52

5.4K 315 92
                                    

_*RASHIN SANI.......*_


*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

5⃣2⃣

BAYAN WATA HUD'U

Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na wucewa,
yayinda cikin Sanah ya girma sosai,
dan har ya shiga watan haihuwar shi,
tun ranar da aka cewa Khulud Sanah nada ciki bata k'ara barinta tayi komai ba,
dai-dai da ruwan wanka ita ke had'a mata,
har wankin under wares ita keyi mata,
abinci kuwa har kan gado take kawo mata,
taci ta d'auke kwanan, duk abinda kuka sani na rayuwar yau da kullum Khulud ke yiwa Sanah,
bata barinta tayi komai, even massage Khulud ke yiwa Sanah,
koda Sanah nasan yin wani abu Khulud bata barinta tayi da kanta, ita keyi mata.

Sosai Sanah tayi mugun sabo da cikin jikinta,
ta shak'u dashi sosai, Allah ya kuma jarrabe ta da san abinda ke cikinta fiye da komai a duniya,
babban burin Sanah a rayuwarta bai wuce taga abinda zata haifa ba,
wani irin mugun so da k'aunar shi take yi,
da tayi zaton bazata tab'a san wani cikin duniya sama da Sir Moli da Khulud ba,
amma sai gashi Allah ya jarrabeta da mugun son abinda ke cikinta,
Khulud Sanah sai tayi kukan bak'in da takaicin,
tana gaf da rabuwa dashi, daurewa kawai take yi,
saboda Khulud da kuma yadda take kula da ita,
amma deep down bata tunanin akwai abinda zata rabu dashi a duniya taji zafi kamar abinda ke cikinta,
kwanakin haihuwarta na matsowa matsananciyar damuwa kan cikin na k'aruwa,
sosai tayi muguwar rama ta k'ek'ashi,
tayi bak'i, ta zama shiru-shiru so silent,
kullum tana cikin d'akin tana kuka.

Fuskarta d'auke da murmushi ta shigo d'akin ta kalli Sanah dake zaune saman sallaya,
da tsohon cikinta tace " my Sanah nan zan kawo miki abincin ko parlor zaki ci....!?

Murmushi itama tayi mata kana tace " a'a ba sai kin kawo nan ba,
ki bari zan fita parlor'n, sai dai idan Hanash yana kan hanyar dawowa,
_(dan har yanzu Hanash bai sai da zaman Sanah cikin gidan ba)_ ,
" a'a ba damuwa tashi muje can d'in kici,
ta fad'a tana rik'o ta,
"kai my Khulud dan Allah ki rink'a bari ina motsa jiki na,
amma komai ace sai kinyi min,
murmushi kawai tayi batare datayi mata magana ba,
tana tallafe da ita har suka k'arasa parlor'n,
zaunar da ita tayi a saman sofa a hankali,
kana ta kawo stool ta d'ora k'afar Sanah sama,
kitchen ta koma ta d'auko tray d'in data shirya abincin Sanah kana ta dawo ta zauna kusa da ita,
ta d'ora abincin akan cinyarta had'i da d'ebowa cikin spoon takai bakinta,
murmushi Sanah tayi gami da mik'a hannunta zata karb'i cokalin,
tace " please yau dai ki barni naci da kai na,
murmushi Khulud tayi mata tana kuma kai spoon d'in bakinta,
" wai meyasa baki gajiya da aiki ne....!?

"Gaba d'aya aikin gidan nan fa ke, ke yinsa,
kwata-kwata baki hutawa ranki,
idan kika tashi tun asuba baki kuma komawa bacci,
ga gyaran gida, ga girki ga kula dani da Hanash haba abin yayi miki,
gashi kink'i yarda a d'auko mai aiki,
Sanah ta fad'a cike da tausayawa dan tasan uban aikin da Khulud keyi ita d'aya,
murmushi Khulud tayi tace " idan banyi miki ba waye zayyi miki my Sanah...!?

"Ai ni nafi kowa cancanta nayi miki, komai a rayuwa,
" amma my.....!
"dan Allah karki ce komai kici abincin,
ta fad'a tana kai spoon d'in bakinta,
ba musu Sanah ta bud'e bakin ta amshi abincin,
sai da ta k'oshi kana Khulud ta mayar da kayan abincin kitchen,
ta dawo kusa da ita ta zauna tace " munyi waya da Papu fa...!
"kai haba yaushe...!?

" D'azu ya kira ni yace " EDD d'inki ya nuna saura 15 days ki haihu,
"Ok to me yace...!?

" Wai zai turo a amshi passport d'inki,
saboda a fara shirye-shiryen tafiya America,
" naji kince passport d'ina ni kad'ai to ke fa.....!?

"Hannunta Khulud ta rik'o cikin nata, tana murmushi tace " kwantar da hankalinki my Sanah,
kema kin san ko nan da k'ofar parlor baki fita batare da ni ba,
ni ai kin san Hanash ne zai nemar min visa,
shiyasa Papu yace akai naki dan next week yake san mu tafi,
" to kuma shi Hanash d'in bazaice zai bi mu ba...!?

RASHIN SANI......!!! Where stories live. Discover now