page 40

2.9K 292 23
                                    

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad 68billygaladanchi.

*Assalamu Alaikum wa rahmatullah, Masoya k'ungiyar haske da masu bibiyar litattafan mu muna godiya, muna so mu ankarar daku kamar yanda muka ga wani littafin na yawo me suna (Magajiyar karuwai) da sunana ni Billy galadanchi rad'au ajiki, ku sani Bani na rubutaba, wasu marasa abinyine suka nemawa kansu abinyi ta hanyar hasada da neman suna suna bak'in cikin suga an zauna lafiya, tomu dayike Allah yasa munada hankali bazamu biye musu ba amma wajibine garemu mu shaidawa masu hankali 'yan uwanmu cewar koda sunga wannan tabarar taci gaba da yawo, to kuwa babu sanya hannun haske ko billy galadamchi aciki, aikine na wanda bas tsoron Allah kuma mu bazamu biye musu ba, muna godiya ba adadi*
    

40

Da sauri ta tura wayar ta janyo hanky kanya iso kusa da ita ta wurga masa a fuska, ragwaf ya fad'o rabin jikinsa duk a jikinta, hannu Takawa ya sanya ya ture shi ya fad'o daga kan gadon kanshi ya mik'e, key dayaga ya shigo dashi shiya zare daga hannunsa ya tashi da sauri ya tura k'ofar ya rufe da key, lalube ya shigayi ajikin mutumin seda ya zaro key na mota da pistol k'arama, had'awa yae da bindigrshi ya tura a k'ugun sa kanya mik'e gaba d'aya

"Wannan abun zuwa yaushe ze saki jikinsa ne?" Kallon sa tae yanzu kam ta fara karaya da abubuwan nan batada k'arfin zuciyar jurar su, hawayen datake k'ok'arin tarewa ya silalo mata cikin takaici tace

"Baze wuce sa sa'o i goma sha biyu ba, kuma kafin nan kaga 'yan uwansa dole su neme sa ni bansan ya zamuyi ba yanzu wlhy" waigawa Takawa ya somayi yana kallon d'akin windows biyu ne aciki kuma duk sunada buglary, matar sa ta fara karaya dole yae aiki irin na cikakken soja yanzu kam, dolene ya nuna cikar zaman sa namiji,Zaro bundigar yae ya harbi wannan mutumin a k'afa duka biyu, sannan ya saurara yaji, ba wanda yako motsa tabbas shishi kad'aine da k'arar bundigar ya ankarar da sauran zuwa inda suke, shikuma azabar bullet ya farkar dashi cikin rud'u sedai babu k'argi har yanzu abun na jikinsa besan me yake bama! Bud'e k'ofar d'akin yae a hankali ya fita waje sadaf, sadaf ya lek'a babu kowa a wajen,wani d'aki ya hango a bud'e a hankali yaje ya leqa,fitilar d'akin a kunne,gardawa ne birjik sunkai susu biyar bacci suke amma baccin beyi kamada na lafiya ba, wataqil wani abun suka sha, koma yae yake sanar da meenal, wani k'aramin roba ta zaro ta mik'a masa

"Ka toshe hancinka ka fesa wannan a d'akin duk bazasu farkaba se bayan awowi sha biyu" Karb'a kurun yae ya juya yanda tace haka yae sannan yazo ganin bega takalmintaba agun ya sanya ya duk'a yace tahau bayansa batai musuba sabida yunwar dake cinta, haka suka fice daga gidan sadaf sadaf, motar daya d'auki key d'inta abaljihun d'ayan gu d'in ita ya d'auka suka keta dajin dabama ganin ina suke tura kan motar tunda darene,cikin k'aguda meenal ta kallesa tace dashi

"Takawa nayi mamakin wannan jejin damuketa luk'awa aciki, Nusy ta sanar dani tayi tracking motar da aka kwashemu duka, kuma suna cikin abuja" murmushin takaici yae

"Kidneppers wa 'yancen thugs d'in fa meenaly, sun canja motar ne, wacce aka kawomu nan da ita daban da wacce aka d'akko mu daga cen, dole ta kasa gane komai yanzu" nisawa tae

"Bari nayita adu'a da karatun k'ur'ani loudly cox yanzu basu kad'ai bane abun tsoro har wannan jejin ma abun tsoro ne, dan wlhy ni a tsorace nake Takawa"  Bece koma8 ba yaci gaba da tuk'insa, sunyi tafiyar awa yafi 5 dan har gari ya soma wayewa amma abin takaici basu kaiga hanyar dazata nuna musu alamun akwai titi bama, jacking motar ta farayi Takawa ya kalli meenal

"Babyna u stay srong kinji, inshaa Allah tunda muka baro dare duhun dare be cutar damu ba yanzu ma lafiya lau zamu fita, man dake cikin motar nan ya k'are kuma da alama sakin hanya mukayi, shisa muketa nausar jeji, daga nan zuwa inda ta tsaya dole mu ajiyeta mu taka da k'afa" Ita yanzu damuwar tama yunwar cikin ta, k'wallan idanta ya gangaro mata tace

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now