*Kuruciyan Asabe*
💃💃💃💃💃💃💃 *kuriciya dangi hauka*💃💃💃💃💃💃💃💃
*Short story*
Written by *matan banufe*
Dedicated to *mutanen minna*Bismillahi Rahmani Rahim
Page *1*
Misalin karfe takwas na dare yara ne sukan taru a baki kofan gidan ladi me banbara dake anguwa daji.
Wasa sukeyi hankali kwance suna rera Waka kaman haka🎼🎼🎺🎷 in da rai da rabo
in da rai da rabo bana sai na auri shugaban kasa
Bana sai na auri shugaban kasa me mulki
*sai yara Suyi amshe*
Wazai baki shugaban kasa me Mulki
*sai ta amsa da*
Allah Mai iko
Allah Mai ikoShi zai bani shugaban kasa
shi zai bani shugaban kasa me Mulki
Sai Sauran yaran su hada baki wajen amshi
Allah bata
Allah bata
kuma Allah bata shugaban kasa me mulki
🎼🎷🎷🎺🎷🎺Wani yaro ne ya sheko da gudu asabe Wlhi ga Kawu nan zuwa ,ko rufe baki bai Yi ba su asabe suka kwasa a guje sukayi gida
Ta zauren gidansu suka dakata ke haulatu mu lalaba muyi dakin me masa kafin Kaka taji motsi ta fito....
Suna shiga dakin me masa suka tarar da ya Tani zaune tana cin nama,,,,, asabe tace a a su ya Tani nama akeci haka toh ina namu kason
Harara tani ta Yi masu tare da jan tswaki in kuna da karfi ai sai kuzo ku karba,Haulatu tace yi hakuri ya Tani
Aisha da take kwance tace tani ke kika tsaya har kina sauraran su
Asabe tayi karaf tace Wlhi in ba a bamu namanga ba Allah kawu zan je nagaya ma cewa yau kunfita zance, ai kunsa ya hanaku tadi ko? In ji dumus ko nakai rahoto
Wasu susha Bulala da daddaren nan ehhe
Haba yar kanwa mu zauna ga shi nan kuchi yanzu naji bayani kam
Jin motsin Kawu na shugowa ai sai kowa ya kwanta
Daki kaka direct ya nufa Yi mata sai da safe
*washegari*
Da safe kowa ya dauki Bokitin dibo Ruwa a rijiya
Haulatu Kalla dunkule yana kwasan kwata yau ba kudin shaye shaye na kwata yau zai Shaka,, kinga asabe zo mu wuci kinsan dunkule ba hankali cikake gare shi dan Allah kar ki tsokane shi
Ai kafin Haulatu ta rufe baki asabe tace kai dunkule...............
Tirkashe ga asabe GA dunkule
New writerSai naga comment Sanan zanci gaba in ba comment that mean novel din baiyi maku ba
See you next time

YOU ARE READING
KURUCIYA ASABE
Short Storyshort story,,,,, kuruciya dangi hauka kar kabari abaka labari ehhe