Final page12

82 4 0
                                    

WAYE SILA. ©®2019
AN HEART BREAK STORY
SHORT AND IT'S MIND BLOWING
STORY WRITER
ABDUL ALHAJI MUSA (10K).
PHONE NUNBER 09077974042.
KARKASHIN
MIRINGA YOUNG WRITERS ASSO.

Page 12 .
Final episode.
15/July/2019.

💔
wani kalar uban Kara Lisa tayi,laila ko tace"Ummah!!!!!!!!".
Da sauri mutanen dake cikin gida suka fito waje, dansu ga meye yasa laila tayi wannan ihun.
Gani sukayi umman laila na kwance cikin jini,sai suka Kama salati.
Duk mutanen dake wajen taro nan sai da suka fita dan  suga meke faruwa,amma mahaifiyar sultan ko ita ta haye kan dakin sama tana kallon komai da suke akasa.

Lisa dago kan ummanta tayi ta aza cinyar ta,sai ta soma ihun wani ya taimaka min.
Laila tsaye take ta kasa mosawa amma dajin karan muryan Lisa sai tayi alamar razana kafin hankalin ta yazo jikin ta, karasa wajen Mahaifiyar tasu tayi,bayan taje daf da Inda take sai ta ajiye guyiwoyin ta kasa, dago tafin hannun ta tayi da niyar ta taaba jikin umman tasu.
Lisa da sauri ta janye jikin Mahaifiyar tasu tace"laila komai daya faru duk kece sila,Dan haka karki karaso Inda muke."
Cike da mamaki laila ta bude baki tana kallon ta.

Auntyn laila da sauri ta karasa,ta taya lisa suka ciccibi umman suka sata cikin mota suka wuce.
Laila zaune take tsaliyar titin tayi shiru,saiga wani Mai adaidaita,da sauri ta tsayar dashi.
Mutumin yace"Ina zamu?"
Tace"inason kabi bayan waccen bakar motan".
Suna wucewa sai abban sultan tare dashi sultan din suka bi bayan su.

Wannan adaidaitan tsayawa tayi a tsakiyar wani asibiti,laila ta sauka ta nufi cikin asibitin da gudu.
Isowar ta keda wuya sai Lisa ta mike tsaye tace"Mai ya kawo ki laila,ko kinzone kijin ta mutune koko?".
Auntyn laila tace"Lisa you mistaken".
A fusace ta juya tace"I know exactly what you will say Aunt,..because you love laila so much".
Ajiyar zuciya tayi sannan ta cigaba da cewa"umma tana cikin wannan halin duk ta dalilin laila,bansan halin da zan shigaba in wani abu ya faru da umma"
Rife Mata baki laila tayi da sauri sannan tace"Lisa karki sake ambatar haka,babu abinda zai sami umma".

Sultan da mahaifin sa labe suke bayan gini suna kallon abinda ke faruwa.
Lisa wankawa laila Mari tayi tace"bana so na sake ganin fuskar ki,tafiiiii!!!!!! Karna  sake ganin ki".

Ruwan hawaye ne suka zobo fuskar laila,sai ta soma jada baya.
Nan sai ga Wata likita ta fito a cikin dakin da aka kwantar da Mahaifiyar su.
Da sauri lisa da aunt suka karasa wajenta,Lisa tace"ya jikin Mahaifiyar mu?".
Shiru likitan tayi na wasu lokuta.
Zuciyar laila sai faman bugawa take da sauri haka zalika zuciyoyin sultan da kuma abban sa.
Wannan likitan ta cire tabaran dake idanta tace"I'm sorry.......Allah ya karbi ajiyar sa".
Lisa yanki jiki tayi ta fadi ta suma.
Laila kuma dajin haka sai ta soma Jada bayan cikin sauri.
Zuciyar tako sai faman radadi take,sultan zubar da hawaye ya soma sai yace da Abban cewa"duk nine silar wannan Abba......nine sila, laila bata da laifin komai".
Abban yace"yanzu yaya zamuyi?".

Laila fita tayi daga asibitin jikin ta a mace,tana wani tafiya tangaltangal kan titi.

5:00pm
Sai ga wata farar motor ta karaso asibitin takuma tsaya a tsakiyar asibitin ,mahaifin laila ne ya sauka daga cikin wannan motan.
Da sauri ya nufi cikin asibitin ya tarar da Lisa da kuma kanwar matar sa,cikin yanayi na ban tausayi ya gansu zaune.
Cikin muryar kuka yace"Ina gawar matata yake?."
Zubar da hawaye suke kurun sunki cewa komi.

Sultan da mahaifinsa komawa sukayi gida,Inda suka tarar da duk yan family Na zaune a falo ciki harda rihana,ganin su yasa rihana ta tashi a fusace tace"Abba!!!!"
Kamal Anna da kuma kakar tasu suka juya.
Da sauri kakar tasu tace"yah jikin tan yake?".
Shiru sukayi suna kallon ta
Karasowa wajan sultan tayi tace"meya faru sultan?".
Sultan kallon ta yake sai hawaye suka soma zubo masa.
Anakan haka sai ga Mahaifiyar sultan ta sauko,da ganin ta sai sultan da mahaifin sa sukayi yunkuri tafiya.
Sai tace"Sultan!!!!".
Ta kuma daga tafin hanun ta alamar karya tafi.
Tsayawa yayi amma kuma bai waiga baya ya kalle taba.
Tace"Ina son muyi wata muhimmiyar magana".
Baban sultan a fusace ya juya yace"oh really,do you still want to talk about the wedding ceremony,ko kuma kina yiwa dan ki da kuma sirikarki planne na zuwa honeymoon.......enough bamu son jin wani abu daga bakin ki".
Da sauri tayi yunkurin cewa wani Abu amma shikuma mahaifin sultan ya hana ta cewa komai.
Sultan juyawa yayi ya kalli Mahaifiyar tasa yace"da muke cen asibitin sai nake tunanin nine silar faruwar haka,amma kuma dana shigo gidannan yanzu sai zuciya ta take rayamin that I'm wrong.....sabida kece silar ruguje rayuwar laila."
Cike da mamaki umman ta kalli sultan.
Yace"eh nasan baki gane meye nake nufi ba,toh bari na fito miki a mutum,...laila ta rasa Mahaifiyar ta, tadalilin ki".
Salati kakan su tayi,jirine ya kamata da sauri Anna da kamal suka rike ta.
Sultan cigaba yayi da cewa"ba iya nan ba kawai domin yanzu a hakan laila ce suke lakadawa laifin da kece Kika aika ta umma".
Juyawa yayi ya kiyale Mahaifiyar tasa a tsaye.
Dukkan su suka shige ciki suka kiyale ta a tsaye tsakiyar falo.
Kwallace ta cika idanun ta,zama tayi da baya ta zauna kan kujera.

WAYE SILA?Where stories live. Discover now