*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻♂🙅🏻♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association*
*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (slimxy)*
01
.......*******.......
Tunda suke maganar gawar kurun ta tasa a gaba ta dask'are a wurin bata ko motsin kirki, yanda kasan wata statue haka ta tsaya k'ik'am, kowa da abinda yake fad'a amma banda ita kowa yana masa adu'a banda Ameena, zaune kurun take kaman wata icce, kuka take amma bana hawaye ba, kukan zuci takeyi gashi k'iri k'iri ta kasa gaskata mutuwar nan, ga gawa agabanta tunka a nad'e gawar ta ganta amma tana gani tamkar ba gawar bace ba, muhammad d'inta ze tashi dogon sumace yayi yaya zasuce ya mutu? Su k'ara masa lokaci mana ze farfad'o...ta ayyana a ranta!!! Mazane suka shigo suka durk'usa suka d'auki gawar ta muhammad dake cikin farin k'yalle, kana an ninninkeshi acikin tabarma a zura a makara!! Mik'ewa tai ta rike makarar"Me kenan zakuyi? Ina zakuje da muhammad, ku barni ko a haka zanta kallon abuna, kurun ku bud'emun fuskar sa, dan Allah karku tafi dashi, ku k'ara masa lokaci dogon suma ce yai" Tausayinta kowa keji, sun kula bata cikin hayyacinta mahaifi muhammad da mahaifin ta sune sukazo suna k'ok'arin b'anb'are Ameena daga jikin makarar data kama ta rirrik'e hannu bibbbiyu da k'yar da sid'in goshi ta sake shima seda k'wace da k'arfin tuwo! Se sambatu takeyi
"Karkumun haka, Akwai maganar da Muhammad ze gayamun daren jiya, ban saurareshi bane ku barshi ya gayamun, koda iya itace, ku taimakamun muhammad ya sanar dani abinda yakeso ya sanarmun, idan baku barshi ya fad'amun ba nima mutuwan zanyi, idan munje cen seya gayamun" babu wanda ya saurareta de d'aki aka wuce da ita aka kwantar da ita masu rarrashi sunayi masu ban baki sunayi amma se sambatu take ga alama Ameena batasan ma metakeyi ba ta zauce mutuwar muhammad ta mata dukan a kawo wuk'a kenan!!!! Ganin abun bame k'arewa baneba ya sanya su daddym Muhammad suka kira likita yazo ya sharara mata allurar bacci.
***************
Mustapha kabeer sharad'a da kuma Muhammad D'ayyib kagara Aminan junane, tun tasowarsu secondry school d'aya suka halarta kuma ajinsu d'aya, had'in kansu yakaisu ga zamtowa aminan juna har sukaje jami'a suka karancin building enginearing a tare, lokaci d'aya suka kammala bautan k'asane kurun ya rabasu kowa yaje nasa garin, bayan sun kammala a tare suka soma harkokinsu tunkan su samu aiki, Alhaj mustapha shine ya soma samun aiki a wanj kampani me zaman kansa na gine gine, yayinda Muhammad ya samu aikin sa daga baya a k'ark'ashin gwamnati, seya kasance mustapha yafi muhammad k'arfi haryake taimakonsa daidai gwargwadon iyawarsa, dama cen shi mustapha d'an wanine sunada arziqinsu, yayinda shi kuma muhammad iyayensa ba masu kudi mahaifinsa ma'aikacine kurun a k'ark'ashin gwamnati me rufin asiri......
Haka har sukayi aure suka hayayyafa, yayinda Muhammad ya zamto yaro a k'ark'ashi mustapha kasan cewar shi mustaphan yakai ga company nasa na kansa, dukda haka seyawa muhammad manager na company d'in inda shima lokaci d'aga ya bunk'asa kasancewar ana matuk'ar jida sharad'a builder's kasancewar su k'wararru masu iya zane da gini na zamani....basu tsaya anan ba seda suka kaiga kawo kayan gini daga waje wanda akasari acen kurun ake samunsuu kayan qawata gida da sauransu, da wannan suka yada a zango a Abuja harkansu ta tsarin gine gine ya bunk'asa akeji da Sharad'a builder's sosai da sosai....
************
Muhammad sunusi shine babba awurin Alhaj muhammad, yayinda yakeda k'annensa susu 4....Yusuf shine me binsa se kuma Bunyameen daganan se yara mata Salma da zuhra, matarsa d'aya wannan ya sanya suke uwa d'aya ubansu d'aya...Alhaj Almustapha kuwa ya jima da aure be haihu ba, dan kuwa har muhammad sunusi yakai shekaru 12 aduniya be haihu ba, seda yakai kusan 13 sannan aka haifi Ameena yarinyace da akeji da ita wanda seda ta share shekaru goma sha hud'u tukunna mahaifiyarsu ta haifi wani Namijin dayaci sunan kakan sa Kabeer anace dashi Kb junior.
*Mom Nu'aiym*
YOU ARE READING
TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...
Diversos"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunanin ka, na Amince zan rayu dakai rayuwa ta amana daso dakuma k'auna" ka tallafi rayuwata kadena fad'ar hakan kaji" Cikin azabar ta ciwon dayak...