Short story page 1

291 10 1
                                    

WAYE SILA.        ©®2019
  AN HEART BREAK STORY
SHORT AND IT'S MIND BLOWING
STORY WRITER
ABDUL ALHAJI MUSA (10K).
PHONE NUNBER 09077974042.
KARKASHIN
MIRINGA YOUNG WRITERS ASSO.


STARTED
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJI MAI ALBARKA,WANDA YABANI DAMAR TSARO WANNAN LITTAFIN MAI SUNA WAYE SILA LABARIN TA SHAFI ZURFIN CIKI DA KUMA KIN DAUKAR SHAWARAN IYAYYE.

PAGE 1

Zaune take bisa wata makeken kujeran,dake tsakiyar wasu ciyayi masu launin daukar hankali.
Dogayen bishiyoyine ke kewaye da ita hade kuma da jajayen fure masu kiyawun karshe.
Jingine take da kujeran ta gefe guda,limshi idanu tayi sai wata zazzafar kwalla ta zubo Mata.
Dago Kai tayi ta kalli sararin samaniya sai ta sake tsinkewa da kuka yayin da take tuno wani Abu daya faru da ita.
Bata furta komai ba amma duk Mai dogon tunani zaisan yarinyar tana matsakaicin damuwa.
Domin inka duba gefenta coffee ne dake aje kan center table kuma hartayi dan karan sanyi,sannan kuma waya na Kara gefenta amma taki dauka.
Abinda zai baka mamaki shine yarinyar takasance yar shekara ashirin da biyu,sannan tana da kiyawun sura,farace fes sannan tana da farare idanuwa.
Kukar da take sai ya Kara Mata kyau sosai.
Yarinyar daga bisani ta Fara furta cewar "wannan da so za'a kirata KO kuma tozarcine,waye silar haka tsakanin mu".
KOMEYE YA FARU DA WANNAN BAIWAR ALLAH OHO

cigaba tayi da kukan nan Nata har dare tayi bata motsa inda take ba.
Inda akayi busar iska mai kura har aka soma ruwan sama,tananan zaune har karfe ukun dare.
Gari tayi shiru sai kukan karnuka ne ke tashi

TWO MONTH BACK
WATANI BIYU DASUKA WUCCE.

Sunana laila Adam,haifaffiyar garin kano,nayi wasan kasata a garin,Kama daga primary school har zuwa junior school nayi a garin.
Amma daga misani sai mahaifi na yasami tirasfa zuwa abuja,tundaga wannan Lokaci ban sake zuwa garin kano ba,sai yau Dana dau niyar sake halartar ganin.
Tsaye take cikin tashar jigin kasa,sanye take da wata shudiyar riga da kuma pink siket,takuma yafa wata jaririyar mayafi sharashara.
Jirgin na tsayawa ta shige ciki,ta taka har wajan zaman ta.inda ta tarar da wani kabjejen kato baki kirin a waje,komawa tayi da baya sai ta hango wata tsohuwa inda take zaune ita kadaice.
Da sauri taje wajanta ta zauna.
Dalilin zuwan ta wannan Karon shine ta samu aiki online a google wacce zata sami albasin miliyan daya kowace wata.
Nan take zaune sai ga wani santalelen saurayi,Mai kyaun sura.
Tikaro ta yayi yazo ya tsaya gaban ta.
Lailah baka fuskance shi da kallo ba.
Shiko yace"malama wajan zamana nane."
Laila bata ma tanka mishi ba,ya sake cewa"hey you, are sleeping"
Laila juyawa wanin bangare tace"baba bawan Allah,taya zaka ce na zauna wajan zaman ka,duk girman jigin nan sai ni ka gani"
Yace"keeeee cikin kakkauran murya,shige bayi nayi baki ga Jakarta gefen ki ba?"
Laila dafa goshi tayi tace"kaico "
Cigaba da rikicin wajen zaman sukayi har laila ta saduda
Tace"toh ban minti daya Zan tashi"
Tsaye yake kanta tasa hanu cikin jakar da ke rataye a kafadan ta,ta zaro wata bakar tabaro Mai duhu,tasa idon ta, ta soma dafedafe.
Da sauri wannan saurayi ya Kama hannun ta yace"I'm sorry I'm sorry please,bansan baki gani ba yar uwa,kiyi hakuri Dan Allah."
Laila tace"no problem Dan uwa,barni kawai na taka"
Yace"a'a Zan zauna wajen naki"
Zama tayi ta soma dariyar ta cikin zuciya tace"na ninke ka baibai"
Ido biyu tayi da wata tsohuwa Wanda ta kura mata ido,gaheriyar murmushi tayi sannan ta hada hannayen ta biyu,alamar kirifamin asiri please.
Laila bayan ta juya tace"kowayasa wancen kato kusa da inda zan zauna oho,yabi ya cikani da kalli"
Ta furta hakanne cikin siririyar murya.
Hmmmmmm duk nisan tafiyar da sukayi laila hankalin ta nakan wancen tsohuwar.
Bayan jigin ta tsaya sai laila taki tashiwa inda take.
Kosam sai taga tsohuwar nan ta saka gabjejen bakar tabaro ta Fara dafedafe.
Zara idanu laila tayi tace"kutt,yanzu duk bata lokacin danayi wajen ajiye hankali na kan matannan Ashe makauni yace"
Laila jiyo muryan wancen sauyarin tayi a bayan ta,yana cewa"ki tashi jirgin ta tsaya."
Bata rai tayi ta cire tabaro tasawa mutunin a hanu ta ruga da gudu.😁
Saurayin nan ya lekata ta wajen window,ya kura mata kallo yana ganin yanda take gudun har kanta ya bace.

WAYE SILA?Where stories live. Discover now