HM - 19

2.6K 241 10
                                    

Misalin goma na safe ya fito daga sasshensa, yau kam yayi bachin safe wanda a manta rabon da yayi irinsa saboda jinyar Hafsatu da yake. Part din Dada ya nufa, yau kam ya tararda Hameeda ita kadai na zaune falon Dada tana karyawa.

“Ina kwana?”

Ta gaisheshi muryarta na rawa, ba tare da ta bari sun hada ido ba. Be amsa ba be kuma fasa kallonta ba har ya zauna kusa da ita kasancewar ita tana kasa ne shi kuma yana saman cushion.

“Akwai wani abun da kike son mu tattauna ne?”

Ta dago idonta ta kalleshi sai kuma ta sauke.

“Aa ba komai”

“Feel free ki fada min abunda yake damunki, zan saurareki”

“Kamar da?”

Ta tambaya idonta narau-narau. Shiru yai kamar ba zai ce komai ba.

“Fiye da da”

Zata sake wata maganar sai ga Dada ta fito daga bedroom dinta sanye da wani tsadadden lace.

“Kai Amaryata kin fito fes...”

“Kasan fa kai dana ne ba jika ba”

Ta fada tana murmushin kasaita.

“Aa yau dai bangaren jika na dauka, ki bar da sai idan nayi laifi, ko da yake na kusa yinsa tun da kishiya zan miki kwanan”

Dam gaban Hameeda ya fadi, zuciyarta nata raya mata ita ce. Dada ta bude baki.

“Kai kai wace mai dajara ce wannan?”

“Wata kyakkyawar yarinya ce kama da indiyawa”

“Ciki ko wajen masarautar nan?”

“Bata da alaka da masarautar nan, amman dai mai tarbiya ce”

A take murmushi da annashuwar dake fuskar Dada ya gushe, ta murtuke fuska kamar an aiko mata da mutuwa.

“Tarbiya bata burge mu, domin cikinta muke kuma munyi gadonta, ko da wasa be kamata ka tsallake marautar nan ka dauko wata ba, ba zaka burgemu ba, mai martaba da ni ba zamu lamunta ba, ba zamu yarda ka kawo mana bare ba...”

Hameeda ta hade yawun bakinta da suka mata daci ta tari numfashin Dada.

“Ko da baren nan ita ce silar farincikinsa? Kuma ita yake so kamar ransa? Haba Dada tun yaushe kuke jiran zuwan wannan ranar ranar da Yarima zai gabatar da wata mace a matsayin matar aurensa?
Dada baki tunanin lokaci yayi daya kamata a bar kowa yabi zabin ransa? Kar kankancinta ya dameki ke dai abunda kika sani wanda zai aurota mai daraja ne a gurinki, dan Allah dan girman Allah ku bar mu mu auri wadanda muke so”

Ta karasa tana hade hannayenta guri daya alamar roko. Zain was shocked irin yadda take defending dinsa. Dada was shocked too da abunda yake fitowa daga bakinta, ga kuma fuskarta na nuna gaskiyar rokon da take.

“Yaushe tarbiyarki ta lalace haka da har zaki iya daga baki ki fadi wannan maganar?”

“Auren biyu zan yi bana daya ba Dada, daga ni har ita muna da damar zaben abar da muke so ko da kuwa wajen masarautar nan ne, ke dai ce gatana a duniyar nan Dada idan kika tsaya min ko mai martaba ba zai musa ma bukatata ba, ke uwace a gareni shiyasa na kawo bukatata a gareni Dada ki taimaka ki zame min uwar da kike ikirari dan Allah”

Ya marairaice mata sosai kamar zai yi kuka..

“Wato kunje kai da wacan bakar yar'uwar taka kun gada kai ko?”

“Ba wani hadin kai Dada kema kin san idan bana son abu babu wanda ya isa ya saka nai yi, ni naga yarinya nanu ina sonta shiyasa kuma nayi tunanin zaki goya min baya shiyasa na gabatar da ita a gareki”

HAFSATU MANGAWhere stories live. Discover now