*BAN ZACI HAKA BA*
_(Tawa ƙaddarar)_*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION* _(HWA)_
Bismillahir rahmanir rahim.
*04*
Wani katafaren get suka nufa, da sauri maigadi ya wangale masu get, bai shiga cikin gidan ba, sai da ya tsaya suka gaisa da maigadin cikin mutunci, har yana yi masa kyauta, a fitowar nan da suka yi da Hisham, Nasreen ta cika ɗan karanci wasu daga cikin halayyar sa, don yadda taga yana mu'amala da mutane, a da can bata taɓa kawowa ranta yana da kirki haka ba, a kullum kallon mara tausayi take yi masa, kallon wanda ba ya mutunta kowa, ashe ba haka bane yana da halin kirki.
Gida ne babba mai dauke da plat kusan biyar, a wajen da aka tanadar don a je motoci ya yi parking din motar, ba su jira shi ba suka nufi daya daga cikin plat din, Jawad da Mufrad suka diba da gudu cikin plat din. Da kallo Hisham ya bisu yana ci gaba da amsa waya, don tun yana tuki ake kiran wayar nasa, tun da ya duba yaga sunan, Al'ameen abokinsa sai ya bari har ya isa gidan.Nasreen da Zuhra cikin nutsuwa suka shiga falon, sallama suka yi, wani farin tsoho da ba zai wuce shekaru saba'in ba ya amsa masu fuska sake yana ta doka masu murmushi, kai tsaye wajen da yake zaune suka nufa.
"Ɗan tsoho mai ran karfe." Nasreen ta fada tana zama kusa da shi.
"Matar tsoho, sai yau nake ganinki? An ya kuwa alkawari ya ce haka?" Alhaji Babba wato kakansu ya yi maganar cikin sigar tsokana.
"Lah me kuma kake nufi? Duk iya kulawar da nake baka shi ne sai ka yi min korafi?" Nasreen ta yi saurin masa tambaya.
"Kulawa? Ina wani maganar kulawa a nan? Mai dai kula dani tana yi." Alhaji Babba ya bata amsa. Daidai da shigowar Hajiya Babba hannunta rike da ƙwarya, wacce ke shake da fura da nono, "A'a'a su waye haka nake gani? Kamar yammatan kauye?" Hajiya Babba ta ida tambayar tana isa wajen da Alhaji Babba ke zaune ta mika masa kwaryar.
Murmushi Nasreen ta saki ta ce "Ke kullum Hajiya sai dai ki ce mana yammatan kauye, Alhalin kaf zaminku babu wanda ya kai mu wayewa." "Ke tafi can ku yanzu har wani abu kuka iya? Baku iya komai ba sai rashin kunya."
"Lah! Hajiya. Nasreen ta fada tana zare ido.
"Eh! Ai gaskiya ce." Hajiya ta bata amsa.
"Ni dai Hajiya ki bani fura, da yake Alhaji Babba naki ne, ai kin miƙa masa." A shagwabe ta yi maganar.
"A'a fura dai don mijina na sanya aka damata, don haka mutum shima idan ya ji haushi ya yi aure."
"Kai Hajiya ke kullum mutum idan ya zo sai kin nuna kin fi son, wannan tsohon akan shi, ni dai ki bani fura."
"Bafa zan bayar da furata ba ehe." Cike da tsokana Hajiya ke bata amsa, Alhaji Babba ma murmushi kawai yake yi, yana jin soyayyar jikar tashi na kara yawa a zuciyarsa.
Ita ma Zuhra dake gefe tana jin diramar Hajiya da Nasreen, sai ko ta kwashe da dariya. Ta ce "Allah kema sister kin cika kwadayi." "Eh na yi ɗin." Nasreen ta bata amsa tana miƙewa.
"Ina kuma za ki je?" Zuhra ta yi sauri tambaya.
"Mota zan koma har ku gama tun da Hajiya ta hana min fura, babu komai da Abbana yana nan ai zata bani." Ta fada tana share kwallah, dama can a sama take yanzu kuwa Hajiya ta kara taɓota.
"Zo nan kin ji matata ta karfen, indai fura ce ga ta nan zo ki sha, karki yi kuka akan ƙaramin abu." Alhaji Babba ya yi maganar ta sigar lallashi.
Makale kafada ta yi cikin shagwaba, ta juya zata fice, ji ta yi ta yi karo da wani abu wanda ya sa ta yi taga-taga zata fadi, runtse ido ta yi ta yi don ta sadakar ta fadi, bakinta dauke da sunan Allah.Ga mamakinta sai ta ji an tallafo ta, kamshin turaren sa da ya cika mata hanci ne ya fargar da ita, a jikin wanda take don haka sai ta fara, kokarin zare jikinta daga nashi, magana ya fara da sansanyar muryarsa kamar ba ta namiji ba "Ke baki da hankali ne? Kina tafiya ba ki duban gaban ki? Yanzu da kin faɗi kika ji ciwo fa?"
Ganin yadda ya rike ta tana son kwace kanta,ta kasa sai kawai ta fashe da kukan shagwaba.
"Don na yi maki magana shi ne zaki tsaya kina yi min kuka? Zaki rufewa mutane baki ko sai na tattakaki." Ya fada yana wurga mata harara, kasa-kasa yake maganar don ko su Hajiya Babba ba su ji abin da yake fada mata ba.
"Wai yaushe ka dawo ne? Megida?" Hajiya Babba ta tambaya ta kare masa kallo.
Murmushi ya yi wanda ya ƙara fito da kyaunsa ya ce "Ɗazun nan, gani na yi ba zan iya kwana ba sai na zo naga matata da abokina." Ya ida maganar yana gama shiga falon.
Zama ya yi kusa da kafar Alhaji Babba kamar yadda ya saba tun yana Yaro, cike da ladabi ya fara gaida su.
Amsawa suka yi, sannan ya gyara zama yana faɗin "Allah yasa an dama min fura don gaskiya na yi missing dinta sosai."
"Fura gata nan Alhaji yana sha, yanzu ma da kaga wancan yar rigimar, akan furar take yi."
Hararar Nasreen ya yi sannan ya ce "A miko min da sauri, don Al'ameen yana can yana jirana."
Bari na sa Ladiyo ta kawo maku, kamar na san kuna zuwa na sanya ta dama da yawa." Hajiya ta dire maganar tana kwalawa Ladiyo mai aikinta kira.
"Wai dama Hajiya furar da yawa kika dama amma shi ne ki ka ce ba zaki bani ba, shi da yake kin fi son Yaya ai gayi kin ce a kawo masa." Duk da kallon da Hisham ke aikawa Nasreen mai cike da gargadi bai sa ta fasa maganar ba, hasalima maganar ta dire tana turo baki.
Maganar tata, ta so ta sanya shi dariya, amma sai kawai ya fuske ya kara bata rai, don ya tsani raini, su kuwa yaran nan yanzu da sunga ka yi masu dariya sai su rainaka.
Babu jimawa Ladiyo ta kawo masu furar, shake da wata babbar jug, kicin Nasreen ta shiga ta dauko cup guda biyu masu dan girma, ta zubawa Zuhra sannan ta zuba nata, don hadama sai da ta cika cup din duk da tasan ba iya shanyewa zata yi ba, ɗaukar jug din ta yi ta miƙa masa.****** ******* ******* ****
"Kika ce Nasreen ta shigo gidan nan Uwani?" Hajiya umma dake zaune akan kujera, tana girgiza kafa ta yi saurin tambaya. "Allah Hajiya sun shigo tare Hisham, har da Zuhra." Ta bata amsa.
"Bangaran wa suka shiga?"
"Bangaran Hajiya Babba."
"Tun yaushe?" Ta kuma jefa mata tambaya.
Da alama Uwani ta soma gajiya da tambayar Hajiyar, don haka sai ta ce "Gaskiya Hajiya ban sani ba, nima wajen Idi direba na samu labari, kuma da alama da gaske ne, don har motarsa na gani." Cikin kosawa ta bata amsa.
"Jeki ki ci gaba da aikinki zan yi maganinsu, su din banza na gama da Saudatu ma bare ita karamar alhaki." A fili ta yi maganar tana mai ci gaba da girgiza ƙafafuwanta.
Lallai dole sai ta mike tsaye, hankalinta ya kuma tashi jin tare da Hisham suka shigo gidan, a duniya ta tsani ganin Hisham da Nasreen, domin kuwa su ne kaɗai wanda ta kasa cin galaba akansu, amma dole ne ta kara miƙewa tsaye don ta tarwatsa masu rayuwa. Don haka da sauri ta dauki wayarta dake kusa, ta danna kira.*SASAN HAJIYA BABBA*
"Yanzu kai abu daya ya rage maka, ka zama babban mutum, ka yi makaranta ka gama ka mallaki ofishin kanka, kana da muhalli sai abin da zai zama cikon mutunci, Aure yakamata ka yi Hisham tun kwanaki na fara yi wa iyayenka magana."
Alhaji Babba ya dire maganar yana tsare Hisham da ido. Dagowa ya yi tare da kallon Nasreen da Zuhra dake zaune, ya kara tamke fuska, uwa bai taɓa sanin ana yin dariya ba, tun kafin ya yi magana suka fahimci inda ya dosa, Ai da sauri Zuhra ta mike tare da barin falon, ita kam Nasreen turo baki ta yi, cikin zuciyarta tana mita 'Shi wannan Yayan ya cika takura, mutum yana zaune zai wani kore shi.' Ta na shiga korido ta ji ya fara magana...*Assalamu Alaikum, da fatar duk kuna lafiya? Ga dai labari nan mun fara, kuma in sha Allah sai mun sai mun kai karshe zamu tsaya, sai dai ba zamu samu zuwa gacci ba sai da haɗin kanku, ma'ana ina bukatar comments din ku, ku sani yin comments shi ke karawa marubuci karsashi, da fatar zaku bayar da hadin kai.*
*Yar Mutan Rano*
YOU ARE READING
BAN ZACI HAKA BA (Tawa kaɗɗarar)
Actionlabari ne na tausayi, sadaukarwa, jarumta, uwa uba kuma soyayya wato kauna, labarin Hisham da Nasreen, ku biyoni don jin yadda zata kaya.