31

3.2K 289 18
                                    

*RUHI DAYA*
                31

HAFSAT RANO

_HASKS WRITERS ASSOCIATION_

WHERE ARE U *DR*. *BINTA* *(TEEMAH GABAS)* HERE IS YOUR PAGE. SAI NAZO ASIBITI KARBAR PARACETAMOL 😂🙊

***

"Bby, Halima, Halima!!!

"Menene?!!!"

rik'e ta yayi kam ganin yadda ta firgita har tana neman hanyar fita, kin sauraron sa tayi idon ta a rufe ta cigaba da ihu dan ba k'aramin tsorata tayi ba, ganin idan ya barta xata tara masa jama'a yasa yayi saurin had'e bakinsu waje d'aya yana saka ta ajikinsa.

Ajiyar zuciya ta dinga saukewa a hankali a hankali, Ahmad dake shafa kanta a hankali ya zuba wa kofar toilet ido, idan har da gaske ne abinda yaji a yanzu toh lallai mafita d'aya ce, share gumin daya taru a saman goshin sa yayi yana gyara mata kwanciya jin tana fitar da numfashi a wahale,

"Am so sorry, i had to do this kinji." Shiru bata amsa ba ya dan leka fuskarta sai yaga ashe tayi bacci, a hankali ya gyara mata kwanciyar ya shiga toilet, tsaftace jikin sa yayi ya dauro alwala yazo ya tada sallah, ya jima yana rokon Allah akan matsalar su kafin ya koma ya kwanta, yadda yake jin gobobin jikinsa na wani irin zugi kamar an buga masa karfe had'e da wani irin zazzafan ciwon kai yasa zazzabi yi masa sallama. Idonsa biyu har aka kira sallar asubah be samu ya koma ba saboda gaba daya baccin ya kauracewa idonsa, zama haka bazai kawo musu mafita ba ko dan lafiyar Sadiya, a yadda ya gane a yanzu masu bibiyar su sam basa son tarayyarsa da Sadiya, koma menene dai akan ta ne duk wannan abun yake faruwa. Shiru yayi yana tuna abinda ya faru dazun, daidai lokacin da komai ya kusa zama daidai sai ya fara jin kamar ana kokarin rabashi da karfin jikinsa, a yadda yaga siffa da kamaninnin Sadiyan sun sauya sun rikid'e masa zuwa wani mummunar kama ya sashi ja da baya ya kasa cigaba da abinda ya faro, abinda be sani ba shine shin ya samu cimma muradin ransa ko kuwa babu wani abu makamancin hakan da ya faru? A halin yanzu bazai iya cewa komai akai ba sai dai ya d'aura d'anbar sanin koma menene da yake kokarin tarwatsa rayuwarsu.

***
Kallon d'akin tayi ganin har tara ta wuce bata ji motsin su ba, duk yadda take jin kishin hakan sai ta danne dan tabbatar da lafiyar su, tsaye tayi tana tunanin yadda zata tashesu, bataso ta buga musu kofa ya zama na cewa baccin suke da gaske shi ya sasu makara tabbas zataji babu dadi, fasa bugawar tayi ta koma ciki tana dakon tashin su, chan ta jiyo kamar maganar Ahmad din a falo, tashi tayi ta fita falon ta tarar dashi yana waya, magana suke da Dr Ibrahim akan rashin zuwan sa aiki, anan yake sanar masa shift d'in rana yake dashi yau kuma ba lallai ma ya samu shigowa ba, so yake ya duba masa ko akwai wanda zasuyi exchanging sai ya karb'e shi

"Karka damu, sai kawai na rik'e maka ba damuwa."

"Thank you dr."

"Ba damuwa, ya maganar visiting d'in ne? Ya kamata ka fara ga Aurora ga Standard plus Premier duk suna neman Neurologist kawai ka musu mail."

"Owk... Zanyi in Sha Allah."

"Ya kamata kam, a gaida amarya da uwargida." Ya fad'a cikin sigar tsokana

"Uwargida first." Ya bashi amsa yana murmushi.

"Kai ka sani, matsoraci."

"Whatever." Yayi dariya

Kallon Seema yayi ya saki murmushi duk kuwa da karfin hali kawai yake amman baya jin dadi.

"Good morning dear."

"Morning yan mata nah, ya kika tashi?"

"Am fine, na jiku shiru tun daxun." Ta fad'a tana kallon d'akin Sadiya. Kallon ta yayi yana karantar yanayin ta, she's so jealous from the inside amman she's trying to hide it, he never expect that from her.

RUHI DAYA (Completed✅)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang