64

5.9K 368 171
                                    

_*RASHIN SANI.......*_


*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

6⃣4⃣

Tana gaf da isa gareshi ya mik'e yana murmushi had'i da goge jinin dake zubo mishi,
ya kalli Sir Moli yace " kayi hak'uri da zagin iyayen mu da nayi،
ba nayi hakan bane dan cin fuska da muzantaka ba,
nayi ne dan nemawa kai na mafita,
kana ya juya ga Sanah gami da sakar mata shu'umin murmushi,
yace " na fad'a miki kina so na kince k'arya ne, idan har baki so na meyasa dan duka na kikayi magana......!?

"Meyasa kika kasa daurewa ganina cikin mawuyacin hali.....!?

"Meyasa kika tausaya min.....!?

" Meyasa hawayenki zubowa.....!?

Ya fad'a idonshi cikin nata, Sanah dake tsaye sororo tana kallan Hanash,
tayi saurin sanya hannu a fuskarta ta shafa dan ita bama tasan tana kukan ba,
" hummm kina tsammanin k'arya ne.....!?

Takawa yayi kusa fa ita gaf da gaf har suna jiyo numfashin juna,
yace " ki yarda ko karki yarda kina sona, dan haka ki saki jiki da ranki,
ki bud'e zuciyarki mu more rayuwa da duniyarmu,
na baje miki......! ya kanne mata ido d'aya ya shige cikin mota yana murmushi,
Jaddah da Mimmee suka bi bayanshi,
Zohal da Wajnah ma haka,
babu wanda yayi magana cikin mutanen dake tsaye kowa  ya tafi،ya bar wajen
Sir Moli yana k'ok'arin shiga mota tayi saurin rik'o bayan rigarshi,
cikin nutsuwa ya juyo ya kalle ta kana ya kalli inda ta rik'e shin,
cikin jin kunya tayi saurin sakin shi،
" kayi hak'uri please....!
"me kikayi min kike bani hak'uri......!?

" Ni dai dan Allah kayi hak'uri, wallahi bada sani na nayi hakan ba,
ido ya d'an k'ura mata kana ya d'auke kanshi daga kanta,
yace " no karki damu nasan mata kuna da raunin zuciya ai,
yayi maganar yana murmushi, zatayi magana yayi saurin shegewa cikin motarshi yabar harabar gidan,
ta dad'e tsaye anan kafin ta taka zuwa inda Khulud keta faman bori tana hauka,
batare datayi mata magana ba ta sanya hannu ta d'ago ta،
ta danna gaban motar Hanash gami da rufewa,
Jaddah tace " irin haihuwa ai nan gurin zamanki ne ba nata ba,
" a'a kuje ni da su Zohal zamu taho a wancan motar,
ta fad'a tana rik'o Wajnah,
a tak'aice Hanash yace " shiga mu tafi..! bata kalle shi ba, taja hannun su Wajnah tayi gaba,
" kuje ku shiga wancan motar ina zuwa,
ta fad'a tana nufar Aarib dake tsaye,
tace " please bani key d'in motarka, batare da yayi magana ba ya mik'a mata,
ta amsa, ganin ta zauna kujerar driver yasa Hanash k'ok'arin fita daga motar,
da sauri tayiwa motar key ta fice,
batare da yayi magana ba ya koma ya shiga motar yaja,
tana yin parking ta fito cikin sanyin jiki ta shiga part d'in Mimmee,
direct bedroom d'in Zohal ta shige ta rufe k'ofa ta fad'a saman bed gami sanya rikitaccen kuka,,
bata fito ba sai gab da magrib ta iske Mimmee zaune a parlor,
cikin sanyin jiki ta zauna saman sofa (kujera),
" nasan masu aiki su gyara miki part d'inshi,
idan sun gama zaki shiga ki duba duk abinda babu sai kuje ku siyo,
in kuma canjawa za'ayi sai a canja,
Mimmee ta fad'a cikin fara'a,
jikin Sanah a sanyaye tace " Mimmee please ki barni na zauna nan part d'inki،
" kin tab'a ganin anyi haka.....!?

Hanash dake shigowa ya fad'a,
bata kalle shi tace " please Mimmee ban san komawa can tsoro nake ji,
" kina tare dani ai karki ji tsoron komai,
zatayi magana Khulud ta shigo hannunta aka tana rusa kuka muryarta harta dishe saboda tsabar kuka،
" yanzu saboda Allah Khulud bazaki daina kukan nan ba.....!?

Mimmee ta fad'a cikin tausaya mata,
batayi magana ba ta zauna a k'asa dirshen tana cigaba da rusgar kukanta,
Mimmee na k'ok'arin yin magana masu aiki shigo,
cikin ladabi suka zube a gaban Mimmee,
" Hajiya mun gama gyarawa,
a mitunce Mimmee tace " yauwa nagode sosai,
" ki tashi kije ki duba abinda babu sai kuje ku siyo,
fuska ta kwab'e zatayi kuka tace " please Mimmee ki barni nan ban son komawa can,
" ba ruwa na ki tambayi mijinki idan ya barki shikenan,
batare data kalle shi ba ta mik'e tace " bari naje zan zauna can d'in haka,
dan data tambayi Hanash alfama a matsayin mijinta ta gwammace ko cikin wuta ne ta shiga ta zauna,
tana k'ok'arin mik'ewa Jaddah ta shigo, fuskarta d'auke da fara'a tace " a'a irin haihuwa ina zuwa.....!?

RASHIN SANI......!!! Where stories live. Discover now