page 27-28

114 7 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

_We are Here to Educate Motivate and entertain Our Readers ..._

☘☘ ☘☘ ☘☘

*AMATULLAH*
_baiwar Allah..._

☘☘ ☘☘ ☘☘☘

©®
*REAL SHAXEE🍒*

*EMAIL*
zeenatdeens90@gmail.com

Shaxeezeenatdeen@gmail.com

*wattpad*
*@Real_shaxee*

*Isntargram*
*Real_shaxee*

*DEDICATE TO*
*my sistar Binta Umar😍❤*

*PAGE 27-28*
____________
Gashi magaruba ta gabato sai tafiya mukeyi ina goye da Abdullayi na ri'ke sadiq·

" Momy wai ina zamuje ne sai tafiya mukeyi·" Sadiq ne yadawo dani daga dogon tunanin dana fad'a." Kaga yanzu zamu je inda zamu kaji mun bar wancan gidan saboda mugayene kaji kaidai kadaure mu tafi kar ka gaji." haka muka cigaba da tafiya har nazo wata unguwa naga wani saurayi yana alwalar sallar Isha'i kasan cewar tagabato na karasa,kusa da shi." Dan Allah bawan Allah kokasan gun wani wanda yake bada hayar gida ina bukatane ga dare yayimun." kallo na yayi da alamu ya tausayamun."Kinga baiwar Allah makocinmu yana bada haya awancan gidan muje inrakaki gunsa Allah yasa akwai daki gidan baicikaba.Ameen." nace sannan yataso yadaukar mun Sadiq muka karasa gidan muna zuwa mukaga mutumin ma akifar gida yagama Alwala saurayinne yayi masa bayani shikuma ya kalleni yace." Baiwar Allah daga ina kike inason sani kafun inbaki gurin zama saboda kinsan duniya ta lalace." nagaya masa gaskiyar labarina har kwallah yayi sannan yace." Bashakka ke jarumar macece kuma Allah tatayaki rikon yarannan muje ga gidancan kuma kizauna kyauta wasu wata ukun masu zuwa zaki biyani dubu uku da dari biyar." godiya nayi masa sosai mukatafi harda wannan saurayin gidane mai dauke da dakuna shida kowanne akwai bandaki aciki kicinne a tsakar gida babba kowa zai yi girkinsa anan mata ukune aciki duka sunada aure tanunamun dakina tare da gabatar dani amatsayin mijinane yamutu yabarni da yara kuma iyayena ba yannan garin bane sun tausayamun sosai nashiga dakin na ari tsintsita natsare dakin tas wata ta kusa da dakina tabani tabarma haka muka kwana anan ahaka nidai barcin rabi nayi donun tunanin wace irin rayuwa zamuyi amma kota halin 'ka'ka saina tallafawa su Sadiq koda ni zan cutu.

Safiya tanayi matan suka bamu cocon da 'kosai naji sadi sosai daga gani zan ji dadin zaman gidan dan haka na ce sukwatantan kasuwa dan inje,insiyo mana abun bukata suka kwat daya makociyar tawa ce mai suna Hasiya tacemun aikwa yau zataje kasuwa tashirya mukaje nasiyo mana laidar daki da tukunya da risho karami sai bokiti da kondon wanka da yar gana masgo babba sai nase ludayi daya faranti babba da karami sai cokali biyu kofun shan shayi uku nasiyo mana shinkafa yar hausa da dan cefane muka dawo Hasiya ta tayani shiya dakin tabani wani kwandon kife kwanuka karami da muciya dawasu kwanukan da kayan sawa kasan cewar taga banzo da ko dayaba sai dai nasu Abdullah dana debo nayi godiya sosai.

Darana nayi mana dafa duka nayi musu wanka bamu da man shafawa inajin kunyar tambayar mutanan gidan saboda kar daga zuwana infara roko nayi shiru dama nasiyo mukuli karami na kulle nafuto danneman sana ar yi awaje naci karo da wannan saurayi muka tsaya muka gaisa." Ina zakije anty kuda kuke baki aunguwar mu." murmushi nayi nace masa " Kaga zanfutane inzaga kozan samu sana ar yi zama haka bazai huyuba saboda abunci da makarantar yarannan." " Hakane Anty muzauna anan muti wata magana."

Muka zauna awani tudun gida yadauki Abdullah yasa acinyar sa." Dafar ko dai ni sunana Shamsu wancanne gidanmu inada kanwa Na'ima ayanzu naiman wani aiki zai dan dau lojaci kan kisamu dan haka ga shawara mai zai hana in baki araon jari kifara abincin siyarwa duk unguwar nan ba ayi,kuma munada samari dayawa da masu shaguna,ga almajirai amma zo muje gidanmu muyi shawara umman mu bata da matsala." tashi mukayi mukaje gidan dattijuwar ta amshemu hannu bibbiyu da mai gidan ma kasan cewar Shamsu ya basu labarina yagaya musu shawarar da yabani yanzu sukayi na'am da ita tare da bani goyen baya dakuma yimun fada duk halin dazan shiga inrike mutuncina amatsayina na mace kuma musulma naji dadi sosa tare da Na'ma muka tawo munsha hira da ita munsaba sosai dab da magariba ta tafi.

Da safe natashi naje sasiyo mana gasara da sugar da kosai nadama mana muka karta ina zaune muna hirar yara nida su Abdullayi domun ya iya surutu saiga Na'ima da kaya niki niki tashigo dasu su shinkafane da cefane inji babansu wai infara sa nar da kadan naji dadi sosai tare da ita muka futa muta tallan abunci za a fara yau kuma ina kara ganin gari.

Muka dawo ta tayani muka dafa shinkafa da miya da taliya da salat muka futo kofar gida muka share nasa kujera muka jera kulolin da Shamsu yadakko mana agidansu shima yayi mana talla sasai cikin sa a kuwa basai ga mutane sunata diddigowa ba kafun yamna abunci yakare gar ana naima naji dadi sosai.

Washe gari nikadai nayi aikin kimai amma na kara yawan abunci nan da nan nakusa siyarwa duk wanda yazo ina masa tallan wainar shinkafa zanfara gobe suna cewa aikwa zasuzo saboda abunci na da dadi da tsafta aikwa naje mayi cefane nabiya gidansu Na'ima nagaya musu umma tabani tandarta babba na dauki su Abdullahi muka tawo dama nan nake kaisu inzan futa nazo tundarw nayi miyata na jika shinkafa muka kwanta da suba na tafi nakai markade na hada komai nafuto waje nadasa murhun waina saida nafara yiwa su Sadiq suka koshi suka tafi gidansu na'ma tas nasiyar da abata nayi wanke wanke nadora girkin rana nagama nashiya gun saida abinci nayi wanka nazubawa su Sadiq sukaci suka koshi nashiryasu nakaisu makarantar islamiyya nadawo nafara saida abincina ina gama sain yi wanke wanke inje inyi cefanan waina in tawo da su Abdullah daga makaranta mutawo gida.

Haka naci gaba da rayuwa yanzu kam har karifa karama da kwaba da wasu abubuwan bukata nagida rayuwa tayi dadi inda nasai firij nafara saida sobo da kunun aya mutanan gidan kuwa muna zaman amana dasu inda Hasiya tabukaci tadinga tayani girkin ina biyanta yafi zaman banzan datake garashin dasuke fama dashi nakwa ji dadi muti girkin tare tayi wanke wanke infuta insiyar ahaka nasamu yan aiki masu tayani saida abincin su biyu saboda abun yayimun yawa su Sadiq kuma gudun in barsu agida su kadai nasasu amakarantar huni tun safe zan musu komai intafi kaisu Hasiya tafara aiki danazo sai muci gaba
ina gama siyar wa kuma sai in je in dakkosu yara sunzama abun sha awa basu rasa komaiba.

Ahaka muje zaune cikin jin dadi da kaunar juna maza dayawa sunzo aurena naki dimun bashine agabanaba yarana ne agaba inaso suyi rayuwa mai dadi.

Ahaka har nasai filina nafara gini abuna gwanin sha awa.

Kwasam sai mai gidan damuke ciki ya mutu ma gada suka bukaci abasu gidansu narasa inda zan saka rayuwata

TURKASHI KO WACE RAYUWA SU SADIQ KUMA ZASU FA

AMATULLAHIWhere stories live. Discover now