|10| THE UNEXPECTED

2.5K 248 73
                                    

"I realized I was thinking of you, and I began to wonder how long you'd been on my mind. Then it occurred to me: Since I met you, you've never left... If I know what love is, it is because of you"

♤♤♤♤♤♤♤

ABU-YAZEED RESIDENCE

A yau kwana daya kenan da aka sallami Zehra daga asibiti.

Tunda ta dawo kuwa take ta hutawa domin kuwa Zain ya bata hutu 'bed rest' na kwana uku kafin ta cigaba da al'amuran ta.

Wuraren qarfe goma sha daya na safe tana kwance a cikin Duvet tana hira da qawarta Hidaya wadda ta zo duba jikinta yayinda take replying messages din mutane da suka yi wishing dinta quick recovery while she was ill.

Fadeela ta je aiki... Khadeeja kuma ta tafi school.

Baraka mai aikin su ce ta shigo riqe da wani cute bouquet na white flowers da wata 'yar qaramar takarda a ciki.

Zehra wadda ta sa ma bouquet din idanuwa ce ta tashi zaune da sauri tace "wow, Baraka daga ina haka??"

Baraka ta qarasa wurin ta tace "Anty dama Hajiya ce ta bani in kawo miki"

Da sauri ta miqa hannu tace "bani in gani"

Baraka ta miqa mata yayinda Hidaya tace "I have never seen a bouquet this cute, babes waye ya aiko miki? dama kina da boyfriend kike ta boyewa ko?? Allah ya kama ki"

Baraka ta miqa mata yayinda Hidaya tace "I have never seen a bouquet this cute, babes waye ya aiko miki? dama kina da boyfriend kike ta boyewa ko?? Allah ya kama ki"

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


Zehra wadda na ga tana karanta takardar kuwa dafe qirjin ta tayi yayinda ta zaro idanuwa cike da mamaki tace "what???"

Hidaya ce tace "Babes lafiya??"

Kafin Zehra tayi magana ne Anty ta shigo dakin tana murmushi tace "ai sai ki fito ki je ki ga kayayyakin da ya aiko miki, kaya dayawa kamar mai shirin bude shago.."

Gani suka yi Zehra ta yaye Duvet tare da sauka a guje ta fita.

Hidaya da Anty ne suka bi bayan ta yayinda Anty take fadin "lallai akwai Magana"

*********

Tsaye take a kicin dinsu tana kallon kayan da ya aiko. Sossai ta cika da mamaki domin kuwa Carton Carton ta gani na drinks kala-kala da packets din chocolates da su biscuits masu tsada. Ga su ice cream nan kala kala da su fresh milk. Fruits kuwa kamar an shiga gona an kwaso.

Hannu ta sa ta rufe bakin ta cike da mamaki.

Juyowa tayi ta kalli Anty tace "I can't believe this"

ZEHRA | ✔Where stories live. Discover now