|22| BOOM

1.8K 193 85
                                    

"Pain is such an uncomfortable feeling that even a tiny amount of it is enough to ruin every enjoyment"

♤♤♤♤♤♤

VILLAGE XXX,
MAIDUGURI

A yau Kwana hudu kenan da suka shiga qauyen. Sossai ake ta fafatawa dare da rana.

A daren yau ne Su Mustapha suka shiga ainihin wurin da Terrorists din suka riqe mutanen qauyen wandanda aka rufe su a cikin wani masallaci babu ci babu sha tsawon kwanaki.

Tunda suka shiga wurin kuwa babu abinda kake ji banda harbin bindiga.

Suna cikin wannan halin ne company din da suke biye da Mustapha suka neme shi suka rasa.

Hakan kuwa ya tayar musu da hankali amma a dalilin ana tsakar yaqi ne suka cigaba da bude wuta yayinda second in command dinshi yayi taking over.

A wannan lokacin kuwa wata dama Mustapha ya samu wadda kuwa idan har ya sake ya shiga ba lallai bane ya fito da rai..

On normal basis yakamata ne yayi commanding wasu su shiga amma kuma Our Mustapha being the fearless One ya wuce ya shiga da kanshi.

Wannan ne yasa Company dinshi suke bala'in son shi, baya taba sa su at risk, he'd rather risk his life for them.

Mustapha dai mamayar terrorists din yayi, basu ankara ba suka ji an buda musu wuta wanda kuwa kafin suyi wani motsin kirki tuni ya fara share su.

Hakan ya ba battalion din shi gaba daya damar shiga wurin da confidence yayinda suka bashi support and together, they finished them all.

Sossai jarumtar Mustapha da rashin tsoro yana ba colleagues dinshi mamaki sannan yana birge su. If not for dabarar da yayi, da zai yi wahala suyi nasara. He risked his life once again and they were all proud of him.

A wannan lokacin kuwa banda ihun 'yan qauyen babu abinda kake ji. Hankulan su duk a tashe a dalilin qarar bindigogi da hayaniya da suka dinga ji non-stop.

Tuni sojojin suka balle qofar Masallacin suka fitar da su.

Yawancin su kuwa duk sun jigata.

Tsofafin cikin su da yara duk sun tagayyara.

Abin ban tausayi ma wasu sun mutu sannan an harbe masu taurin kai wadanda da alama sunyi gardama ne.

***********

Tsaye suke suna bincika Maps da sauran tarkacen da Terrorists din suka bari.

Wata dattijiya ce ta nufi wurin Mustapha ta riqo hannun shi tace "Yaro Allah yayi maka albarka da kai da yaran ka, Ubangiji Allah ya sada ka da alkhairin da yake cikin duniyar nan. A yadda ka ceci rayuwar mu Allah ya dafa maka a dukkanin al'amuran ka. Matar ka ta gode ma Allah da ya bata jarumi a matsayin miji. Ka fadi mata Inna Binto tace kar ta sake ta bata maka domin kuwa Allah bazai barta ba"

Gani nayi Mustapha yayi murmushi yayinda yake ta sauraron ta.

Ji nayi ta cigaba da fadin "...Yaran ka dole ne suyi alfahari da kai..."

Daya daga cikin sojojin da suke ta zuba 'yan qauyen a cikin motoci ne ya qaraso wurin su yace "Mama mu je ki shiga mota.."

Mustapha ne ya dakatar da shi tare da fadin "don't worry, she will be right behind you..."

ZEHRA | ✔Onde histórias criam vida. Descubra agora