13

348 21 4
                                    

13

A kofar shiga mall na *DARAJA SUPERMARKET*, ya yi parking motar, a wajen da aka tanadar domin aje motoci, sannan ya juya tare da kallonta ya ce
“Mu Shiga ciki Kanwata. ”
Cike da nutsuwa ta bude motar ta fita, a jere su ka shiga babban mall din, duk wanda ya kallesu zai gane cewa su din masoyane wanda su ka mutu akan junansu, musammam irin riritawar da Ya Usman ke yi wa Nasreen.
Ko a wajen zaben abubuwan babu abu daya da ta dauka duk shi ya zabar mata, kusan duk kayan makulashe ne, sanan su ka nufi wajen biyan kudi, yana gama biya ya dauki kayan sannan su ka fita.

Cike da nishadi su ka nufi gidan, horn ya yi maigadi ya bude masu kofa, shi kuwa Ya Usman ya tura hancin motar cikin gidan, suna cikin motar suna ci gaba da hira, ban da murmushi ba abin da Nasreen ke yi.

Zaune yake kan daya daga cikin kujerun da aka kawata wajen da su, tun da ya baro gidan Baba Musaddam ya kasa samun nutsuwa babban burinsa ya ga dawowar Nasreen, duk da yasan Nasreen din can gidan ya barota amma sau uku yana tambayar Zuhra akan har yanzu Nasreen ba ta dawo ba.
Amsa daya Zuhra ke ba shi
“Eh! Yaya.”
A na karshe ma rufe Zuhra ya yi da masifa akan me yasa basu tafi tare da Nasreen din ba.
“Ka yi hakuri Yaya lokacin da ta tafi muna aiki ne da Aunty, kuma sai da Aunty ta ce ta bari sai gobe mu he, shi ne ta sanya kuka ita dole sai ta je ta ga halin da Ya Usman yake ciki, shi ne Aunty ta sanya aka kaita.” Cikin ladabi Zuhra ta ba shi amsa.
Shi kam jin da ya yi har kuka Nasreen ta yi akan an hanata zuwa dubo Usman sai ya ji ya kara shiga taahin hankali fiye da da.
Hancin motar na shigowa gidan ya zuba mata ido, da wani irin faduwan gaba yake kallon motar, musamman da ya ga wani lyakkyawan murmushi kwance a kan fuskar Nasreen. Bai gama shiga rudu ba sai da ya ga Usman ya bude mata kofa, ita kuma ta fito da wani irin nutsuwa idonta akan Usman tana yi masa wani kallo kasa-kasa, wanda masoyin gaskiya kawai ake iya yi wa. Sannan su ka fara tafiya a jere, kallo daya mutum zai masu ya tabbatar masoya ne na hakika. Musamman tsadadden murmushin da Nasreen ke jifar Usman da shi.
Hisham na mijin duniya, saurin dauke kansa ya yi a lokacin da su ka iso kusa da shi.
  “Sannu da hutawa Bros.” Usman ya fada tare da matsawa wajen da yake zaune.
“Yawwa da alama ka samu lafiya ko? Tun da ga yi har ka iya yin tuki.” Da siririyar murya yake magana, kuma cikin kulawa.”
“Alhamdulillah! Na samu sauki kam, kanwata na rako saboda babu wanda zai kawota, Mummy ta aike direba
“Madallah!” Hisham ya fada yana mikewa.

  “Don Allah Yaya idan ka isa gida ka gaisar min da Aunty Maryam.” Shagwababbiyar muryarta ne ya daki dodon kunnesa, wanda ya tilasta masa dakatawa da tafiyar da yake yi, tare da juyowa ya yi sa'ar zura idonsa cikin nata. Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma cikin wani voice mara sauti ya ce

“Dan aike kika mayar dani?”

Kallon da yake yi mata ya masifar kashe mata jiki, wani kasala take ji wanda ba ta taba jin irinsa, ga yi ta kasa cire idonta daga cikin na shi, ko da yake ta yi kokarin yin hakan amma ta gaza.

Da kyar ta iya jawo kalmomi biyu ta furta “A'a!” Allah Ya sa Usman bai ma san abin da suke yi ba, domin shi gaba daya hankalinsa na kan waya.

“Ok! Ya furta sannan ya fara tafiya, tana kallonsa har ya shiga motarsa, sannan ta ce wa Usman

“Yaya mu karasa ciki mana, shi fa Ya Hisham ya wuce.”

“Ayya! Sorry Kanwata, kin ga na mayar da hankali kan waya ko? Magana muke da wani mutum kan aikin da zan yi masa.” Ya dire maganar yana mikewa, sannan su ka karasa shiga falon, in da su ka iske Aunty tare da Zuhra sai hira suke, gaisawa su kai da Usman, Aunty na tambayarsa jikinsa.

“Da sauki sosai Aunty, jiya iwar haka ai ban san ina kaina yake ba, yau kuma gani na kawo Kanwata gida da kai na na yi driving. "

“A lallai kam lafiya ta samu, Allah Ya karo ingatacciyar lafiya.” Amin su ka hada baki wajen fada.

“Lafiya kike ke kam?" Aunty ta jefa wa Nasreen tambaya.

“Wallahi Aunty kai na ciwo yake, yanzu ma tashi zan naje na sha magani...” Ta kai karshen maganar tana mikewa.

“Subhanallah! Kanwata kanki ke ciwo? Kodai za mu tafi asbiti ne?" A rude Usman ya jera mata tambayoyin. Aunty cika ta yi da mamaki sosai ganin yadda ya rude lokaci daya.

“No! Ya Usman ba sai mun je asbiti ba, idan na sha magani zai warke.”

“Tom yi sauri ki sha please. ” Har wani marairaicewa yake lokacin da yake mata magana.

Murmushi ta yi kawai sannan ta wuce bed nasu, Da ido Aunty ke bin Usman da Nasreen, ita abin ma mamaki ya ba ta, ganin yadda Usman din ke yi, ita kuma Nasreen sai basarwa take yi. Zuhra ma abin ya ba ta dariya, don har sai da ta dan dara kadan sannan ta bi bayan Nasreen.

“Wassh! Nasreen ta fada bayan ta shiga bedroom dinsu tare da fadawa kan gado. Dama can ba wani ciwon kai, kawai so take ta kebe ko za ta samu damar yin tunanin kallon da Hisham ya yi ma ta dazun, abin ya matukar tsaya mata a rai, lallausan murmushi ta saki tana kara rungumar filo.

“Ai shi ne kika kwanta ba ki dauki maganin ba?" Zuhra da dama ta biyo Nasreen a baya ta jefa mata tambaya.

“Zan sha ne, na dan kwanta ne na kara samun sassauci.” Nasreen ta ba ta amsa tana lumshe ido.

Kafaɗa kawai Zuhra ta ɗaga, sannan ta shige toilet.

****

Rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin sauye-sauye da ake samu na zamani, bangaren Usman da Nasreen kuwa ko yaushe abin gaba yake, duk da har yanzu bai fito fili ya fada mata ba, amma ta fara fahimtarsa ta wasu bangarorin, abin damuwarta daya alkawarin da ta daukarwa Hisham, ba ta san wanne mataki zai dauka a kanta ba muddin ya kamata tana soyayya a bayan fage, wannan tunanin shi ne ya hana ta sakewa da Usman duk da kullum a hanyar zuwa gidan Daddy yake, kawai don ya ga Nasreen.

*****
To haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, cikin sauye-sauyen yanayi, musamman a bangaren Tafida family. Wanda farin ciki a ko yaushe shi ne kan gaba.

Usman ne zaune a gaban Baba Musaddam wato mahaifinsa, kasan a ƙasa ya kasa yin maganar da ta kawo shi, sai jan yatsun ƙafarsa da yake yi.

“Wai lafiya kuwa Usman?" Baba Musaddam ya jefa masa tambaya.

“Ummm! Dama Baba zuwa na yi akan in yi ma maganar kanwata Nasreen.” Sai kuma ya yi shiru.

“Ya kuma ka yi shiru? Ci gaba da bayaninka mana.”

“To Baba don Allah ina neman alfarma a taimaka a aura min Nasreen, wallahi ita nake so da kauna.”

“Haba Usman? Dama wannan matsalar ke sanya ka cutuka? Amma shi ne ba ka taɓa fada min ba sai yanzu? Ai shi kenan tun da haka ne zamu zauna da iyaye da Yaya da sauran yan'uwa, duk abin da muka yanke za ka samu labari.”

“Na gode sosai Baba.” Usman ya fada cike da fara'a, sannan ya bar wajen.

Girgiza kai Baba Musaddam ya yi, shi ma ya mike don zai fita yana da ganawa da wasu mutane.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 21, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAN ZACI HAKA BA (Tawa kaɗɗarar)Where stories live. Discover now