kuskure 41&42

1.1K 67 2
                                    

🌸 *KUSKURE*🌸

   Written
   *by*👇🏻
Aysher Abbakar(Meerah)

® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on wattpad @aysherabbakar

'''Page'''
*41&42*

"Nabeelah me yake damunki ne Wai?"

Shuru ta mishi had'e da kau da kanta gefe.

"Magana nake Miki bakiji ne Wai"

Harara ta zabga mishi tace" Dan Allah kayi damuwarka"

Girgiza Kai yayi ya ma rasa abunda zai ce.

Wucewar Bad'd'o ta gani ta gefenta.

A zatonta sama zatayi se taga ta nufa wajan Muhammad.

Mutuwar tsaye tayi ganin Bad'd'o manne jikin Muhammad sun zuba ma juna ido.

Murmushi ya sakar mata ita Kuma ta amshi brief case d'in hanunshi, kama hanunshi tayi tace" baby muje in kaika kayi wanka kaci abinci nasan ka gaji"

Ba musu ya Fara binta a baya.

Hanyar stairs suka nufa Nan Nabeelah Tasha gaban su tana huci ta kalli Bad'd'o tace" sakar min hanun miji"

Dariya Bad'd'o tayi tace" mijinki ko mijinmu? In da hali ma ince mijina ni kad'ai"

Ido Nabeelah ta zaro tana mamaki Wai wanann k'aramar yarinyar ke fadamata Magana.

Muhammad da ranshi ya Fara b'aci yace" kiba mutane waje su wuce dalla"

Cikin takaici ta Dube shi tace" Muhammad me zaka ma wannan k'aramar yarinyar da Bata wuce sa'an 'yarka ba Dan girman Allah?"

Kallon mamaki ya Mata yace" ban gane abunda kike nufi da me zan Mata ba,itad'in ba Matata bace?"

"Yaya zanyi na sani ko matarka ce ko ba taka bace? Tunda banida shaida"

Dariyar rainin hankali yayi yace" to kuwa very soon zakiga shaida,Dan Haka matsa in wuce"

Tare hanya ta sake yi tace " se fa ka fad'amun abunda zakuyi"

Bad'd'o ce ta dubeta tace" dallah malama ki matsa ma mutane a hanya kina b'ata mana lokaci"

Gyara tsayuwar sa yayi yace" to tunda so kike kiji me zan Mata, to abunda nake Miki shi zan Mata"

Ihu Nabeelah ta sanya had'e da toshe kunnenta, inama ace mafarki take ba a gaske ba.

Tsalle ta daka da niyar cakumo wuyar Bad'd'o..

Cak Muhammad ya d'aga Bad'd'o ya rik'e ta Gam kaman za a k'wace Masa ita.

Bad'd'o ganin Haka ya sanya tayi luf a jikin shi ta kwanta.

Bai tsaya wata wata ba ya bi gefenta ya wuce.

Nan ta Fara surfa masifa da zagi tana fad'in an cuceta.

Basu bi ta kanta ba suka tafi, Kuma yak'i ya sauketa.

Esher da Billy suka tuntsire da dariya.

Bak'in ciki goma da ashirin ya cika ta.

Kitchen ta shiga da gudu kafin kace me se gata da wuk'a.

Nan Aka fara wasan gudu da su Billy,da k'yar suka iya bud'e k'ofar suka fice ko mayafi Babu.

Cikin motar suka shiga suka zauna kowa na maida numfashi.

KUSKUREWhere stories live. Discover now