29

3.1K 288 20
                                    

   *RUHI DAYA*
                               29

©Hafsat Rano
Haske Writers Association💡

This page is dedicated to my one and only dota BILLY S FARI. Thank for all the love and care, i appreciate it wholeheartedly 💕❣️

Danne kiran tayi tana tsaki, matar da tun rashin lafiyarta bata kira taji komai akai ba shine yanzu zata wani kirata, sannan ko da Ahmad ya dauko guguwar auren sa babu wanda ya hanashi ciki, kiran ne ya sake shigowa ta d'aga ba ason ranta ba

"Ina kwana?" Ta fad'a muryarta a cunkushe

"Seema, kuna lafiya?"

"Lafiya lou." Ta amsa a takaice

"Kina ji?"

"Eh."

Kasa tayi da muryar ta sosai

"Ki tabbata baki bar yarinyar nan da Ahmad ya auro ta sake a gidan nan, ki sani zaman yarinyar nan yana daidai da rugujewar zaman lafiyarki."

"Why are u telling me all this?" Ta tambaya tana yatsine fuska

"Emm emm kin gane Seema, taymakon ki nake son yi, kinga ai am like a mother to you ai."

"Ni gaskia ban fuskanci komai ba, bayan haka ma wlhi bacci nake kika katse min shi, I tot wani important magana ne, please ki bari in na tashi sai mu k'arasa."

"Seema..."

"Bye."

Katse kiran tayi taja k'aramin tsaki

"Munafukan banza duk ina sane daku."

Gaba d'aya sai ta nemi baccin ta rasa, saukowa tayi ta shige toilet tana sakin tsaki, sai data shirya tsaf sannan ta fito falon, lokacin Sadiya ta share ko ina ta gyara tsaf tana zaune tana sauraron shirin barka da hantsi data kunna a radio wayarta, fitowar Seema yasa ta dago suka hadu ido, tabe baki Seema tayi ta wuce kitchen, conflakes ta hada a k'aramin bowl ta jefa kankara ciki ta fito falon, kallon Sadiya tayi tana yatsine fuska tace

"Please ki rage volume d'in mana, karar na hawar min kai."

Da sauri Sadiya ta rage volume d'in dan ita fa Seeman nan bala'in kwarjini take mata, daya daga cikin kujerun falon ta kama ta hakimce tana shan conflakes din tana danna wayar ta, kira wannan, kira wannan tun da ta zauna takeyi, ta gefen ido Sadiya ke satar kallon ta, yar gayu ce sosai ko a yadda take maganar ta, turancin da ke zaune rad'am a bakinta shi ya k'ara mata class, sai data gama waye-wayen ta daidai lokacin aka kawo wuta, d'aki ta shiga ta dauko jakar series film d'inta ta baje ta ciro wanda ta jima da kalla saboda babu sababbi ta fito falon, lokacin Sadiya ta tashi ta shige ciki, sauke curtains d'in d'akin tayi baki d'aya ta kwanta, bata dade da kwanciya ba bacci yayi awon gaba da ita, chan cikin bacci taji ana buga kofar d'akin, tashi tayi tasa hijab d'inta ta bud'e kofar,

"Kizo kina da bakuwa."

Gyara zaman hijab din nata tayi ta fito falon, fad'ad'a fara'ar ta tayi ta k'arasa cikin falon

"Laa anty Husna."

"Na'am amarya."

"Sannu da zuwa."

Zama tayi suka gaisa, hira suka shiga yi Seema na jinsu bata tanka musu ba, Sadiya na lura da ita, ganin yadda take ta bata fuska yasa ta mik'ewa tace

"Mu shiga ciki anty Husna."

"Owk."

Cikin d'akin suka shige Seema tabi su da kallo tana tab'e baki, ita sam husnan nan ba class d'inta bace shiyasa ba wani sabawa sukayi ba.

RUHI DAYA (Completed✅)Where stories live. Discover now