*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻♂🙅🏻♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association*
*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*
Wattpad 68billygaladanchi.
32
Sake hannunta yae yabar d'akin gaba d'aya zuwa wajen asibitin, keb'an taccen wuri ya samu ya zaro wayarsa ya kira Ummin sa, bayan sun gaggaisa da yaransa da kowa har mahaifinsa ya buk'aci magana da Ummin tasa, cikin kuka ya furta"Ummie wai kinji Meenal se an mata dashe k'oda akan wannan gubar datasha amadadina, kuma samun k'odar yana wahala, shine na yanke shawarar kurun abata tawa k'odar d'aya idan ya kasance lafiyata k'alau" Jikinta ne yae sanyi matuk'a
"Lallai Mu'az wannan yarinyar ta cancanci sakayya fiye dama bayar da k'oda, tanada halayye ngartattu masu inganci, tanada karcin data cancani amata komai arayuwa, tana kumada kirki ga tausayi, bazan tab'a hanaka abun Alkhairi ba nikam wa iyalanka, sedai nai maka fatan Alkhairi, Allah ya bada sa'ar abinda kasnya agaba na Alkhairi Allah ya dad'a kareka daga sharrin masu sharri da duk wani abin k'i, kaje ka ceci rayuwar matar ka da iya k'arfin dakakeda shi, karkayi wasa da lafiyar wannan yarinyar kuma lallai ka aika mahaifiyarta taje duk k'asar daza'ayi aikin, Nan muma muna saka ran a sallamemu nanda kwana biyu danfa yaro jikin Abbanka se Hamdala dama baida wata cuta seta yunwa da wahalar zama gu d'aya ido kuma ko bayan an dad'e ba'a ganin haske ga shekarun tsufa kuma amma bakaga yanda yayi b'ulb'ul ba, bazakace acikin satuka biyu yayi wannan k'ibar ba, ammai general check up bashida ciwon komai se wannan allurar daya zama addict to sabida yanda suke ta danna masa ita, shima ana controlling sosai dan yanzu ya soma sabawa da komai, kuma memory d'inshi ma dasuke b8rkitarwa yana ta zama Normal" Nisawa yae
"To Ummi Alhamdulillah haka nake sonji, Allah ya k'ara masa lafiya, Meenal ta sanar mun cewar Sarauniya hassy tanacen tana shirin zuwa gun bokanta akan akashe mata Abba aduk inda yake, seku tsare adu'a da kuma ajiye k'urani agefen kanshi akodawane lokaci kuma kar ayi wasa da ruwan addu'ar nan inshaa Allah babu abinda zezo ya sameshi" Murmushi tayi taci gaba da bashi hak'uri har seda hankalin sa ya kwanta.
Akalar kiran sa ya juya zuwaga daddyn Meenal bayan dasuka yanke shawarar yanda za'ai da Ummi. Bayan sun gaisa yake msa bayani akan shinkafar b'eran da Meenai taci ga abinda ya haifar, amma dai shize bada tashi k'odar, mahaifin Meenal yashiga tashin hankali sosai lokaci d'aya ya rok'i Takawa akan su koma India akwai wani abokinshi k'wararren likita ne acen akan wannan b'angaren hankalinsa yafi kwanciya, dama kuma sunada shirin zuwa family trip to india nanda 2days haka yace da mahaifin nata ba komai shima ze shirya tafiyar tasu yau.
************
*India*Acen suka taradda su mummyn Meenal, mommy tare da k'anwarta suka zo sabida ita a rikice take tunda aka gaya mata, kallo d'aya tayiwa Meenal ta sanya kuka me tsuma zuciya, hankalinta a matuk'ar tashe yake, ganin yanda yarinyar nan kumbutinta yanzu harya kaiga fuska dako ina ma na jikinta, halitta ta canja kam duk ta gama birkicewa! Mu'az shima dai a zaune kurun yake amma hankalinsa baya jikinsa daddy dukya fisu k'arfin hali.
Mu'az be damu da mutanen dake nan ba su daddy, ya kasa ya tsare awurin matar sa hannun sa acikin nata yana mata wasa sabida kawarda damuwa a ranta, se murmushi take zuba masa dukda tana cikin azabar ciwo, ganin wannan ya sanya duk suka watse daga d'akin suka basu wuri
" 'yan matan Mu'az zakiyi kyau abinki da k'iba inama ace wannan k'ibar ta lafiya dana mora" Murmushi tayi ba kasafai yanzu kam take magana ba, hakan ma seta d'an matsa hannunsa dake cikin nata
"Ranar dakika samu lafiya kullum so hamsin zanna baki abinci ki samu kiyi k'iba mu huta" murmushin dai takeyi matsowa da kujerarsa yae kusa da kanta ya soma shafa sumar kanta bayan ya janye hular dake kanta
YOU ARE READING
TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...
Random"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunanin ka, na Amince zan rayu dakai rayuwa ta amana daso dakuma k'auna" ka tallafi rayuwata kadena fad'ar hakan kaji" Cikin azabar ta ciwon dayak...