4

6.2K 369 21
                                    

_*RASHIN SANI.......*_

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

4⃣

Suna isa k'ofar office d'in gabanta yayi muguwar fad'uwa,
amma ta dake dan kar Khulud ta fahimci halin datake ciki,
Sanah na niyyar danna kai, Khulud tayi saurin rik'o ta had'i da cewa " ke wai meyasa kike haka ne?

Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " me kuma nayi?

Khulud tace " amma sanin kanki ne ba'a shigar masa office kai tsaye ko?

"Tunda a gabanki ko head girl ce tazo tsayawa take a bakin k'ofa, ta fara yin sallama kafin ta shiga ,
sannan ta tsaya har sai ya bata izinin shiga,
kuma ma ko ba haka ba ai bai dace ace kin shigar masa office kai tsaye ba,
Sanah tace " to amma kema ai kina ganin yadda yake shanya mutane a cikin rana, sai ya mula ya mulmule kafin ya bawa mutane damar shiga office d'in,
kuma ni gaskiya kin san ban iya jira a rana saboda tana iya sani ciwon kai,
ta k'arasa maganar tana zumb'uro baki,
"ko ma dai miye ai sai mubi doka da k'a'idarsa dan mu zauna lafiya dashi,
tunda haka muka ga sauran students nayi, ba kuma fin su mukayi ba,
rolling idanta tayi sama had'i da dafe goshinta, tace " to naji yanzu dai sai kiyi masa sallamar,
mu kuma muyi ta zama anan har sai sanda yaga damar damu izinin shiga,
duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Khulud Sir Moli na jinsu,
murmushin takaici yayi cike da mamakinta,
girgiza kai kawai Khulud tayi batare data kuma cewa komai ba ta k'arasa gaf da k'ofar tayi sallama,
ga mamkin Sanah sai ji tayi ya amsa had'i da bada izinin shiga,
kallanta Khulud tayi tana yi mata alamar kinga ni ko, da idanta.

"Assalamu Alaikuma Khulud ta kuma fad'a lokacin da suke shiga,
batare daya d'ago ya kalle su ba ya amsa,
baki Sanah ta tab'e a ranta tace " majhulil hali,
duk abinda take yana kallanta,
dakyar ya bud'e baki yace " meya hana ku zuwa d'azu?

Kai tsaye Sanah tace " gani nayi during class hrs ne shiyasa nace kar muzo,
batare daya bud'e idansa ba ya kuma cewa " uban wa ya ku izinin tafiya jiya?

Nan ma kai tsaye Sanah tace " ni ce!"
saboda me? ya tambaye ta a tak'aice,
"Lokacin salla ne yayi, shiyasa nace, ya kamata ace muje muyi sallah, sannan munci abinci,, ta k'arishe maganar kanta a k'asa.
A hankali ya bud'e idansa ya zuba mata batare daya ce komai ba,
leb'e ya cije saboda yadda take bashi amsa kai tsaye, wani irin tsanarta yakeji na ratsashi, dan ya tsani rashin tarbiya, ya kuma lura yarinyar bata da kunya, cikin isa ya mik'e zaune daga kishingid'en dayake ya kalle ta,
yace " ke 'yar iska ce ?

Ido itama ta zuba masa batare data ce komai ba,
ya kuma cewa " ke wacce iriyar fitsarerriya ce?
a gidan ku babu manya ne?ko suma iyayen naku basu iya magana da manya ba?
balle su koyar daku tarbiyyar iya magana da manya?" Fuska ya kumatsukewa tare da cewa:
"Amma ina ganin kamar a gidan ku kowa zaman kansa yake yi ba babba ba yaro ko!?"
yayi maganar duka a lokaci d'aya,
ba Sanah mai bak'ar zuciya da zafin rai ba,
dai-dai da Khulud mai sanyin rai sai da maganganunsa suka saukar mata bak'in ciki da b'acin rai,
take idanuwan Sanah suka canja launin su daga fari zuwa jajaye,
ya kuma kallanta yace " fool an idiot,
stupid girl kawai, ke har wata shegiya kike d'aukar kanki ko?, to bari kiji ba gagarerre sai barerre,
ke a cikinfitsararrun ma wacece ke?
'yar tatsitsiya dake sai fitsara, shigiya empty head,
kanki ba komai sai rawar kan banza,
daman k'anan yaran nan kunfi manyan 'yan mata iya iskanci,
'yar iska ko majinar hancinki baki gama iya cireta ba, amma har kin fara zubdawa wasu jini a jiki, woto ke gaki yar sara suka, zaki b'ata mana tarbiyar yaran makaranta daga zuwanki ko,
wannan iyayenki idan basu da gaske ba, Uwar yan daba zaki zama,
jacakar banza".
iya bak'in ciki da takaici Sanah ta k'unsa,
saboda tsabar yadda take jin zuciyarta na tafasa,
jikinta har tsuma yake, mak'ogwaronta ya bushe rak'ayau, idanuwanta suka koma asalin red,
ta kafe shi da ido cike da tsantsar fitsara bata ko k'ifta idanta,
ya kalli Khulud dake durk'ushe tana hawaye, yace " Jeki kira min head girl, da Era,
cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita,
ya mayar da kallansa ga Sanah yaga har lokacin kallansa take yi kurrrr ko k'iftawa batayi,
ganin yadda lokaci d'aya ta birkice, kamanninta suka sauya ne ya d'aure masa kai,,
a ransa yace " lalle yarinyar nan nada bak'ar zuciya.

RASHIN SANI......!!! Where stories live. Discover now