*Hazaƙa writer Association*
*BAN ZACI HAKA BA*
_(Tawa kaɗɗarar)_*Dediceted Zeety (Mum Hanan)*
*Happy Sallah to all muslim Ummah*
A yi hakuri sai yau na samu yin typing, kuma a hakan ma ba wani page mai yawa ne ba, shi din ma na aje duk abin da zan yi ne na yi maku wannan kaɗan din. Amma zuwa gobe za ku samu mai yawa.😅
Bismillahir rahmanir rahim.
*11*
Ita Nasreen ba ta ma san wani Hisham yana wani abu ba, domin kuwa hankali kwance take hira da Usman, wanda ke yi mata magana ƙasa-ƙasa tana ta sakar masa kyakkyawar murmushi, daga wajen da Hisham yake ji yake kamar zuciyarsa za ta buga, wani irin zafin zuciya ya ke ji, bai taɓa jin abin da yake ji game da diya mace kamar yadda yake ji a wajen Nasreen.
Kiran da aka yi wa amarya da kawayenta ne ya ba shi damar tashi daga kujerar da su ke. Bai isa wajen da su ke zaune ba sai da ya daidaita nutsuwarsa, Hisham namijin duniya yana zuwa bai tsaya komai ba ya cafki hannun Nasreen, bai ce komai ba ya nufi hanyar waje da ita, da kallon mamaki Usman ke binsu, domin tashi ya yi domin ya amsowa Nasreen abin sha, yana dawowa ya iske wannan ɗanyen hukunci. Shi kam ko a jikinsa, inda Allah ya rufa masa asiri wajen da suke babu mutane da yawa, da yawa kuma hankulan su yana kan amarya da kawayenta, haka Hisham ke jan hannunta tana biye da shi kamar dai raƙumi da akala, bai zame ko ina da ita ba sai wajen motarsu, buɗe motar ya yi tare da jefata ciki yana cewa
"Wato ke da yake kin isa da kanki, shi ne za ki zauna tsakiyar maza kina hira da su, kina wangale masu baki ko? To wallahi wannan shi ne hukuncin ki, ba ki kara komawa cikin hall din can har a tashi." Yana gama faɗin haka ya juya, tana kallo ya koma cikin hall din.
Wani kuka ta fashe da shi na zallar takaici, "Me Yaya ke nufi dani ne wai?" Nasreen ta jefa wa kanta tambayar da babu amsa.
"Shi kenan kuma ni bani da yancin kaina? Wallahi ba zai taba yiwuwa ba, don ba karkashin sa nake ba." A fili take maganar.
Tun tana sanya rai zai dawo har dole ta cire rai, kuka kam ba ta fasa ba domin gani take Hisham ya gama cutar ta.
*****
Hankali kwance Hisham ya shiga cikin hall din, domin kuwa ya yi maganin abin da yake damar masa zuciya, bai ko kalli su Usman ba ya koma wajen zamansa.
Bangaran Usman kuwa ya na ganin Hisham ya shigo ba tare da Nasreen ba, sai ya ji wani irin nauyi ya tokare masa zuciya.
A hankali ya kai hannu tare da danna saitin zuciyarsa, ganin numfashinsa yana ƙoƙarin yi masa wahala sai ya mike, bai ko iya yi masu sallama ba.Yana fita motarsa ya shiga, kafin ya ƙarasa gida wani zazzafar zazzaɓi ya kama shi, da kyar ya iya kai kansa gida.
Can kuwa wajen dinner, an ci gaba da gudanar da hidima cikin kwanciyar hankali, ba a tashi ba sai karfe goma sha daya, ana tashi Hisham ya kira Al-ameen a waya, bai fi minti biyar ba ya iso.
"Please ka dauki Maryerm da kawayenta ka kai su gida, ni zan shiga gidan Dady."
"Menene haka kuma? Kana nufin ni zan yi direbin nasu?"
"Eh! Ni akwai uzuri da ya taso min yanzu nan."
"Uncle Al-ameen ba muga Sistor ba fa." Su ka ji maganar Zuhra a bayansu.
A dan rude Al-ameen ya juya ga Zuhra yana tambayarta.
Mtsww Hisham ya saki tsaki bai ko koma ta kansu ba ya fice daga hall din, da kallo Maryerm ta bishi, har lau dai tana cike da mamakin halinsa.
YOU ARE READING
BAN ZACI HAKA BA (Tawa kaɗɗarar)
Açãolabari ne na tausayi, sadaukarwa, jarumta, uwa uba kuma soyayya wato kauna, labarin Hisham da Nasreen, ku biyoni don jin yadda zata kaya.