|09| THE CONSEQUENCE

2K 220 13
                                    

"When you choose an action, you choose the consequences of that action. When you desire a consequence you had damned well, better take the action that would create it"

♤♤♤♤♤♤♤

OMAR TAFIDA RESIDENCE

Wuraren qarfe goma sha daya na dare tana kwance a kan gado cikin Duvet tana ta kyarmar sanyi.

Jikinta yayi zafi kamar wuta.

Fadeela wadda take a rikice ce tace “Zee kin dai san cewar laifin ki ne ko? Me zai sa ki shiga cikin ruwan sama bayan kin san cewar Papa yayi warning dinki? You know perfectly well cewar duk lokacin da kika shiga ruwa sai kin kwanta. Toh wai tsaya ma in tambaye ki, me kika je yi a cikin ruwan?”

Before Zehra could respond ne ta sauka daga kan gadon ta cigaba da fadin “...gaskiya zan je in fadi ma Mummy, you need to go to the hospital. thank Goodness My sweetheart, your brother is on night shift”

Muryar Zehra qasa qasa tace “Please Dee don’t tell Mummy, zan samu sauqi”

Fadeela dai bata saurare ta ba ta wuce ta fita.

Aikuwa ba da jimawa ba sai gata nan ta dawo tare da Mummy harda Daddy.

Ganin yanayin jikin basu wani bata lokaci ba aka tarkata ta aka sa ta mota.

Sanin cewar Mustapha yana fama da nashi zazzabin ne yasa suka tafi asibtin ba tare da an neme shi ba.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

NATIONAL HOSPITAL

Sossai Zehra take jin jiki domin kuwa a duk lokacin da ruwan sama ya bige ta sai ta kwanta.

Zain ne ya bata taimakon gaggawa wanda kuwa har allurar bacci yayi mata.

*****************

Bayan kusan awa daya gaba dayan su suna zaune a waiting room na dakin da aka kwantar da Zehra.

Fadeela ce ta basu labarin abinda ya faru and they were all worried thinking about what made her to enter the rain.

Papa wanda ran shi yake a bace ne yace “wallahi Zehra bata jin magana, ta sani cewar tana samun matsala idan ta shiga ruwa me zai sa ta shiga?? Idan ta farka I will deal with her”

Su Anty da Mummy ne suke ta bashi haquri.

Zain wanda ya shigo waiting room din riqe da takardu a hannun shi ya samu kujera ya zauna yace “Papa I am going to keep her here zuwa gobe mu gani, so I think zaku iya komawa gida. Dee da Deeja zasu zauna da ita but she will be fine In sha Allah”

Ya kalli Anty ya cigaba da fadin “Anty ki hada mata 'yan kayayyakin da zata buqata sai ki ba driver ya kawo mata”

Da wannan ne su papa suka yi musu sallama suka tafi.

************

OMAR TAFIDA RESIDENCE

A bangaren Mustapha ma kusan halin da Zehra take ciki shima shi yake ciki.

Yana nan kwance a cikin Duvet yayinda jikin shi yayi zafi sossai. Zazzabi ne ya saukar mishi shima.

Da qyar ya lallaba ya dauko PCM a cikin first aid kit ya sha.

A rayuwar Mustapha babu abinda ya tsana irin allura.. mamaki yake yi yadda kawai mutum zai je asibiti a yi mishi allura yana ji yana gani, hakan yasa da zarar ya ji jikin shi babu dadi yake saurin shan magani don kar ciwo ya kai shi ga kwanciya wanda har zai janyo ayi mishi allura.

ZEHRA | ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang