Part

5.2K 70 3
                                    

[7/22, 8:29 PM] Maman Momy😘: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *NI DA YAYA AL'AMEEN*

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

         *STORY AND WRITING*

                    BY

       *RAHEENAT M ABBAKAR*
                  _(Heenat)_

Whattpad
@rahinamustapha

MARUBUCIYAR

*1 KOMAI YAYI FARKO....*
*2 HALIN RAYUWA*
*3 RAYUWAR SAUDA*
*4 RAYUWAR HANEEFA*
*5 MAHAK'URCI....*
*6 RUK'AYYATU*
*7 RAINA FANSA NE GARETA*
Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN*

        SADAUKARWA GA

*MAMAN LABYB (MAMIEN MU)*
*FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI*
*SHAFA'ATU BALA BABA*
*ADAMA TANIMU A BIYE*
*AISHA NICHOI*

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A W)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛'''

Page 11


Da ƙyar Suhailat ta samu ta rarrashi Meenat tabar kukan, sai ajiyar zuciya kawai take saukewa, a hankali ta miƙe ta shige toilet.

Ta daɗe tana wanka kafin ta fito ta saka wata doguwar riga, ko mai bata shafa ba ta nufi ƙofa, Suhailat da take zaune ne tace "ina zaki je Meenat.?"

Waigowa tayi ta kalleta da idanunta da sukayi luwu-luwu saboda kukan da tayi, cikin sanyin murya tace "zanje na ga yah Al'ameen ne, nasan yau lahadi be fita asibiti ba. "

Ajiyar zuciya Suhailat ta sauke cike da tausayin ƙawar nata tace "to ni bari na wuce gida, sai gobe zan dawo mu tattauna akan abinda ya kamata muyi."

Tare suka fito ɗakin Suhailat tayiwa Ummi sallama sannan suka fito, gidansu Al'ameen Meenat ta shiga ita kuma Suhailat ta kama hanya domin tafiya gida.

*******

Da sallama ta tura ƙofar falon nashi ta shiga, zaune yake yana aiki a computer ɗinsa, ɗagowa yayi yana kallonta har ta ƙaraso kusa dashi ta zauna, ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke tare da mayar da hankalinsa kan computernsa ya ci gaba da abinda yakeyi ba tare da yace mata komai ba, wasu ƙwalla ne suka ciko idanunta tayi saurin mayar dasu tace "sannu da aiki yayah. "

Be ɗago ba yace "yauwa."

Ƙara matsawa tayi kusa dashi tace "yayah ya yafe min laifina dan Allah. "

Still be ɗago ba yace "laifin me.?"

Shiru tayi ta kasa magana kuma, ɗan ɗago da kansa yayi ya kalleta sai kuma ya mayar ya ci gaba da abinda yakeyi, hawaye Meenat ta fara cikin muryar kuka tace "yayah baka sona yanzu ko, kana ji a ranka ka tsaneni ko, ba ka son na zo kusa da kai ko.?"

Yanayin yanda tayi tambayar yaso bawa Al'ameen dariya duk da yanda yake jin zuciyarsa kuwa, rufe computern yayi ya ajiye ya juyo yana kallonta sosai, hannu yasa yana share mata hawayen cike da kulawa yace "ko ɗaya Meenat, sam yayanki be tsaneki ba, kuma be daina sonki ba, Meenat in dai zan iya daina sonki to tabbas zan iya daina son kaina, sai dai bazan ɓoye miki ba Meenat ina jin haushinki sosai saboda kece kika jawo mana komai, da a lokacin da na zo miki da soyayyata kin amsa da yanzu na tabbatar mun zama mata da miji, amma babu komai Meenat, na yarda da ƙaddara, nasan komai na Allah ne, Allah ne ya ƙaddaro haka, dama can ya rubuta hakan sai ya faru, Meenat ina son farin cikinki fiye da yanda nake sonki, na barwa Kamal ke ne dan ina tsammanin zakiyi farin ciki da aurenshi, sai kuma Allah ya juya al'amarinsa, yanzu Meenat kin zama allurar cikin ruwa me rabo ka ɗauka, duk da ta wani ɓangaren ba zance haka ba, saboda Abba yace ya zaɓa miki miji, kenan wanda aka zaɓa mikin shine be rabon, Meenat ina sonki ba kuma zan taɓa daina sonki ba sai ranar da numfashina ya bar gangar jikina, soyayyarki a cikin jinina yake, inayi miki fatan samun farin ciki tare da soyayya ga duk mijin da zai aureki. "
Ya kai ƙarshen maganar hawaye na zubo masa.

NI DA YAYA AL'AMEENWhere stories live. Discover now