Kuskure 30&31

1.3K 62 6
                                    

🌸 *KUSKURE*🌸

   Written
   *by*👇🏻
Aysher Abbakar(Meerah)

® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on wattpad @aysherabbakar

'''Page'''
*31&31*

~Assalamu Alaikum, this goes to all d fans of this novel... Ngd da kulawarku, likes nd comments, thats wat keeps me move nd strong... Nd plx those that are seeking asking different pages privately, dan Allah ku rinƙa tanbaya a groups ko wajan wanda suke tura muku zaku samu, i told u not once bana ajiye pages a wayata cox anytime yana iya gogewa, hakan ya sha faruwa dani, dan Allah ku rinƙa tanbaya a groups ko kuyi searching a wattpad, ko yaushe ina update acan.. Ngd.~

*Nd those da suke cewa pages yyi kaɗan ko in banyi typing  ba suyita ƙananan surutu, did u think this typing its easy ne?  Kunsan hour nawa nakeyi ina typing kullum, ya kamata ku rinƙa mun uzuri, bazan takura kaina ba iya abunda zan iya kenan kuma shi nakeyi,  if u guyx appreciated fine.. Media ba a taɓa musu gwaninta, kayi abun ma wataran abika da xagi, in kuma kuna ganin kasawata dan Allah inaso kuyi typing ko da readmore* '''ɗaya ne se ku fadamun hour nawa ko minti nawa kukayi kuna typing.. Ai ko sallah ne akwai lokacin da Allah ya sauwaƙe mana mu huta balle wani typing.. Dan Allah kuna mun uziri nima sometimes ina bukata hutu, kuma Inada aikin da nakeyi bawai typing ne Damuwata Ba '''. Thnx

Washegari misalin ƙarfe 9 Deedat ya iso garin Abuja, bai tsaya kiran driver ba, taxi ya nema ya wuce gidan shi.

Wanka kawai yayi sanann ya rama sallolin da ya rasa sanann ya canja kaya ya nufa gidansu, dan bai sanar ma kowa da dawowar shi ba.

Da sallama ya shiga,  Ammi ya gani zaune tana kallon BBC world, mamaki ne ya cika ta ganin Deedat, mutumin da zaiyi sati sai gashi kwana huɗu ya dawo?

Murmushin yaƙe ya mata sanann  ya zauna  kusa da ita yana gaisheta.

Zuba mishi ido tayi dan ta kasa amsa gaisuwar, gani tayi ya rame hasken shi ya ragu, sunkuyar da kanshi yayi ƙasa kaman mara gaskiya.

Sa hannu tayi ta ɗago fuskarshi tace "Ahmad me yake damunka?  Ko aikin ne ya  sanya ka koma haka?  Meya dawo da kai yanzu? "

Kasa bata amsa yayi, dan baisan wanne daga ciki zai fara amsa mata ba, saboda tanbayoyin da ta watso mishi lokaci ɗaya.

Ganin yayi shuru ta tabbatar bashida lafiya.

Bata kai ga sake magana ba sallamar muhammad da Ayser ya katseta.

Tana ganin su tace" Alhamdulillah, gwanda da Allah ya kawoku,  kuzo ku tayani tanbayar shi ko Allah zai sa ya faɗa muku abunda ke damun shi"

Kallo ɗaya ya musu ya sake sunkuyar da kai.

Zama sukayi suka gaida ta, Aysher ce ta dubeshi tace" Dee yaushe ka dawo"

"Yau da safe"

Ya bata amsa ba tare da ya kalleta ba.

Muhammad kasa cewa komai yayi, dan duk hankalin shi baya wajan su, tunanin matarshi kawai yake, a ina zai samo ta.

Ammi hankalinta ya fara tashi, ganin yau ɗanta ya koma miskilin gaske.

Kiran sunanshi tayi a karo na farko, ya amsa mata.

Ta sake cewa" Ahmad ka ɗago ka kalleni kamun magana"

KUSKUREWo Geschichten leben. Entdecke jetzt