[7/17, 4:50 PM] RAHEENAT MUSTAPHA: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*NIDA YAYA AL'AMEEN*
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*STORY AND WRITING*
BY
*RAHEENAT M ABBAKAR*
_(Heenat)_Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga duk wani makarancin littafin nan na baku shi kyauta Raheenat nayi muku fatan alkhairi a duk inda kuke.
Whattpad
@rahinamustaphaMARUBUCIYAR
*1 KOMAI YAYI FARKO....*
*2 HALIN RAYUWA*
*3 RAYUWAR SAUDA*
*4 RAYUWAR HANEEFA*
*5 MAHAK'URCI....*
*6 RUK'AYYATU*
*7 RAINA FANSA NE GARETA*
Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN*SADAUKARWA GA
*MAMAN LABYB (MAMIEN MU)*
*FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI*
*SHAFA'ATU BALA BABA*
*ADAMA TANIMU A BIYE*
*AISHA NICHOI**🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A W)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛'''Page 7
Tace "yayah kana sona da aure kace.?"
"Eh Meenat, ko ke bakya sona.?"
Hawayene suka fara sauko mata murya na rawa tace "yayah wallahi ni ban taɓa kallonka a matsayin mijin aure ba, kallon yayana nakeyi maka, ina sonka yaya amma soyayya na jini ɗaya, yayah kamar yanda nake faɗa maka ne wallahi kafi ƙarfina, yayah ban masan ta wacce fuska zan kalleka a matsayin miji ba, yayah ina amshi soyayyarka yanzu me kake tunanin zan faɗawa Kamal, so kake ya kirani da mayaudariyya ? Yaya kana da babban matsayi a zuciyata, ina yi maka son da ko ƴan uwana da muka fito ciki ɗaya ba nayi musu irinsa, Yayana dan Allah ina roƙonka kabar maganar soyayya tsakaninmu mu ci gaba a yanda muke."👏
Idanun Al'ameen ne suka kawo ruwa, amma sai yayi ta maza ya mayar dasu, kallon Meenat yayi wacce take hawaye zuciyarsa nayi masa zafi da kalamanta, shi a tunaninsa a yanda suke da Meenat duk lokacin da yazo mata da buƙatarsa ba zata juya masa baya ba, ashe yayi kuskure, ashe da gaske takeyi ba zata iya aurensa ba ? To wai duk soyayyar da take nuna masa tare da kulawa na menene ? yana cikin tunanin nan yaji Meenat ta riƙo hannunsa tare da duƙawa gabansa tana cewa "yayana dan Allah ka fahimci ƙanwarka, dan Allah kar kayi fushi dani, wallahi ba zan iya juran fushinka gareni ba, ina ji a jikina zaka samu matar da tafini komai, wacce zata kula min da kai sosai. "
Ta ƙarasa maganar tana ɗaura kanta saman cinyarsa tana ci gaba da shashsheƙa.Hannu Al'ameen yakai ya ɗago da ita cikin nuna jarumta ya sakar mata murmushi yace "is ok my meenat stop craying, alƙawarin zuciyata ce bazan taɓa tursasaki ki soni ba, sannan ba zan taɓa aurenki ba tare da yardanki ba, Meenat duk da son da nakeyi miki wallahi zan haƙura tunda ke bakya ra'ayin aurena, ina da tabbacin in najewa su Abba da maganar ina son aurenki zasu aura min ke, amma ba zanyi hakan ba tunda zuciyarki bata buƙatar hakan, Meenat zan iya sadaukar da farin cikina dan ke kiyi farin ciki, farin cikinki kawai ya isheni farin ciki, Meenat ki saka a ranki daga yau yayanki ba zai ƙara yi miki maganar soyayya ba, na haƙura, na sadaukar da soyayyata domin farin cikinki, na san kina son Kamal ina fatan ya sakaki farin ciki ƙanwata, hakan kawai in yayi ya isheni. "
Ya ƙarasa maganar ƙwalla na ciko idanunsa, faɗawa jikinsa Meenat tayi tana kuka faɗi take "kayi haƙuri yayah, kayi haƙuri, bansan me yasa na kasa amsar buƙatarka ba yaya. "Murmushi ƙarfin hali yayi yace "kibar kuka dan Allah, kukanki na taɓa min zuciya. "
Da ƙyar ya lallasheta ta bar kukan suka miƙe sukayi cikin gida.