadiq yanada ahekara shida zuwa sannan nagama makaranta inada burin cikaba da karatu amma bayadda zanyi domun Hajiya tace saidai inyi komai da kudina dakuma kaina bazata iyaba nikuma kudin danake tarawa na Sadiq ne dana ke saimasa kaya da abunda yake bukata wata rana da daddare muna zaune nida wata kawata Ummi halinmu daya komai tare muke da ita burinmu nacigaba dakaratu daya amma mun hakura suk shaku da Sadiq itama mun gama hirar mu a kusa da wata bishiya nace tazo mutafi tace muje nida Sadiq mutafi ita Hajiya tana kiranta zataje gidan ta mukatafi itama ta tafi shiru shiru har wajen awa uku bata dawoba gashi Sadiq yafara barshi natashi ina haska 'yar cocilan dina har nazo kofar dazata sadani da falon Hajiya din ina kokarin shiga naji ana magana nayi saurin kashe futilata nalabe naji hajiya tana cewa." Alhaji dafatan komai yayi daidai ko."

muryar wani naji yana cewa." Kai Hajiya narasa ma irin godiyar dazan miki yarinya tayi sosai danya shakaf da ita kuma ninafara budeta ammafa tayi mun gadda taki yadda dani dan haka nayi ma fyade kawai nama jimata ciwo ungo dubu ishiri akaita asibiti wannan kuma nakine." " Ai Alhaji nasan budurwa kakeso shiyasa nasamo maka." " Hakane Hajiya aini inna yi amfani da yarinya sau daya bana sakewa bara intafi,dare yanata yi sai kin kuma jina." " To alhaji Allah yakiyaye." labewa nayi ina kuka har ya huce bai ganniba nayi saurin shiga dakin naga bakowa dan haka na kutsa kai cikin uwar dakin naga Ummi cikin jini dakyar take numfashi gawaye yanata zuba Hajiya ta daga kai ta kalleni." To muna fuka saida kikazo ko to wallayi indan naji maganar nan tafuta sai na batar daku kawai kuce wasune sukayi mata fyade kuma baku sansuba." ina kuka na gyada mata kai muka saga Ummi takaita bandaki ta yimata wanka ta gasata tabata shayi tasha taba farasitamol ta sha na riko Ummi muka dawo dakin mu.

AMATULLAHIWhere stories live. Discover now