*BAN ZACI HAKA BA*
_(Tawa kaɗɗarar)_*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION* _(HWA)_
*Ina mai farin cikin sanar daku duk wacce take son ci gaban Labarin nan, to fa sai dai ta je wattpad ta same shi.*
_My wattpad username zulayheartrano89_
Bismillahir rahmanir rahim.
*07*
Fitowar Aunty daga bedroom shi ya sanya Hisham yin shiru, don ya kula har yanzu fuskarta babu wani walwala. Hannun Nasreen ta kama su ka nufi bedroom, inda ta haɗawa Nasreen ruwa mai zafi ta ce ta yi wanka. Bayan ta fito tea mai zafi Aunty ta miƙa mata, ba ta wani sha da yawa ba ta ce ta koshi. Pharacitamol Aunty ta ɓallo mata ta ce ta shanye, duk da Allah ya yo ta sam batta kaunar magani, amma haka ta amsa ta shanye. Za ta kwanta Aunty ta hana, sai ma hirar da Aunty ta fara janta da shi, duk don kar ta kwanta.
Shi ma Hisham ganin sun shige bedroom, sai ya mike da ya yi na shi bangaren, ruwa kawai ya watsa bayan ya yi shafa'i da wuturi, sai ko ya yi kwanciyar sa.
Washegari da ƙarfe shida na safe, Zuhra ce ta mike bakinta dauke da addu'ar tashi daga bacci, kallon dakin ta soma yi ga mamakinta babu Nasreen a ciki. Da sauri ta dauki hanyar fita ko dankwali ba ta tsaya ɗauka ba, tura bedroom ɗin Aunty ta yi, ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba. Ƙarasawa ta yi tare da zama a bakin gadon tana dan ya ye mata bargon da take rufe ciki.
Jin ana ya ye mata bargo, ya sa ta bude ido. Fararen idonta tas kamar ba wacce ta tashi daga bacci ba, su ka sauka akan fuskar Zuhra, ta sakar mata murmushi.
"Wato shi ne ma kika yi min wayau ko?" Zuhra ta tambaya ta yi mata hararan wasa.
"Lah! Sis me na yi?" Nasreen ta yi mata tambayar tana zaro ido.
"Ba ga ki kin kwana dakin Aunty ba? Ki ka bar ni ni daya a dakinmu?"
"Oh! Sorry nima fa ban san lokacin da bacci ya daukeni ba."
"Ai shi kenan, bari na yo alwala kin san Allah ko sallah ban yi ba."
Zaro ido Nasreen ta yi ta ce "Ba ki yi sallah ba? Ni na yi tun da asbah, ban sani ba da na tashe ki, Ai kam tashi ki yi sauri ki yi, tun kafin Aunty ta shigo." Da sauri Zuhra ta mike bata ɓa ta lokaci ba har ta idar, sannan su ka shiga aikin gyaran dakin, suna yi suna hira har su ka kammala.
Falo su ka koma shi ma suna ci gaba da gyara shi. "A'a'a yau yammatana da aiki aka tashi kenan?" Aunty ta tambaya lokacin da take shakar kamshin turaren da suka turare falon da shi. Murmushi kawai su ka yi sannan su ka soma gaisar da ita, amsawa ta yi fuska fal fara'a tana sanya masu albarka.
Ko da za ta shiga kicin hada abin break tare su ka shiga, su na cikin aiki Aunty ta dube su ta ce "Wai duk me ya ja maku tashi da wuri haka? Ni dai ban saba gani ba?"
"Kai Aunty mu ne ba ma tashin wuri?" Nasreen ta yi tambayar cikin shagwaba.
"Eh kuna tashi da wuri idan akwai abin da kuke bukata, ko kuma yau don ganin Dodanku na gida be? Kuna tsoron yin kuskure ko?"
"Lah! Ba fa haka bane Aunty." Sai ta yi shiru ta kasa ci gaba da maganar ta, zuwa can ta ce "Aunty dama cewa muka yi don Allah ki rokar mana Ya Hisham ya bari mu je gidan Mummy."
"A haf ko da na ji, ni dai na san ba haka nan banza za a ta yi ni aiki ba." Fuska ɗauke da murmushi Aunty ke magana.
"Please Aunty." Nasreen ta fada kamar za ta saki kuka.
"To mu kammala tukun." Dukkan su ihun jin dadi su ka sake, sannan su ka ci gaba da aikin, sai ƙarfe tara saura minti goma su ka kammala. Farfesun kan rago ne sai kunun gyaɗa da soyayyen doya da kwai, wacce aka yi mata miyar vegiteble.
YOU ARE READING
BAN ZACI HAKA BA (Tawa kaɗɗarar)
Actionlabari ne na tausayi, sadaukarwa, jarumta, uwa uba kuma soyayya wato kauna, labarin Hisham da Nasreen, ku biyoni don jin yadda zata kaya.