page 33-34

123 7 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

☘☘ ☘☘ ☘☘

*AMATULLAHI*
_baiwar Allah..._

☘☘ ☘☘ ☘☘☘

©®
*REAL SHAXEE🍒*

*EMAIL*
zeenatdeens90@gmail.com

shaxeezeenatdeen@gmail.com

*wattpad*
*@Real_shaxee*

page 33-34

____________
Murmushi Ibrahim yayi sannan yace." 'Yan uwa na mun sami bakin zaran nan fa damuketa naima yanzu muje gida indakko muku shedar hotel din dana samo ahada su saura abu daya da ace zamu samin koda sunan unguwar sune ko garinsu to da hakan zai taimaka mana." Hakanane kuma amma abunda nake tunani shine mufara zuwa unguwae su Alhaji Hashimu mudanyi wani bincike hakan zai tai maka mana.'' Sadiq ne yake fadar haka sallama sukayi da doctor suka futo tun d'azu doctor Ahmad yake kallon Sadiq har suka fura da sauri yadaukko wayar sa yakira wata nomber jim kadan aka daga." Daddy naga wani abu mai matukae daure mun kai ayau." daga can wani magidancine daga jin muryar sa akwance yake yana fama da ciwo cikin dauriya yace." Yarona mai kuma kagani ko wani mara lafiya aka kawo mara galihu indai,hakane kabiya da kudinka ayi masa magani kaji yaro na." murmushi yayi sannan yace." A a daddy yau naga wani matashi sunzo guna akan wasu marasa lafiya daddy yadda kasan kaine sanda kana yaro kamarku tayi mugun baci kuma daddy sunan sa Sadiq." daga can azabure mutumin yace." Bashakka Sadiq dinane ganinan zuwa kace yajirani." cikin kuka mutumin yake magana shima doctor kuka yasa ka sannan yace." Daddy sun tafi amna zan bisu inga gidansu sannan ayi bincike agano shin ko yaya nane Sadiq duk da inada tabbacin cewa shine domun kuwa naga shedar daka nunamin ahoto tsagar jikin kunnesa kazauna asibitin daddy insha Allah zan kawo maka shi har london din."

" Ahmad nawarke wallahi zanzo in ganshi da kaina kajirani kawai ganinan." sauri doctor Ahmad yayi yace." Indai katawo Daddy to bazan taba nuna maka shima kazauna aikin da za ayi maka gobe yanada mahimmanci arayuwarka nima gobe zan tawo london din kuma nadaukar maka hotonsa bai saniba zaka gani goben." " Shikenan yarona Allah yayi maka albarka ina jiranka." kashe wayar doctor Ahmad yayi tare da kifa kansa akan tebur yana kuka kofar office dinsa yaji an kwankwasa yayi saurin gige hawayensa tare dacewa." shigo."

Su Abdullahi suna futowa suka dau hanya basuyi nisaba anty tace." Nikwa akwai wata rana muna hira naji Amatullahi tace mun ita yar garin kakano ce unguwar dorayi amma shekaru uku da dawowar su garinnnan saka makon wani ifla i daya samesu." " Alhamdulillah." suka fada gaba dayansu jejin su suka je suka zauna anty tadafa musu abinci sukaci sannan ta kallesu tace." Daga yau kowa acikinmu ya daina futa da rana sai dare shima saiya badda kama gudun samun matsala kun gane." dukansu sunyi na amda hakan dare yanayi Ibrahim yadau lopton din sa yahau bincike wani ihu yasaka tare da dariya." Mai yafaru Ibrahim." dukansu suka fada cikin furgici." Kuzo kuga nasamo mana hotunan yar Alhaji Hashimu ta gasken sunanta itama Amatullah." dukansu sukazo sukagani hotunantane ita da babanta harda ummanta da kaninta saikuma nata dana kawar ta danata ita kadai.

" Kai amma nayi mugun jin dadi domun hotunannan samunsu kamar gama aikinmune." Kaidai bari sanda nake bincikena nafarko ne nahada kawance da kawarta batare da tasan kudirinaba cikin dabara nace ta turon pic,din aminiyarta to bayan kashemun iyaye da akayi na manta da batun sai yanzu dan haka daga yau zamu fara aikin mu.'' shawara sukayi suka amunce sannan anty t tabada pic,din Amatullah ta gidan yari aka hada da pic din Alhaji,Hashimu wanda yayi da yarsa suka rubuta akasan pic din

"Shin acikin wadannan wacece yar gidan Alhaji hashimu ta gaske wacce aka yankewa hukunci ko,kuma wannan kokuma yayan sa biyu maau suna daya muna son sani." suka tura cikin awa daya abu yadinga yawo agar a a cikin dare saiga maganar ana haskota agidan type,da kuma gidan redi'o.

Dan dad'i har rawa sukayi sai 12:00 suka yi barci washe gari suna karyawa suka kunna inji suka fara kallon labarai abun jiya lipton kowa ya dakko tasa yabude duk dai zancan akeyi nan take Aibarahim yadakko video sanda ake shiga da amatullah gidan yari da kuma maganar da dasuka nada ta likita suka tura tare da daukar pic din takaddun amsar iyayen Amatullah a asibiti suma tura wayyo gari ya dauka yan jarida sukayiwa doctor Ahmad kaura suka sameshi shikuma alokacin yanata naiman Sadiq yaje gidansu ance ankwana biyu ba a gansuba yanaji abunda 'yan jarida suka fada yagane sune dan haka takara maimaita abunda yafada tarw da tabbatar musu sa cewa iyayen Amatullah ne wannan har video da ake nada a asibitin yadakko ya datso komai yabawa yan jarida domun shi burinsa Sadiq ya gani yazo koda yimasa godiyane shina yayi abunda akeso nagano shi wanene.

Alhaji Hashimu han kalinsa yayi mugun tashi domun bullowar wannan maganar wayar sa kawai aketa kira yama,daina dagawa matarsa hajiya Halima itama hankalinta ya tashi." Alhaji wai wanene yakeson tona mana asirine in kudi yakeso yafuto ya fada mubashi nidai nashiga ukuba 'yar tawa akeson kashewa." " Hajiya akwai wasu lauyoyi guda biyu aikinsune dan sunfara bibiyar lamarin nadauke shugaban masu kula da gidan batare dasun sami wani bayani agun saba na dauke yarinyar amma ashe hakan duk bazai yiba wanene yagaya musu lamar taya suka gano wannan abu buwan kuma anrasa inda suke kwata kwata suncire layinsu sunbar gidansu sun hada kai da wannan lauyan na baya." Kace abun babbane to wallayi dole mutashi mu kamosu mu kawar dasu domun gudun bacin rana akama yan uwansu mana.'' " Yauwa hajiya kin kawo shawara bara in futa in tura su Goga su naimo su." tashi yayi yafuro daga falon zuwa harabar gidan yadau mota mai gadi yayi saurin zuwa yace masa." Alhaji karka futa yan jarida sunan acike a kofar gidan wai sunason magana da kai." dukan kan sitiyarin yayi yafuto daga motar yakoma cikin gidan.

WANENE ALHAJI HASHIMU?

AMATULLAHIWhere stories live. Discover now