*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻♂🙅🏻♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association*
*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*
Wattpad @ 68billygaladanchi.
42.
A reception suka nemi kujerun da aka zagaye gun dasu suka zauna, k'afa d'aya takawa ya d'aura akan d'aya hannunsa d'aya yana cikin aljihun sa, d'ayan kuma yana danna wayarsa fuskar nan tashi babu annuri ko kad'an, kallo d'aya zaka mai K'warjinin sa ya cika maka idanuwan ka, Gashin girarnan dayake da yawa ya had'e gaba d'aya sabida yanda ya yamutsa fuskar sa, alawar dake bakinsa ya shiga yamutsawa yana tsotsar ta tamkar am masa tilas, yayinda Abokin tafiya ya k'ura masa na mujiya yana nazarin sa, ya tabbatar wa kansa Maganganu ne dashi yakeso ya furta amma yau mulkin akeji ya kasa furta koda kalma d'aya ne cikin mintuna arba'in dasuka kwashe zaune awurin jugum jugum sekace masu zaman karb'ar gaisuwa, idan kaga motsinsa alawar dake bakinsa ya shanye a sannan ze zaro hannunsa dake aljihu ya b'are wata ya wurga baki, Abokin Tafiya ya rasa ta ina ze fara mashi, yadaiga shine ya kirashi yace yazo har jigawa, yanzu kuma ya amsa masa kiransa amma ya masa buris, taunar alawar bakin sa yae da k'arfi take ta tarwatse ya fesar da b'urb'ushinta a wurin cikin rashin damuwa, tun bayan musabiha da sukayi be sake koda kallon saba se yanzu, So barkatae yana motsa labb'ansa kamar zeyi magana sekuma ya basar se cen ya furta kamar an masa tilas
"Menene sunan wannan" ya dire masa wayar akan table dake gabansu yana me lumshe ido cikin muryarsa dabatayi kamada saraki sam se mata" Wayar abokin tafiya ya d'auka sannan ya kalli hoton daya nuna masa sosai, be gane komai ba tunda a hoton mutane uku ne
"Yallab'ai mutane uku ne a hoton wanne daga ciki kake magana?" Kawar da kanshi yae gefe kamar ma badashi yake magana ba, seda yagama shan k'amshin sa sannan yace
"Me b'akin kaya" K'ara k'urawa hoton ido Abokin tafiya yae cikin nazarin hoton sosai
"Bana tunanin acikin duka uku na tab'a ganin fuskar d'aya daga ciki, bansan ko waye ba" Hannu ya mik'a masa ya gano wayar sa yake buk'ata dan haka cikin girmamawa ya d'aurata a tafin hannun sa, bece komai ba fiyeda mintuna biyar sedabya gama jida ikonsa sannan ya mik'e, bekuma ce masa k'alaba hanyar barin hotel d'in ya d'auka, da sauri Abokin tafiya yaxo yaci gabansa yana sassarfa ya isa mota, bud'e masa gidan baya yae ya zauna a owners corner, sannan ya zagaya ya shiga gaban motar ya zauna ya bata wuta suka d'auki hanyar zagayen danshi be isa ya tambaya ina zasuje ba, shi kuma baze sanar masa inda zasu ba seyaga dama, zaga garin ya hauyi dashi na kusan awa d'aya da rabi babu mewa wani magana
"Ina zan samu wurin siyar da mota agarin nan? Naga anata zagaye banga wurin ba?" Murmushin Takaici Abokin Tafiya yae, waishi Takawa halinsa baze sauya ba kenan har abada, koda yake yauma ai yayi abin kai gida tunda ba'a gama suguda agari yace ajuya gidaba
"Ranka ya dad'e Aikuwa mun wuce har biyu ba jimawa" Be kulashiba yakuma san bawai kulashin zeba, da wannan ya kame bakinsa ya gimtse bece kanzil ba har suka isa wurin, yafi mintuna 30 a kotar yana karatun News paper yana murmushi ance an nemesa shida matar sa an rasa, seda ya gama iya nasa jinkai sannan yace
"406 manual" iyakar abinda yace kenan banda haka be k'ara komai na, Abokin tafiya kamar ya sharara masa mari haka yaji amma danin hali ya sanya yafita kurun yaje ya samo wata sabuwa gal ya gama ciniki yazo ya gaya masa komai
"Yallab'ai da zuwa kayi ka gani wa idanka yafi ai" D'agowa yae ya kalleshi cikin lumshe ido
"Idan kazo da kud'in ka biya kaji" Be musaba yadan shine mafi alheri agareshi ya juya yaje ya biya kud'ad'en da dama yazo dasu suna booth kasan spare tire sannan yadawo ya zauna a motar
YOU ARE READING
TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...
Random"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunanin ka, na Amince zan rayu dakai rayuwa ta amana daso dakuma k'auna" ka tallafi rayuwata kadena fad'ar hakan kaji" Cikin azabar ta ciwon dayak...