KUSKURE 49&50

1K 54 10
                                    

🌸 *KUSKURE* 🌸

Written
*by*👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)

Follow me on wattpad @aysherabbakar

'''Page'''
'''49&50'''

Tun da asuba Bad'd'o ta Fara aiki, Dan ta kasa komawa bacci bayan sallar asuba kaman ynda ta saba.

K'arar plates d'in da take wankewa a kitchen ne ya tashi Muhammad a bacci.

Fitowa yayi sanye da jallabiya ya nufo kitchen d'in.

Tsayawa yayi daga bakin k'ofar kitchen d'in ya hard'e hannayen shi duka a k'irjin shi yana kallon yanda take faman aiki.

Sanye take da pijamas pink colour wandon da ratsin fari a jiki.

Kanta Babu d'an kwali ta kama gashinta ta baya.

Tsayawa tayi cak da aikin dan ji tayi kaman akwai mutum a bayan ta.

Juyowa tayi a hankali, had'a ido sukayi Nan ya sakar Mata murmushi.

Sunkuyar da kai tayi a hankali tace" an tashi lafiya"

" Lafiya kalau Alhamdulillah,how's your night?"

"Was splendid"

Shuru duka sukayi sun kasa furta wani magana.

Ji tayi yace " wannan sammakon duk na zumud'in zuwa ganin innar ne?"

Girgiza kai tayi tace" kawai dai inaso mu isa da wuri ne"

6ata fuska yayi yace" am so sorry little princess, zuwanmu bazai yuwu....

Kafin ya k'arasa ganinta yayi a gabanshi, kama hanunshi tayi duka biyu ta had'a cikin nata, kaman zatayi kuka tace" please don't say no, wallahi na sa rai kan maganar tafiyar nan"

Jin muryarta ya Fara rawa ya sanya shi d'ago kanta ,hawaye ya gani cikin idonta da suke kokarin zubowa.

Girgiza Mata Kai yayi yace " don't cry princess wasa nake Miki"

Wani ajiyar zuciya ne ta kubce Mata.

Dariya yayi ya ja hancinta.

Itama dariyar tayi had'e da rufe idonta da tafin hanunta.

Juyawa tayi ta koma dan cigaba da wnke wanken ta.

K'arasa wa yayi ya nad'e hanun rigarshi ya Fara d'auraye Mata yana jerawa.

A haka suka Gama tayi mopping shikuma ya share palour.

Tea kawai ta dafa musu sannn ta dama kunun gyad'a ta soya chips nd egg sannan ta musu egg sauce.

Before u know sun kammala komai.

Seda suka jera tare kan table sanann kowa ya wuce side D'in shi Dan yin wanka.

Lokacin k'arfe takwas ne.

Ta rigashi shiryawa dan haka ta nufa dak'in shi.

Kasa shiga tayi ta tsaya a bakin k'ofar dak'in tana tunanin in ta shiga me zatace.

Ji tayi Ana k'ok'arin bud'e k'ofar.

Da sauri ta juya zata gudu.

Ji tayi an kamota ta baya.

Runtse idonta tayi jikinta ya Fara rawa.

A hankali ya janyota sannan ya juyo da fuskarta.

Har lokacin idonta na rufe.

Jin muryarshi tayi  yace " princess"

Bata amsa ba Kuma Bata bud'e idon ba.

Seda ya kirata sau uku sanann ta amsa.

KUSKUREWhere stories live. Discover now