2

4.7K 350 9
                                    

*RUHI DAYA*
                      2

©Hafsat Rano

Haske Writers Association💡

*****
A gajiya ya dawo tikis, tun daga kofa ya fara cire bakin sau cikin sa, farar safa ce kal saye a kafarsa. Haka ya taka ya haye sama. Shiru saman Babu motsi ko alamar akwai mutum a gidan. Direct dakinsa ya zarce ya fara rage kayan jikinsa. Sai daya watso ruwa ya saka Ash jallabiyar sa ya sauko xuwa kasa. A falon kasa ya tarar da Seema tare da kawarta Blessing. Har yanzu fushin da take dashi ne kwance a fuskarta.
Washe baki blessing din tayi tana gaishe shi, ba yabo ba fallasa ya amsa yana neman wajen xama. Ganin haka yasa ta mik'e tana wa Seema sallama ta fice tana satar kallon bangarensa.

Bayan ta raka ta ta dawo ta hau kwashe kayan da suka shigo dashi me dauke da tambarin Unique shopping mall. Ta gefen ido ya biya da kallo da ledojin hannunta. Tabe baki yayi a hankali ya furta

"In kin ajiye kayan ki dawo nan."

Kamar bazata amsa ba haka tayi, kafin tace toh a dan xafafe ita a lallai yayi mata laifi.
Girgiza kansa kawai yayi ya shiga lalubar number Amminsa.

***
Washegari be samu ya tashi da wuri ba saboda raba Daren da sukayi suna rigima da Seema akan ya hanata kudin zuwa shopping. Da yaga dai rigimar tata ba ta kare bace kawai sai ya sauko ya barta.
Ko da yaje asibitin ma sai yan dabaru kawai yake, nauyi ne dankare a kirjinsa ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa. Kwakwalwarsa dankare take da abubuwa masu yawan gaske. Bashi da xabi illah ya nufi garin na Kano gobe gobe ko da kuwa hakan na nufin wani abu.

Yana dawowa ya shiga hada Yar karamar trolley dinsa. A haka Seema ta iskeshi mamaki karara a fuskarta.

"Ya naga kana hada jaka?" Ta tambaya tana kallon sa cikin ido

"Kano tayi kira, zanje na duba su Ammi, kwana biyu bana Jin dadin jikina, Amman saboda baki damu da sanin halin dan nake ciki ba, babu abinda kika ce ko kika nuna damuwar akai." Ya fada ransa a dan bace.

"Toh ai gani nayi in da sabo na Slsaba da yanayin nan naka, mutum k..."

"Auw haka ne ma?" Ya katse da mamaki.
"Shikenan tunda haka kika ce, bani waje na wuce an kira sallah." Gefenta ya raba ya wuce

Yana jiyo ta tace

"Mutum sai mitar balaee. Mtsw."
Girgiza kansa kawai yayi ya fice gaba daya ransa na suya.

Washegari da duku- duku yayi wa garin na Kano tsinke. Direct gidansa ya nufa dake kundila housing estate. Kayan jikinsa ya cire ya rage daga shi sai farar singlet da boxer ya fad'a gado. Babu bata lokaci barci yayi awun gaba dashi

***
A bangaren su Sadiya abubuwa sun cigaba da garawa. Wani zuwan Kamalu ne ya sanar musu yadda sukayi da Yaya Rabi'u akan kawo Sadiya ta ga likitan kwakwalwa. Wannan shawarar sukayi amfani da ita suka saka rana dan zuwa garin na Kaduna.

Su Sadiya Basu da duhun Kai duba da yanayin su a kauyen, babban gida ne gidan kakannin nata, akwai manyan Yayan malam da suke xaune a garin Kaduna, Jigawa Kano da Katsina. Dukkanninsu suna da rufin asirinsu daidai gwargado tuna sun waye da karatun Boko da kasuwanci
Baban wansu Yaya tukur shine ya fara fita Kano yana karatunsa a sa'adatu rimi har ya samu ya gama yana dan neman kudinsa.
A hankali rayuwarsa ta soma chanjawa lokacin da ya hadu da wani uban gida a kasuwar singa.
Ba bata lokaci ya koma makaranta inda yayi HND dinsa.
Ganin fa'idar karatun yasa ya jawo sauran kannensa uku suma suka shiga harkar. Allah ya sa musu albarka.

Yanzu dukkanninsu sun zama magidanta kowanne ya ajiye iyali sai Dan autansu Kamalu dake karatunsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Lokacin komawar Kamalu tayi suka dunguma har Malam suka bishi garin Kaduna gidan Yaya Rabi'u.

Kwanansu biyu Malam ya koma aka bar Inna da Sadiya Wanda za'a kaita asibiti ranar litinin.
Ranar da suka je asibitin akayi gwaje- gwaje aka bata magani sannan suka tura su xuwa babban asibitin koyarwa Na Malam Aminu Kano in da za'a yi mata wasu tests

Sati daya suka Kara akai suka dunguma suka yo Kano, kasancewar YayaTukur dama anan gidansa yake. Dalilin dama dayasa suka bi Kamalu Kaduna dan Yaya Tukur din baya gari yaje duba wasu shaguna da yake son bud'e wa Gawon dake Katsina.

Sai wajajen Azahar sannan Ahmad ya farka, rabon da yayi irin wannan baccin a Lagos ya manta. Sai a sannan ya lura da yadda gidan yayi kura. Be wani bata lokaci ba ya shirya cikin Kananun kaya Wanda suka fito da xahirin kyaun sa na Kanurin asali. A kafa ya fito ya tari abun hawa zuwa gidansu, kasancewar motar sa da yake amfani da ita in yazo tana gidan Amminsa.

Tun da ya shigo layin samarin unguwar ki daga masa hannu har ya isa kofar gida. Ajiyar zuciya ya sauke tare da jin wata irin nutsuwa ta zo masa... Cikin takunsa me kama dana namijin Duniya ya tura gate din. Da bangis ya fara cin karo. Mamaki ne shinfid'e a fuskar sa.

"Yaya saukar yaushe?." Ya tambaya yana Daria.
Hannu ya mik'a masa sukayi musabaaha kafin yace

"Yau na shigo da safe bangis, mun same ku lafia?"

" Lafia Lou Yaya Ahmad,Ina anty Seema?" Ya tambaya bayan sun jera cikin gidan hannayensu sark'e da juna.
A falon ma kowa sai da ya nuna mamakinsa ganin shi. Murmushi kawai yake hannunsa zub'e cikin aljihunsa ya karasa gaban Ammi dake zaune a kasa. Tankwashe kafarsa yayi cikin matukar girmamawa yace

"Barka da gida Ammi, mun same ku lafia?"

"Alhamdulillahi kowa lafia, dan shegantaka shine muka yi waya jiya baka sanar dani zuwan naka ba."

Shafa sajensa ya shiga yi Yana murmushi

"Suprise visit kenan inji bature Ammi."

"Kaji dashi, yanzu Ina ita me dakin naka, tana lafia dai ko? Dan ban ganku tare ba."

"Lafia lou, a chan na barota saboda makaranta, Amma tana gaishe su." Ya fada yana juya kansa wajen Shukra dake jera masa abinci da ruwa a gabansa. Tuni ya nad'e hannu bayan ya wanke shi cikin wata yar roba ya shiga cin tuwon shinkafa miyar taushe.

Sai da yaci yayi nak sannan ya shiga bawa Ammi labarin aiki da Lagos. Har aka kira la'asar suna hira bayan ya bawa Bangis mukullin gidansa yaje ya gyara masa.

Rano

RUHI DAYA (Completed✅)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon