HM - 10

3.5K 327 19
                                    

Yau da kanta ta kai yara makaranta, sabanin baya da shi yake kaisu, su kansu sun lura da yadda yanayin Mahifiyarsu ya canja a yau. Bayan ta sauke su ta kama hanyar da zata kaita sami naka, a kofar gidansu Samira Dahiru tai parking, sannan ta bude motarta ta fita kamar marar lafiya haka ta shiga cikin gidan, ko gaisuwar da mai gadin yake mata bata ji ba, domin kwatakwata hankalinta baya jikinta. A bakin kofar shiga falon ma tsaye tai tana tunanin yadda zata tunkari aminiyar da maganar.
 
“Assalamu Alaikum”

Tayi sallama bayan ta tura kofar falon ta shiga, gidan ba bakonta ba ne, dan haka bata jiran izinin zama ba ta zauna saman tana kallon kofar bedroom da Samira take kokarin fitowa fuskarta shimfide da murmushi.

“Lallai Amaryar Bashir yau sammako aka mana har gida”

“Wata matsalar ce take tafe da ni, Samira ina cikin wani hali mai daure kai”

“Miya same ki kawata?”

Ta tambaya fuskarta dauke da damuwa, sannan ta zauna kusa da ita. Kai ta sunkuyar cike da nauyin maganar a bakinta, tasan kawayensu da Samira ya wuce ta boye mata komai, amman ya ita Samira zata kalleta da wannan maganar? Ya zata kalli zaman aurensu idan har ta san sirrinta? Ba komai ne ya kamata ace kawayenka suna sani ba, musamman akan lamarim aurenka, amman kuma idan ta boye mata ya za'ayi ita ta samu mafita.

“Rukaiya lafiya kike kuwa?”

Ta dago da sauri ta kalleta, kana ta hade yawun bakinta.

“Samira ya zaki ji idan aka ce mijinki yana kokarin kulla alaka da yar'uwarki?”

Daukewar wuta Samira tai na yan sekonni kamin ta sauke wani dogon numfashi, ta dade tana jinjina lamarin sannan ta kalli Rukaiya da kallo na tsanaki ta ce.

“Ba zan yi mamaki ba, domin duniya tana cike da kazanta, dama ya nemi mahaifiyarsa, uba ya nemi yarsa, to miye abun mamaki dan miji ya nemi yar'uwar matarsa?”

“Amman ita ma yar'uwarsa shi Samira, ni da ita duka cousins dinsa ne”

Ta fada hawaye na saukowa daga idonta.

“Abu na biyu da zanyi zan fara tabbatar da inda labarin ya fito, na tabbatar da gaske ne miji yana nemanta ko kuma wata ce take kokarin kashe min aure ta gina nata? Idan na tabbatar da gaske ne sai ya bincika ya nema din ko kuma zai nema ne? Idan har ya fara zan datse alakarshi da ita, idan kuma zai fara ne to zan shiga tsakani”

Dagowa Rukaiya tai ta kalleta.

“Namijin daya shirya cin amanarka komai zaka masa ba zaka burgeshi ba sai yayi”

“Karki yaudari zuciyarki Rukaiya, kar shaidan ya zigaki ki rushe gidan aurenki, karki yi kuskuren da zai zama abun fada a tarihinki da na yayanki, zaki iya canja miji baki canja yar'uwarba, kiyi tunani kamin ki yanke hukunci”

Samira ta fada tana dafata.

“Be riga ya fara ba, amman Farhat ba ni ta fadawa ba, wata makociyata ta samu ta fadawa, ita kuma ta same ni office tai min maganar, dana zo gida sai na kore Farhat yau ta dawo tana fada sun hadu da barayi, a yau ta dawo Bashir yayi ta fada akan korarta da nayi, amman ban fada masa abunda yasa na koreta ba, karki so ganin yadda ya fita yau saboda kawai na koreta, shiyasa na fara zargin ko da gaske ne”

“Amman kin tuntubi Farhat kinji daga gareta?”

“Ban yi ba, kaina ya rufe Samira ban san abunda zan yi ba”

Ta fashe da kuka. Samira ta rika hannunta.

“Ke kika kan mijinki ciki da waje Rukaiya, ki gode Allah da yasa be riga ya fara ba, ki gode Allah da yasa kanwarki bata cikin irin wadannan matan na zamani, ki zaunar da mijinki ki nuna masa illar abunda yake kokarin aikatawa, da kuma irin gubar da zai zuba a zuri'arsa, Rukaiya kanwarki ta isa aure ya kamata ki aurarda ita, kuma ki rika sakata tana rufe jikinta, sakin jiki na daya daga cikin abunda yake janyo hankalin namiji ga mace har yayi sha'awar wani abu na nata, wannan dalilin ne yasa Allah yace kar mu bayyana adonmu sai ga iyayenmu ko yayayenmu ko mazajenmu ko yanuwanmu maza ko mata a suratul Ahzab, da ace Farhat tana yin shigar data dace da be ga wani abu a jikinta har yai sha'awaba, da ace mijinki ya saba neman matan waje ba zai zo neman kanwarki ba, idanuwansa zasu fi budewa da na wajen.

HAFSATU MANGAWhere stories live. Discover now