page 41

3.2K 302 39
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

    Wattpad @ 68billygaladanchi.

                  41
###############
      Fu'ad kuwa tunda ya azabtar dasu da abinci me yaji me koma ta kansu ba, cewa yae kar wanda ya basu abinci se yunwa ta kashesu a binne, haka suka kwana suka wuni babu ci babu sha yara sun galabaita sunyi kuka har rayukansu sun b'aci murya ta dusashe, hankulansu sun gushe Ummie kad'aice me dama dama acikin su, mutumin dake kula dasu ne ya shigo d'akin ya lalubesu yana jijjigawa

"Wai acikin su babu wanda ya mutu, nina gaji da gad'in gawarwaki wlhy, so nake yunwar ta kasheku d'aya bayan d'aya na bunne ku in kama gabana akwai aikin dake gabana kuma naira dubu d'ari uku za'a bani, bazan zauna ina gadin kuba idan yamma tayi baku mutu ba shak'e ku zanyi in binne in kama gaba na" cikin dauriya dan kuwa tanada muguwar ulcer tace dashi

"Bawan Allah katab'a yin aiki an baka miliyan uku?, gida, motar hawa dakuma fili guda biyu manya manya duk a garin abuja?" Waigowa yae ya kalleta

"Ban tab'ayi ba yoko rai na kashe ai duk rai d'aya dubu hamsin ne kurun, nida zan samu miliyan uku ma wlhy ko babu wancen tarkacen sana'ar ma barinyi zanyi" Murmushi tayi na k'arfin bali

"Ka fitar damu daga nan, ka tseratar da rayuwar mu har driver nan, namaka alqawarin baka dukkanin abubuwan dana lissafa maka yanzu, miliyan ukun dakaj8 na ambata da wayana yana hannuna dana maka transfer ta rabinsu dan kawai ka yarda zancika alk'awari na,idan kuwa ka kaini abuja gun mijina na maka alk'awarin, mota, gidan zama agarin nan dakuma filaye biyu manya manya d'aya anan d'aya a abuja, kuma bazan tab'a fallasaka ba sedai zan rok'eka akan kadena ta addanci" Wata mahaukaciyar dariya ya kwashe da ita kan yace

"Hajiya kenan, me kike tak'ama dashi daze tabbatar mun kinada wannan dukiyar da har zaki bani ita?" Murmushi tayi
.
"Nice uwar sarkin garin nan, me mulkin masarautar hankaka, ka fahimceni idan duk wannan be makaba, sark'ar wuyana miliyan biyar ce zan baka ita har awarwarayena na miliyan biyu da rabi, da zobena na dubu sari bakwai, sarkar kafata miliyan d'aya, wannan abun na hancina kawai miliyan daya da dubu d'ari biyu ce, a kunnen jikatan nan sark'arta miliyan biyu ce, awarwarom hannunta daya da rabi, agogon hannuna ma zallar zinariya ce dazatakai miliyan uku, suda ka gani a zahiri xan iya cire maka su duka dan kawai ka tseratar da rayuwata, abuja zaka kaini gun mijina kai tafiyar ka bana buk'atar komai se hakan" Nisawa yae

"Hajiya duk zaki iya bada wannan akan rayuwar jikokin ki data direbanki, in hakane zan karb'i wasu nabar wasu" Girgiza kanta tae

"Idan dai har wannan dikiyar zata hanaka aikata ayyukan b'arna irin wannan tokoba rayukanmu ina me tabbacin zan iya mallaka maka su kyauta, bana buk'atar ka rage komai daga ciki, idan akwai abinda zan roqa kabarmi dashi shine zoben hannuna mijinane ya bani kuma yafi shekaru 40 a hannu na" Haka yaeta murna tare da alk'awarin ze dena har abada, ya tattara dukiyar sa, acikin daren ya d'auki hanyar abuja dasu shida yaranshi susu biyu, se godiya yake mata tare da alk'arin ya dena kenan har abada shida yaranshi, yana tsananin godiyax har motar haris suka d'akko dan haka kai tsaye gidansu Meenal ta nuna musu acen aka ajiye su.

°°°°°°°°°°°°°°°°°
   Takawa yana baccin sa na gajiya yaji motsawar meenal tayi yawa, farkawa yae ya k'ura mata ido, se murk'ususu takeyi tana yarfe hannayenta, adu'a yashiga tofa mata inda nan take ta farka a firgice tana ambatar sunan Hidar abakinta, rik'eta yae se gumi take had'awa, hannayen sa duka biyu ya sanya ya rik'o fuskar ta

"Meenalyn mu'az menene na firgici haka ehn? Mafarki kikayi akan yaranki?" Da sauri ta gyad'a masa kanta, jinjina ka yae

"To basekin fad'a ba kiyi adu'a kinji" nanma jinjina masa kanta kurin tayi

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now