page 09

478 25 1
                                    

*Hazaka writer's Association*

      *BAN ZACI HAKA BA*
                _(Tawa kaɗɗarar)_

*Gaba daya labarin nan sadaukarwa ne wa ZAINAB SULAIMAN (Zeety Mum Hanan), Allah ya bar kauna, ina fatar Allah ya kara daukaka ki fiye da haka, Allah ya raya zuri'arki ya albarkaci rayuwar su Amin.*
   

Bismillahir rahmanir rahim.

*09*

"Me kika ce Uwani?" Hajiya Umma ta jefa wa Uwani tambayar hankali a tashe.
"Da gaske Hajiya Umma, ga can ana ta fama da ita, domin tun da aka dumfaro hanyar gidan nan haukar ya dawo sabo..." Hajiya Umma ba ta tsaya sauraron maganar Uwani ba, ta yi saurin shiga bedroom din ta, saboda ganin aikinta na daf da warware wa, ita a yanzu ba ta fatar abin da zai rabata farin cikinta, don haka mintina ƙalilan ta yi sannan  ta sake fitowa in da ta nufi fita wajen da su Dady ke tsaye cikin jimami.

Cike da matukar jimami ta ƙarasa wajen, bayan ta gaisar da su Dady ta hau tambayar mai jiki, take su ka yi bayanin duk abin da ya faru, jin ai limami yana zuwa ta yi saurin tarar numfashin Dady, "Dadyn yara ina tunanin wannan gidan ne ba ta son a shigo fa, tun da ka ce lafiya ku ka kamo hanya."

"Eh! Tabbas kema kin yi tunani, bar mu gani kafin zuwan liman din."

"Inna lillahi!  Ni Hansatu me zan gani haka? Saudatu!" Shi ne abin da Hajiya Umma ta fada lokacin da ta isa kofar gidan.

"Wallahi ke dai Hajiya kin ga ikon Allah! Lafiya lau mu ka taho da ita, amma muna shigowa layin nan sai abu ya koma haka." Dady ke bata amsa cikin jimami.

"Ikon Allah! Lallai Allah buwayi ne gagara misali, to Dadyn yara ko dai shiga cikin gidan ne ba ta so?" Umma ta yi masa tambayar a darare, don gani take kamar ba zai yadda da shawarar ta ba, ga mamakinta sai ta ji ya ce

"Nima abin da nake tunani kenan, dama ba wai zama za mu yi ba, kawai Alhajin mu da Hajiyar mu za su ganta, amma tun da haka ne bari kawai mu tafi can din, idan yaso a kai su su ganta." Yana gama faɗin haka ya shiga Mota.

Wani murmushi Umma ta saki na jin dadi, don ba ta yi tsammanin haka ba.

"Amma Yaya Alhaji Babba ya ce ajira Malam Umaru fa." Baba Musaddam ya fada.

"Idan ya iso ka kawo shi can gidan." Amsar da Dady ya ba shi kenan yana mai tada motarsa.
Su ma sauran su ka shiga ta su, inda aka bar Baba Musaddam da Hajiya Umma tsaye.

Girgiza kai kawai Baba Musaddam ya yi, ganin sun tafi sannan ya shige cikin gida.

Hajiya Umma tana ganin sun wuce ta kwashe da wani irin dariya har tana rike ciki, ta ce "Ba dai ni ce ba, ai wannan kaɗan ne, na tsaneki Saudatu na tsani zuri'arki da duk wani wanda ya ji ɓance ki." Tana gama faɗin haka ta shige cikin gida.

****

"Sun tafi kuma? Wane irin sun tafi?" Alhaji Babba ya yi tambayar cikin takaici, bayan Baba Musaddam ya gama fada masa yadda aka yi.

"Ka dai yi hakuri Alhaji, amma, zan jira idan Liman din ya iso sai mu tafi tare da shi gidan nata." Cike da ladabi Baba Musaddam ya ke magana.

"Toh ai shi kenan Allah ya ba ta lafiya."

"Amin." Duk su ka amsa har Hajiya Babba dake zaune cike da jimami.

Cikin haka Liman Umaru ya kira Alhaji yana sanar masa da zuwansa, ya fita sun gaisa yake yi masa bayanin komai, inda Baba Musaddam ya kara yi masa bayanin, gyaɗa kai ya yi cikin fahimtar bayaninsu, sannan ya fara yi masu batani shima.

"Kar ka damu Alhaji, in sha Allah komai zai daidaita, irin wannan tun wuri ake yin magana, da tun tuni ne ina mai shaida ma da tuni an samu waraka, amma a haka din ma karka damu, idan Allah ya so zuwa gobe zan kawo maka wasu magunguna, dana sha da na hayaki, idan aka yi sa'a sai a samu waraka."

BAN ZACI HAKA BA (Tawa kaɗɗarar)Where stories live. Discover now