Kuskure 29&30

1.1K 53 0
                                    

🌸 *KUSKURE*🌸

   Written
   *by*👇🏻
Aysher Abbakar(Meerah)

® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on wattpad @aysherabbakar

'''Page'''
*29&30*

Belt ɗin jikin shi ya fara cirewa, ganin da gaske yake ta fara zandama ihu.

Da gudu Hameedah ta fito a ɗakinta jin momin ta na ihu.

Daddyn ta ta hango yayo kan maman,  da gudu ta gangaro daga steps, kafin ta ƙaraso ya zuba mata a jiki,  wani ihun ta saki tana murza wajan.

Hameeda ce ta sha gaban shi ta riƙe belt ɗin tana kuka.

Idon shi ya riga da ya rufe,  wurgar da ita yayi gefe ya cigaba da zubawa nabeelah bulala.

Saleem ne ya fito jin hayaniyar tayi yawa.

Ganin ana dukan mum ya sauko da sauri ra riƙe hanun baban sannan ya dubeshi da idon shi wanda da ƙyar yake buɗewa yace" haba daddy wannan ba girmanka bane"

Muhammad ne ya dubeshi rai ɓace yace" get off me"

ƙin sake shi yayi yace" daddy please mana, ka ƙyaleta dan Allah, kai haƙuri... Plx"

Ya ƙarasa maganar yana haɗa hanun shi da na daddyn shi.

Sake mishi belt ɗin yayi ya juya ya wuce ɗakin shi.

Juyowa saleem yayi ya dubeta yace" mum.. U again?  Why?  Dan Allah na rokeƙi ki barmu mu zauna lafiya, meye abun ɗaga hankali dan ya ƙara aure?  Meye baya miki dan Allah... Kefa ba yarinya bace"

Harara ta watsa mishi ta miƙe da ƙyar dan jikinta ya fara mata tsami ta nufa ɗakinta.

Ɗaga kafaɗa yayi shima yayi wucewar shi.

Nabeelah ko tana shiga ɗaki ta sake fashewa da kuka, ba dan zafin dukan ba sai dan cin mutuncin da ya mata.

Sai da tayi mai isarta sannan ta shiga toilet tayi wanka da ruwa mai zafi sossai.

Muhammad gari ya mishi zafi, ga tashin hankalin nabeelah ga fitinan baɗɗo, ya rasa ina zai sa ranshi yaji sanyi.

Fita yayi ya nufa gidan Aysher.

Yana zuwa ya isketa tana zaune ita da yaranta.

Zama yayi ya kama kanshi, jiri yake ji dan rabon shi da abinci tun jiya da safe.

Ruwa ta kawo mishi, sipping biyu yayi ya ajiye a gefe.

Abinci ta zuba mishi yace ya ƙoshi, da ƙyar ta samu yaci kaɗan.

Juyowa tayi suna fuskantar juna tace" yaya me yake faruwa ne?  Na jika shuru, Deedat ma tun shekaranjiya wayarshi a kashe, hankalina ya tashi"

Wani ajiyar zuciya yayi sanann ya dubeta yace" Aysher dan Allah ki taimakeni, wallahi ina sonta, bazan iya rabuwa da ita ba, please ki sanya baki, rayuwata tana cikin hatsari"

Ya ƙarasa maganar kaman zai zubar da hawaye.

Kama hanunshi tayi tace" yaya ya kukayi da ita? "

Nan ya bata labarin komai har da haukan da nabeelah take.

Kallon shi tayi tace" yaya naji abunda kace, amma bai kamata ka bigeta ba tunda ita ba yarinya bace, se dai ka ɗau wani matakin akanta ta hanyar horata, amma dan Allah karka sake dukanta"

KUSKUREWhere stories live. Discover now