page 05

484 22 0
                                    

*BAN ZACI HAKA BA*
           _(Tawa ƙaddarar)_

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION* _(HWA)_

Bismillahir rahmanir rahim.

*05*

"Alhaji indai maganar ne karka damu, nan bada jimawa ba zan kawo ma matar da zan aura." A ladafce ya yi maganar.
"Masha Allah! Na yi farin ciki da jin haka, saboda aure shi ne cikar mutuncin mutum, daga lokacin da ka samu iyali za ka ga yadda mutane za su rika mutuntaka, Allah ya yi albarka, sai ka yi kokarin faɗawa iyayenka, don su shiga a yi komai da wuri." Alhaji Babba ke wannan magana, duk da a cikin zuciyarsa akwai wani babban manufa akan Hisham din, sai dai har zuwa yanzu ya fi maida muhimmanci ga addu'a, idan alhairi ne Allah ya tabbatar ya kuma cika masa wannan buri.
"In sha Allah Alhaji mu dai a ci gaba da yi mamu addu'a."
"Addu'a kullum yin ta ake babu dare babu rana, Allah dai ya baka tagari, mai sonka da gaskiya." Amin duk suka amsa.
Nasreen dake makale tana jin maganganun da suke yi, taɓe baki ta yi a ranta tana faɗin "Tab zan ga wannan mata da har take son kawo kanta mahallaka, mutumin da baya dariya ba ya fara'a, kullum rai a haɗe shi ne wata ke son ta aure shi, tab aiko sai ta yi dana sani wata rana. A fili take maganar sai dai ba lallai ko mutum na kusa da ita ya ji me take fada ba. "Ke kike ganin zata kawo kanta mahallaka, Ya Hisham ai miji ne irin na nuna wa a ko ina, ga kyau ga aji uwa uba kuma ga nairori, duk wacce ta same shi matsayin miji ta more." Mtsww ta ja tsaki, wanda ba ta san a fili ta yi shi ba har sai da ta ji muryar  Zuhra na cewa. "Lafiya ke kuma?"
"Lafiya lau, me kika gani?" Nasreen ta yi mata tambayar, tana ƙara kallon Zuhra.
"Da tsaki fa kika shigo, kuma ina kika tsaya tun sa'adda muka baro falo?"
Dariya Nasreen ta tuntsire da shi ta ce "Wallahi tsayawa na yi a koriɗo ina jin maganar da su Alhaji ke yi da Yaya, sai da na ji komai, yanzu ni jira nake naga matar da zai aura, ni nasan ta shiga uku da muskilancin sa, Allah da a ce na santa tsaf zan shirya na je na bata labarin halinsa." Harara Zuhra ta jefa mata, ta ce "Za ki je ki bata labarin halinsa? Wane irin hali ke gareshi? Na san dai BOSS ko baya da hali mai kyau dole budurwa ta soshi, domin kuwa Allah ya yi masa kyau sannan kuma ga kare magana wato kudi, balle ma yana da halayya mai kyau, da zai iya nemar ko wacce irin budurwa kuma duk matsayinta."
"Haka ne, amma fa ba ina nufin yana da hali mara kyau ba ne, a'a shi matsalar kullum cikin haɗa rai yake, ko murmushi yana dadewa bai ba, bana jin ko ya yi aure zai canza hali."
"An ya kuwa dai Yar Dady? Ko dai kina ciki ne, na ga kullum maganar ki ba ta wuce ta BOSS, kin ga kuwa yadda kuka yi matukar kyau ɗazun, lokacin da za ki faɗi ya tallafo ki? Wollah da ina da waya sai na yi maku photo, don kun matukar dacewa da juna yadda kika san a Film din JAMAI RAJA, da su Dady za su yadda wallahi da an hada ku aure." Zuhra ta kara maganar tana sakin dariya.
Dogon tsaki ta saki ba tare da ta ce komai ba, ta yi hayewar ta kan gadon Hajiyar, don sosai take kaunar gadon karfen Hajiya, wanda ya sha shimfidu na alfarma, gefe guda kuma maganar Zuhra ya tsaya mata a rai. lumshe ido ta yi cike da son bacci ya kwashe ta. Ko kadan yanayin Nasreen bai ba Zuhra tausayi ba, domin ta dade da sanin burin Dady ne burin Aunty ce, kuma burin Hajiya da Alhaji Babba ne, don haka kullum tana yin addu'a ne akan Allah ya kawo ranar da Nasreen zata kasance matsayin matar BOSS din su.
****
Can a falon Hajiya Hisham gyara zama ya yi, sannan ya fara magana "Alhaji yanzu kafin mu iso nan gidan sai da muka fara zuwa wajen Ummie, na yi farin cikin yadda muka sameta, don yadda likitocin suka yi min bayani, na fahimci an samu ci gaba da yawa musamman da muka shiga har dakin lafiya lau muka fito, ba tare da ta yi mana wani abu ba."
"Masha Allah! Na yi farin ciki da jin wannan labari, don kwana uku da suka wuce da muka je, mu ma haka muka iske ta da sauki sosai." Alhaji Babba ke maganar cikin jin dadi.
"To Alhaji dama cewa na yi mai zai hana a dawo da ita gida? Duba da yadda aka samu canji, sai a ci gaba da yi mata maganin a gida."
"Allah ya yi ma albarka, ɗazun nan na gama tunanin haka, amma tun da kai ma ka yi tunanin haka, zamu zauna da iyayenka, duk shawarar da muka yake zaka ji labari, amma ya zama lallai a dawo da ita gida."
Farin ciki sosai Hisham ya yi, don haka sai ya fara yi wa Alhaji Babba godiya. Kallon agogon hannunsa ya yi inda ya nuna masa karfe bakwai saura, don haka sai ya ce "Alhaji bari mu je masallaci idan mun dawo zan mayar da wa'innan yaran gida." Kusan a tare suka mike da Alhaji Babba, suna tafe suna tattaunawa har suka isa Masallacin dake cikin gidan.
Ko da suka fito sallah bai koma ciki ba, Jawad ya aika ya kira mashi su Nasreen, Nasreen dake kwance har bacci ya soma daukarta, don tun da Zuhra ta yi mata wancan maganar, bata kara cewa ƙala ba.
"Aunty BOSS ya ce ku tashi mu tafi." Maganar Jawad kenan da ya haddasa mata buɗe idanuwanta da su ka rine su ka zama ja.
"Ka ce masa ni dai ya barni anan gobe zan dawo yanzu kaina ke min ciwo."
"Ciwon kai? Kai sister wai maganar da na yi maki ce ta sanya maki ciwon kai? To Allah ya sawwaka." Tana gama faɗin haka ta fice tana dariyar mugunta, don har ta ga yadda BOSS zai yi da Nasreen.
Lumshe ido ta yi tana mai son ci gaba da baccinta, sai dai me? Kamshin turaren sa ta ji ya cika daki, ai da sauri ta tashi zaune, shi din ne kuwa tsaye ya harde hannayensa a ƙirjinsa, ya kafeta da lumsassun idanunsa, fuska tamke babu wani alamar rahama. Wani irin faɗuwar gaba ya ziyarce ta, da sauri ta fara jawo dankwalin kanta da ya zame, cikin inda-inda ta fara magana "Am-emm dama yanzu nake shirin tashi."
Bai ce mata komai ba sai kada kai ya yi ya bar ɗakin, tsaki ta ja tana mitar, Shi wallahi wancan Yayan ya fiye takura, ko da ta fita falon bata ko tsaya yi wa Alhaji Babba sallama ba ta bar falon.

Cike da haushin Hisham da kuma baccin dake idonta, shi yasa har take wani lumshe ido, , abin da yasa  har bata iya ganin hanya sosai, sam bata kula komai ba, shi yasa bata kula da tahowarta ba, sai ji ta yi an kashe mata mari, buɗe murya ta yi  tana kwarara ihu, dama ga ta da shegen raki. Da sauri har da gudu Hisham ya karaso wajen, don ganin me yake faruwa, daidai da zuwansa ta fara magana "Ke da yake ba diyar mutunci ba ce, ba ki ga ji abin arziki ba kin kwaso halin Saudatu, shi ne har za ki iya shigowa gidan nan, har ki gama zamanki ba za ki zo ki gaida ni? Yanzu idan Saudatu ce za ki iya yi mata haka? Ai ko ba ki mutunta ni don komai ba kin mutunta ni don Mukhtar, saboda ko banza ni din matarsa ce, da yake an shiga an fita ai gayi an rabani da ke." Ta ƙarasa maganar tana wani kumfar baki.
"Kar ki kara ce wa Ummienah batta da halin arziki, kuma ki daina kira min sunan mahaifi tun da ya rasu, don kin ga ni marainiya ce shi ne zaki rika cin zalina wallahi Allah zai saka min..." Kafin Nasreen ta rufe baki, ta sake daga hannu zata kai mata wani marin, da sauri Hisham ya riƙe mata hannu yana faɗin "Karki ƙara marmarin dukanta, domin ba jaka kika samu ba, idan ko ba haka ba..." Hada yan yatsun shi ya yi waje daya suka bada sautin kara, wanda ko yaro aka yi wa haka ya san gargadi ake masa, daga haka yaja hannun Nasreen din suka juya za su bar wajen.
"Munafiki kai har ka kai matsayin da zan yi abu ka tanka min? Wallahi sai na yi maganinku shashashai."
"Lafiya kuwa Hajiya Umma?" Uwani mai aikinta ke mata wannan tambayar.
"Ina fa lafiya Uwani? Yanzu na samu wancan mara kunyar yarinya na mareta, shi ne shi kuma wancan miskilin yake neman gaya min magana, wallahi idan ban ɓatar da su an bar jin labarin su ba, ki ce ba ni ce Hansatu ba."
"Kin yi min daidai Hajiya, ai gara da kika ɗauki wannan matakin, gaskiya yakamata ki mike tsaye, yanzu fa da na baro sashin Hajiya Babba ina ji suna maganar, babban burinsu shi ne a hada Hisham da Nasreen aure." Cikin zallar gulma Uwani ke magana." Wani kallo mai kama da ban fahimta ba Hajiya Umma ta jefa mata, tana faɗin "Ban fahimta ba Uwani, wallahi matukar na bincika na samu karya kika min sai na yi maki abin da baki tunani.
"Allah Hajiya Umma da gaske ne, har ma ji na yi suna cewa za a dawo da Hajiya Ummie, suna maganar a samu wanda zai gyara mata bangaran ta." Wannan karon Hajiya Umma sai da ta zaman yan biri, don sosai maganar ta zo mata a bazata, magana ma kasawa ta yi, sai da ta karfafa zuciyarta kafin ta mike, jiki babu kwari ta nufi sashin ta, ƙwaƙwalwar ta ta toshe ta ma rasa wanne tunani zata yi...

****

*Asalin labari*

*Shin wane mataki kuke tunanin Hajiya Umma zata dauka?*

*Me kuke tunanin zai je ya dawo tsakanin Nasreen da BOSS din ta Hisham?*

Ku biyoni sannu a hankali zan warware maku.



*Yar Mutan Rano.*

BAN ZACI HAKA BA (Tawa kaɗɗarar)Where stories live. Discover now