page 2

81 6 1
                                    

WAYE SILA. ©®2019
AN HEART BREAK STORY
SHORT AND IT'S MIND BLOWING
STORY WRITER
ABDUL ALHAJI MUSA (10K).
PHONE NUNBER 09077974042.
KARKASHIN
MIRINGA YOUNG WRITERS ASSO.

Page 02

Laila iso gida tayi karfe uku,gidan da laila ta sauka ciki katotone sannan kuma kota'ina ka duba jikin ginin zaka ga anyi Mata adone da fararan duwasu.
Gigan babu kowa illa aunty ta,wato kanwar mahaifiyar ta.
Karkuji mamakin jin cewa laila na kiran ta da aunty,domin ita ta kasance shekarar ta hamsin amma bata taba aure ba.
Ta tsani taji ankira ta da umma shiya sa laila ke kiranta da aunty.
Kimanin kwana uku,lokacin da sanyin safiya laila na kwance makwancin ta sai taji karan waya da sauri ta tashi ta duba,sweet mom tagani a rubuce.
Dauka tayi tace"Assalamu alaikum"
Umman tata ta ansa tace"yah kike laila"
Laila tace" lafiya"
Tace"yasu Auntyn ki.....da sauran friends naki"
Tace"suna Lafiya,sai dai haryanzu ban soma zuwa gun aikin ba.....Ina kuma tunanin yau za'a jarrabani"
Umman tace"toh Allah bada sa'a"
"Amin" tace cikin siririyar murya.
nan mahaifiyar tata ta soma bata shawara akan maganar auranta taji shiru inji ta.
Laila bata ce da ita komai ba sai sauraron ta kawai take tayi Shiru.
Umma ta karashe batun ta da cewa"kinsan yanayin zama cikin zuri'ar tamu,bakayi bama ace kayi ballen tana ace kinki aure don aiki."
Laila tace"Hmm umma na zata kece zaki fahim ceni amma KO kadan bakiyi ba,aure yin Allah ne indan lokacisa bai yiba toh babu Wanda zai. sashi yayu"
Shikenan laila ta sauke wayar tana kuma jin muryar mahaifiyar tata amma ta kashe.
Laila ta kasance tana son shan coffee sannan kuma tafison rayuwan online wato chatting domin kullum tana online, shine ma dalilin makarar ta kullum.
Laila na kwancen nan ta dago Kai ta leko agogo,7:30 ta gani tace"kai inada interview 8:00shape"
Da sauri ta sauko daga gadon ta shige bayi tayi wanka,tasa Jan leshi Wanda yayi mata kyau sosai.
duk cikin sauri tayi komai,dau jakar ta ta rataya a kafadar da,kiran wayar kwarta tayi tace"Ina kike bestie,da fatan kin rigani isowa"
Tace"a'a wallahi aiyuka ne suka min yawa,sai dai inkin gama ije na dauke ki"
Laila ranta a bace tace"alright yanzu yazan yi da kayakin dana dauka,kina so na rasasu ne"
Tace"a'a laila kiyi hakuri karranki ya baci"
Laila tace"hmmmm good"
Ta sauke waya,bude kofa tayi ta fito tsakiyar falo,inda ta tarar da auntyn ta tana kaimata coffee.
Karba tayi tasha ta ajiye. kofin tace"natafi"
Auntyn tace"laila wait a minutes"
Juyawa tayi ta shige ciki ta dauko wata laima pink color ta mikawa laila.
Tace"da wannan laimar na sami true love dina" ajiyar zuciya tayi ta sake da cewa"dukda baya tare dani I have strong filling that he still love me my child,so I want you to get your true love with this"
Murmushi laila tayi tace"Aunt I'm running late,bye "
Da sauri ta fice daga falo ta kiyale Aunt a tsaye ta ciko idanun ta da kwalla.

Makarancin yayi ajiyar zuciya so biyu sai ya cigaba.

Garin tayi baki kiren, haduri ne ko Ina iska kuma na kadawa ta kowace bangare.
Laila tsaida motar ta tayi ta sauko.
Saukar ta sai aka soma yayyafi kamar fesawa ake ship ship ship sannan aka soma busar iskan da karfin gaske.
Wabtu laima iska yayi daga hannun laila yayi tafiya dashi mai tsaho kafin ya jefar gaban wani saurayi,saurayin ya kasance bayan sane ke fuskan tar laila ta yanda ta kasa ganin fuskar sa.

Vote pls

WAYE SILA?Where stories live. Discover now