HM - 12 Turmoils

3.4K 313 15
                                    

YARIMA ZAIN POV.

Tun da suka fito tiyata yake jin ba dadi, ba kuma na rashin lafiya ko na bacin rai ba, jikinsa na bashi kamar wani abu ya faru da shi ko kuma zai faru da shi ko wani nashi.
Tafiya yake kamar mai tausayi kasa, a yadda ya sake fuskarsa zaka dauka murmushi yake maka saboda yadda ya samu kansa a yanzu shi ba farinciki ba kuma ba damuwa ba.

Duk inda ya ratsa gaisheshi ake amman be daga kai ya amsa ba balle ya amsa musu, a kasaitaccen office dinsa ya shiga, wanda aka kawata da kayan ado na zamani irin wanda ake gyara manyan offices da su, sai da ya zauna saman kujerarsa mai juyawa sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali.
Wayarsa ya dauko ya shiga contactlist dinsa neman Number Ikram, dialing yai in few minutes aka dauka muryar Hameeda yaji bakinta kumshe da sallama.

“Assalamu Alaikum”

Wani dip yai kamar ba zai amsa sallamar ba, yaji kamar kar ya amsa sallama.

“Ina Ikram?”

Ya tambaya yana wani hade rai kamar ance masa tana gabansa.

“Bata kusa, kana da bukatar wani abun ne”

Be jin zai iya kara amsa mata, sai kawai ya sauke wayar, daman yana son ya tambaya ne idam Mai Martaba yana gida kuma yana lafiya, duk da kasancewar yasan ya baroshi lafiya amman yana da bukatar jin lafiyarsa, saboda abunda yake ji, obviously jin muryar Hameeda ya hana shi tambayar hakan. Juyi ya soma yi saman kujerar yana lilo, bayan Mai Martaba Anty Ummi ce mutum ta biyu da suka fi kowa muhimmanci a rayuwarsa, it could be her wani abun ya sameta ko zai sameta,  numberta yai dialing ringing biyu ta dauka.

“Doctor”

“Professor”

“Ya aka yi?”

“Kalau, kawai ina son ji daga gareki ne”

Jimm tai, dan tasan ya saba kiranta a duk lokacin da yake tunanin wani abun ya sameta.

“Lafiya ta kalau, sai dai ko Mai Martaba”

“Na kira Ikram yanzu Hameeda ta dauka da akwai wani abun da zasu sanar da ni, kina gurin aiki ne?”

“Yeah ban dade da zuwa ba na zo late ma”

“To ina kika bar Mama?”

“Wace Mama...?”

Tuna Hafsat yasa ta ce

“Oh tana can tana bachi”

“Ita kadai?”

“Baba Asabe ai tana nan, kuma Farhat ma tana dakina tana bachi”

“Haba Anty kin san Farhat din nan ba wani hankali ya isheta ba, last time ma ba ita ta bude mata kofa ta fita ba, kuma ita ma Baba Asabe idan ba magana kika mata ba ai zata iya barinta ta fita...”

“Hey hey hey...  karka dame ni da zacen wata yarinyar kauye, aiki nake yi sai anjima”

Ta katse wayar, tsaki yaja yana kokarin mikewa tsaye, lapcoat  din take jikinsa ya cire ya rataya a hanger, ya fice office din da sauri. Tun kamin ya karasa gurin motar ya danna keys din hannunsa motar ta fita key yana isa budewa kawai yai ya shiga ya tashi motar. Daga saminaka area zuwa gada biyu area babu wani nisa sosai dan haka cikin kankanen lokacin ya iso. Tun da yai horn be ga an bude masa gidan ba zuciyarsa ta soma raya masa babu lafiya, sai dai yai horn kusan sau shida amman babu wanda ya leko balle ya bude masa, hakan yasa ya fita da mota ya taka kasa ya shiga cikin gidan, dakin dake kusa da gate ya fara leka dan ya gani idan Malam Adamu na ciki, amman sai ya tarar babu kowa ciki, yana nufar main house din sai ga Malam Adamu ya fito daga Bq da saurinsa, ganinsa yasa Zain tsaya yana kallonsa tare da jiran ya karaso.

HAFSATU MANGAWhere stories live. Discover now