KUSKURE 47&48

1K 54 18
                                    

🌸 *KUSKURE* 🌸

Written
*by*👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)

Follow me on wattpad @aysherabbakar

'''Page'''
'''47&48'''

Wajan k'arfe biyar Nabeelah da Lubna suka baro wajan boka.

Basu iso cikin Abuja ba sai bayan sallar Isha.

Seda ta dropping lubna sannan ta k'arasa gida.

Shuru ko Ina ba wani motsi Sena tsuntsaye, se hasken daya karad'e ko Ina Kai kace Rana ne.

A hankali ta bud'e k'ofar palour ta shiga da sand'a.

K'arar sanyin AC kawai ke tashi a palour.

A hankali take tafiya Kai kace sata ta shigo Yi.

Takalmanta a hannu tana faman zare Ido.

Bad'd'o da ke tsaye bakin k'ofar ta tana kallonta,da yake an kashe wutan corridor d'in Nabeelah Bata hangota ba.

Jikin Bad'd'o ya Bata wani mugun abu Nabeelah ke Shirin aikatawa, duba ga yanda jikinta duk datti ga zaninta a yage.

Nan ta Sha jinin jikinta,bawai tsoron abunda Nabeelah zata aikata take Yi ba.

Tsoronta karta cutar da Muhammad,Dan d'an zaman da sukayi na 'yan kwanakin Nan ya Fara shiga ranta, Dan haka ya Zama dole ta zuba Ido akan Nabeelah.

Seda ta shige dak'in ta sannan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya.

Idonta ne ya Kai kan wani abu akan gadonta.

Da sauri ta k'arasa wajan Dan tabbatar da zargin da take.

Maganine k'ulli uku kamar yanda bokan ta ya sanar da ita.

Wani ihun farin ciki tayi ta fad'a kan gadon.

Gani take zuwa gobe buk'atar ta ta biya.

Wayarta ta d'auka ta Kira Lubna.

Nan ta Bata labarin abunda ya faru.

Itama farin ciki tayi sannan tace " ai Dama na fad'a mki ki jira kiga aiki da abun mamaki gobe"

Nan sukayi sallama kowa ya kashe wayar shi.

Mik'ewa tayi ta shiga toilet Dan yin wanka.

Dan duk tayi datti Kuma yunwa take ji.

Duban agogon dake manne jikin bango tayi taga k'arfe 8:30pm.

Da sauri ta shige toilet.

Can stairs Kuma Nabeelah ce ta Sha wanka ta shirya cikin doguwar riga ta Atampa tayi Mata kyau sossai.

'Dakin Muhammad ta nufa a hankali tayi knocking.

Daga ciki aka Bata izinin shiga.

Sallama tayi sannan ta shiga.
Yana ganin ta ya sakar Mata murmushi.

Zama tayi gefenshi sanann ta gaida shi.

Cike da farin ciki ya amsa sanann ya dubeta yace " ya akayi princess?"

Sunkuyar da kai tayi sannan tace" please inaso gobe driver yaje ya taho da Amina ne dan Monday zasu resuming School"

Kallonta yayi yace" why not muje tare?"

Da sauri ta d'ago ta dubeshi tace" are u serious?"

"Of course I am"

Murna ta Fara Yi a fili, Dan tasan tayi missing gidasu ba kad'an ba.

KUSKUREWhere stories live. Discover now