*kuruciyan Asabe*
💃💃💃💃💃💃💃💃
*kuruciya dangin hauka*
💃💃💃💃💃💃💃💃
Written by *matan banufe*
Dedicated to *mutanen minna*
*page 3*
Da kuka asabe ta shige cikin gida,kaka tace Yaki nan ja'iran yariya shiga daga ciki ki tube kayan jikin ki, da murna asabe ta shige ciki a zuciya take maga " yau mutanen kirki ne a kan kaka na dauka duka na zatayi"Asabe na shiga daki kaka ta biyo ta har da sa makulli .zabori ta jawo a kar kashin gado ,kaka batayi wata wata ba sai ji kawai fayau fayau kakeji
Wani uban ihu da asabe ta saki tare da Wani uban kara sai yaja hankalin me masa har da makobta kaka kiyi hakuri Wlh Allah bazan kara ba
Ki ma kara Wlh jikin ki ne zai gaya maki kullun In ba a taba lafiyan jikin kiba baki jin dadi magana kaka takeyi har da haki Kamar wanda tayi tsireKaka dan Allah ki bude kofan nan"me masa take ta magana"ki kyale ta hakannan, bude kofan kaka tayi Sannan ta jawo asabe ta hau saman cikin ta ta falla mata mari, da dan gudu me masa ta karaso.
Haba mana Kaka ko haka kika barta ta daku.Asabe na gani Kofa abude da gudu ta an taya waje, su ya Tani da Aisha dariya suke tayi, ya tani tace Wlh banso kaka ta duke asabe ba da kawu ya duke ta nasan da Bulalan inji ko Ice zai duke ta.ke dai bari ai yanzu me masa baza tabari kawu ya duke taba zatace Kaka ta duke ta ko Aisha ne me magana.
Haka asabe ta sha kuka ta wuni ranan Kaka ko kallo bata isheta ba sai me masa da Haulatu ke faman lallashin ta.
Haulatu tace asabe tashi muje gidan su Abu kafin Lokacin makaranta yayi,
Assalamu alaikum ,Wa'alaikumu salam mama ina wuni lafiya , Yasu Kaka ?lafiya qaula.Mama Abu na nan eh tana baya, Abu kenan a kan ice, kiyi shuru kafin mama ta jiki.
Haulatu tace Abu tsun ko gwaiba da yawa ,yau dashi zamu islamiya, haka Abu ta tsun ko gwaiba da yawa su asabe na kwashe wa suka daure a dankwalin su,suka boye ta wajen kofan fita gidan.
Ko da Lokacin islamiya yayi Abu ce tabiyo masu asabe, me masa ta basu ashirin ashirin haka suka biya gidan su baby kanwa mallam nura.
Allah baby baza mu wuce islamiya ba sai munbiiya gidan ladi me banbara in na tarugu da tafanuwa dance ki dauko Haulatu ta ce gashi nan yau kullun tawaska zamu siya ke baby ki kawo mana Magi "eh na kawo".Ladi asamana kullun tawaska na sittin ke Abu Kuyi sauri ku daka su tarugu muyi ta soya mana, haka sukayi
Ko da suka doso hanyan islamiya suka hangi mallam nura na Kama latti yaya baby.Baby tace yau mun shiga uku ya nura zai mana bulala double ya zamuyi.
Asabe dan Allah muje muce me masane ta aike mu,toh in su ya Tani da Aisha suka Karya ta mu fa..
Ahaye sha madaran lilo
Ahaye sha madaran lilo
Ga wasu nan Zasu sha Bulala sha madaran lilo asabe ke Waka tana wucewa gaba.......Su Haulatu bin ta sukeyi da ido......
*matan banufe*
Pls *comment*
*vs*
*share*

YOU ARE READING
KURUCIYA ASABE
Short Storyshort story,,,,, kuruciya dangi hauka kar kabari abaka labari ehhe