63

6.9K 419 313
                                    

_*RASHIN SANI.......*_


*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

6⃣3⃣

Tsaye Sir Moli yayi yana kallan yadda Sanah ta rud'e lokaci d'aya ta birkice,
gaba d'aya parlor'n kasa mik'ewa kowa yayi,
dan babu mai wani gwarin jiki،
har Mimmee da Jaddah kasa motsawa sukayi,
cikin tsantsar tashin hankali Khulud ta rarrafa ta isa gareshi,
ta shiga jijjiga shi tana ihuuuun kuka,
" Hanash...! dan Allah ka tashi,
ta fad'a cike da tsantsar tsoro,
ganin bai motsi yasa Abbu da Dide  mik'ewa cikin mutuwar jiki suka nufeshe,
ganin suna shirin sungumarshi,
yasa su Ziyad saurin mik'ewa suka d'auke shi,
jikin Sanah na kerrrrma ta mik'e tana rik'e da hannunshi gam cikin nata,
  cikin mota aka sanya shi itama tayi saurin shiga akayi hospital dashi،
Doctors sun kai 3hrs a kanshi suna k'ok'arin ceto rayuwarshi،
dakyar suka samu numfashinshi ya dawo amma bai farfad'o ba,
suna ganin Doctors sun fito daga cikin emergency room sukayi saurin mik'ewa،
jikin Sanah na tsuma tace " ya jikin nashi Doctor....!?

"Alhamdulillah munyi nasarar ceton numfashi sai dai bai farfad'o ba،
amma in sha Allah ba zai jima ba zai farfad'o،
cikin muryar kuka Khulud tace " meke damunshi......!?

"Shock ya samu sosai har yakai ga zuciyarshi ta tsaya da aiki،
" yana ina....!?

"Yanzu za'a fito dashi a kaishi d'akin da za'a kwantar dashi,
Doctor yana gama rufe bakinshi aka fito da Hanash kwance kan gadon tura mara lafiya,
hancinshi sanye da oxygen, da sauri Khulud ta mik'e ta nufe shi,
ta dafa gadon tana kuka, cikin sanyin jiki gaba d'aya suka bi bayansu zuwa d'akin da aka kwantar dashi,
dudduba shi Doctor ya k'arayi sosai, gami da juna mishi drip kana ya fita,
kowa ka kalla zaga ganshi cikin jimami da sanyin jiki,
jikin kowa yayi mugun yin la'asar,
Khulud na zaune gefenshi a kan gadon, su Abbu na zaune saman sofa,
yayinda Sanah ke tsaye ta jingina da bango,
a hankali su Jaddah suka turo k'ofar d'akin suka shiga bakinsu d'auke da sallama,
cikin nutsuwa Zohal ta ajiye food basket a gefe,
basu jima da shigowa ba, su Mamu da Juju suka shigo،
suma d'auke da abinci,
ganin mutane cike da wajen yasa Mimmee jin kunya,
dan haka ta mik'e gami da kallan Sanah,
tace " zo mu tafi gida kije kiyi sallah kici abinci ko......!?

D'an shiru Sanah tayi batare data motsa ba,
Mimmee tace " ko bazaki tafi ba.....!?

Kallan da Mamu tayi mata ne yasata mik'ewa ba shiri tabi bayan Mimmee,
basu dad'e da fita ba Hanash ya farka,
a hankali ya soma magana, " Sanah.....!,
jikin Khulud na kerrrrma ta mik'e ta nufe shi bako kunyar families dake tsaye,
" Sanah.....! ya kuma fad'a cikin sanyin murya, cak....! Khulud ta k'ame a inda take tsaye,
take wani irin tuk'uk'in bak'in ciki da tsagwaran kishi ya tukare mata mak'ogwaro,
"Sanah.....! ya fad'a cikin muryar marasa lafiya,
" please ku bani Sanah, yayi maganar yana jujjuya kanshi،
idonshi rufe dan har lokacin bai bud'e idonshi ba,
Sanah.......! ya fad'a da k'arfi,
fuskar Halan d'auke da murmushi tace " good inzaka gina ramin mugunta ginashi gajere,
tayi maganar yadda babu mai jinta,
cikin k'araji Hanash yace " SANAH.......!,
ya fad'a gami da mik'ewa zaune,
"please ku bani Sanah.....!
ya fad'a a haukace,
da sauri Khulud taje gabanshi ta sunkuyar da fuskarta saiti tashi,
" Hanash nice Khulud, " ina Sanah....!?

Shine abinda ya fito daga bakinshi,
zatayi magana ya daka mata gigitacciyar tsawa " nace ina Sanah ko....!?

Ganin babu wanda ya kula shi yasa shi soma k'ok'arin cire k'arin ruwan dake jikinshi,
gami da k'arajin kiran Sanah.....!
a haukace Khulud tafashe da mahaukacin kuka saboda tsabar kishi,
ta rik'e hannunshi gammmm cikin nata,
" Hanash nice fa Khulud baka gane ni ba.....!?

Cikin zafin rai yayi jifa da ita gefe,
had'i da mik'ewa tsaye, yana huci yace " ban san ki ba Sanah kawai na sani,
ganin haka yasa Jaddah isa gare shi ta rik'e hannunshi ta zaunar dashi a hankali,
"kayi hak'uri ka zauna ka kwantar da hankalin ka,
kaci abinci kaji Hanash......!?

RASHIN SANI......!!! Where stories live. Discover now