39

6.2K 338 93
                                    

_*RASHIN SANI.......*_


*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

3⃣9⃣

After 1 year
Bayan shekara d'aya

Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na wucewa,
kwanaki na gudu, while Sanah an shiga  first semester level 3,
yayinda soyayyar su da Sir Moli sai abinda ya k'aru,
sosai suke matuk'ar so da matsanancin k'aunar junansu,
duk ahalin Hard'o family's sun san da zaman Aryan Moli,
kowa ya sanshi sosai dan baya da burki cikin gidan,
cikin ikon Allah,
Ubangiji ya yayewa Aarib matsananciyar soyayyar Sanah,
sakamakon addu'ar daya dage yana yi ba dare ba rana,
dayake Allah maji rok'on bayinsa ne ya amsa rok'onshi,
yanzu babu komai tsakanin shi da ita sai zumunci da 'yan uwantaka.

A b'angaren su Khulud kuwa abun ba'a magana dan sosai Jaddah da sako ta gaba kan rashin haihuwa,
ta musgunawa rauuwarta sosai,
kullum cikin kuka da k'unci take,
duk ta rame ta kod'e saboda damuwa,
damma tana samun sauk'i wajen Hanash,
dan tunda suke dashi bai tab'a nuna mata damuwarshi ba,
amma tasan shima yana cikin damuwa kan rashin haihuwarta,
dan lokuta da dama tasha shigowa d'aki ta iske shi yana kuka,
ko ta jiyo shasshekar kukan shi cikin bathroom,
amma duk da halin dayake ciki yake danne nashi bak'in ciki,
ya rarrashe ta, dan ta samu sukuni,
dan yasha yin fad'a da Jaddan kanta,
while kowa na gidan su yasan matsalar datake ciki,
amma babu yadda suka iya sai dai su tayata da addu'a.

Khulud na zaune cikin parlor taji an banko k'ofar da k'arfi an shigo
a hankali ta d'aga kanta ta kalli bakin k'ofar,
ganin Jaddah yasa gabanta muguwar bugawa,
da  saurin ta mik'e jikinta na kerrrma da tsuma,
har k'asa ta duk'a cikin rawar murya tace " sannu da zuwa....!,
wani irin wulak'antaccen kallo ta watsa mata batare data amsa ba,
k'asa ta k'arayi da kanta cikin girmamawa tace " ina yini?

" Ke ni tashi kije ki kira man d'aya munafukin mad'aurin gindin naki,
kin dame ni da wata banzar gaisuwarki,
kanta k'asa cikin rawar murya tace " baya nan,
" a fusace tace " wad'ancan motocin da suke waje fa?

" Eh.! da d'aya ya fita,
kallan banza ta k'ara watsa mata tace " ina yaje?

" Ban sani ba ya dai fita ne kawai bai fad'a man inda zai je ba,
" da naso na same ku gaba d'aya dan ingano ta inda matsalar take kece ko shine,
amma tunda bai nan shikenan ke bari na fara ta kanki,
cikin d'aga murya tace " to nagaji da ga fara sa har yanzu banga k'aho ba,
nagaji da zamanki cikin gidan nan haka,
batare dana ga jikoki na ba,
so nake idan na shigo in fara jiyo hayaniyar yara tun daga waje,
ina jiyo hayaya-hayaya ana guje-guje da bari-bari,
ba wai kullum nazo gida na rink'a ganin fuska d'aya tak ba,
babu abin da kika iya sai dai ki ci kwanta,
idan kinji kashi kije kiyi ko?

Ta fad'a idanta kanta,
a hankali Khulud ta sanya hannu ta goge hawayenta,
" au kuku kike yi?

"Dan munafurci dukanki nayi ko zakinki nayi?

Shiru tayi bata ko d'aga kanta ba,
rankwashi Jaddah tayi mata akanta had'i da cewa " bak'ar munafuka,
wallahi ko kiyi ciki ki haihu ko kuma inyi mishi aure,
imma shanye shi kukayi kuka hanashi k'ara auren,
tunda dama naga alamar ba'ayiwa irinku kishiya,
to ni bazan d'auka ba dan bazan tsaya ina ji ina gani a mayar man da jikana juya ba,
eheee gwara ma kisan halin da kike ciki,
imma bak'in cikin kike man dan kar naga yaran shi to wallahi baki isa ba,
haba ace aure shekara biyu yanzu amma kwata-kwata babu wani motsi,
ko sau d'aya baki tab'a yin b'ari ba,
balle mu shaida kina haihuwa,
kin zauna kullum daga kici ki kwanta shikenan,
to wallahi baki isa ba, imma shi da kanshi bai iya nemo wata,
ni ina iya nemo mishi ehee, fa fad'a tana gyara mayafinta,
" shima zai iske ni ne har gida imma bai je ba zan dawo,
tana k'arasa maganar ta fita  fuuuuuu,
bayanta tabi da kallo tana kuka mai cin rai,
saboda ba'a shafe sati d'aya sai Jadda tazo har gida taci mata mutunci san ranta,
bata tuna cewa Allah ke bada haihuwar da kanshi,
bata tunanin bata isa ta bawa kanta ba,
sai wanda ke bayarwa yaga damar bayarwa,
takai 1hr tana ruzgar kuka,
kwata-kwata bata ji tsayawar motar shi,
ko motsin shi ba sai ganinshi tayi kanta,
da sauri ta fara k'ok'arin goge hawayenta dan kar ya gani,
cikin sanyin jiki ya k'arasa inda take zaune,
ya zauna kusa da ita,
cike da tsantsar tausayawa ya kalle ta yace " yauma Jadda tazo ko?

RASHIN SANI......!!! Where stories live. Discover now